Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 59

Chapter 59

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta wanke fuskarta ta fito danjin alamun ya fita. Kwanciya tayi saman gadon wasu hawayen na zirarowa, itafa koma mizaiyi tana akan bakanta, dolene saiya kar6a laifinsa sannan koda zai sameta yanda yakeso. A can falo Samha yabama Amaturrahman yay musu sallama ya fita. Shareshi momma tayi, sai aunty Mimi ce tace, “Dan ALLAH Momma Ku tsaida shirinan naku keda mom, kubashi matarshi, yanzune hankalinsa ya kwanta yadace yasami cikakkiyar nutsuwa da iyalinsa, amma kunbi kun kankane, haba dan ALLAH Momma ”. Da 6acin rai Momma ta kalli Aunty Mimi, “To mai d'an uwa, yanzu ke idan Sauban ne a matsayin Munaya zakiso wani yazo ya auresa a sigar da d'an uwan naki yayi? Miyasa kukeda son kanku, wlhy kinji na rantse inhar bai gane kuskurensa ya nemi yafiyartaba ta yafe masa bazan ta6a bashi itaba, idan yagadama ya cika gidannan da fushi, kuma aiga y'ay'ankunan mata kun haifa, ba kuma zakuso a aikata hakan agaresuba ince?”. Aunty Mimi ta tausasa murya ganin ran Momma ya 6aci, “tokiyi hak'uri Momma, ni aganina a zaunar dashi a karanta masa laifinsa, kinga shi yanzu dukma baisan dalilinkuba wlhy”. Banza Momma Tamata, ta ajiye Abdurraheem ta tashi takoma d'akinta. Binta kawai da kallo aunty Mimi tayi, tasan akan gaskiya su Momma suke, to amma sai a tausayama Sameer ai shima, akuma sanar dashi laifinsa, tasan halin Momma akan son kwatarma mai gaskiya gaskiyarsa, bakuma zata ta6a tank'waruwa ta sauk'iba, balle ga mom a gefe na angizata. **************** Ran Galadima a 6ace yay wannan tafiya, sauk'inma da yaje yaga jikin Abie ne sai nutsuwa ta saukar masa, har yanzu yanata samun kulawa ta musamman, bakuma a shiga inda yake, amma kullum Dr Erfan cikin ma Galadima albishir yake akan cigaban da ake samu, yauma sosai ya labarta masa komai gameda ga66an Abie da ayanzu zasu iya fara aiki, zasu barsane yad'an k'ara kwanaki domin k'arfin jikinsa da abinda ba'a rasaba, dama ciwo shike shiga lokaci d'aya, amma sauk'i sai a hankali. Kwanan Galadima biyu yadawo new Delhi. Ranar kamar wasa Munaya da Samha suka shiga kitchen wai zata koya mata tuwo, har Momma na musu dariya da tsokanarsu yau zasuci tuwon y'an gayu. Daga abin wasa sai Munaya ta zage tayi nutsetstsen tuwo da miyar ganye, tamusu juns na kayan itatuwa, gamawarsu kenan sukaje zasuyi wanka, Momma da Aunty Mimi na zaune afalo suna jiran suyi wankan azo abasu tuwo suci, su Abdurrahman duk suna tare dasu aunty Mimi na yanke musu k'unba, Yayinda jakadiya ke tayata, babu Wanda ya sanarma zaizo, sai kawai sukaga ya shigosa da sallamar nan tasa ciki-ciki. Duk juyowa sukai suna kallonsa da mamaki, jakadiya ce kawai tasami damar amsa masa, sai Khaleel dake wasa ya tafi da gudu yana masa oyoyo. 'Daukar yaron yay ya d'aga sama, dukda yayi girma masha ALLAH. Ya k'araso cikin falon Jakadiya na gaisheshi, amsa mata yayi da kulawa, sannan ya zauna a kujera yana rik'e da hannun Khaleel. Momma tace, “wai dama kana tafe?”. “Wlhy kuwa Momma”. Yafad'a cikin sauke numfashi, itama ya gaisheta. Itama aunty Mimi suka gaisa, tana masa sannu da tambayarsa jikin Abie. Cikin fad'in “Alhmdllh” ya amsa musu, yabasu labarin cigaban da aka samu, farin ciki na manaye zukatansu. Ajiye ruwan da baiwar tamasa yay dai-dai da fitowar Munaya cikin matsakaiciyar kwalliyar data k'ara mata kwarjini da cikar haiba, dan zani da rigane na atanfa, ta fito asalin bahaushiyarta jinin buzaye tawani fannin. Lokaci d'aya idonsa ya sark'e cikin na juna, kowanne sirrikan kewar d'an uwansa na fita daga cikin nasa, Munaya tafara d'auke kanta, yayinda shima Galadima ya janye nasa cikeda basarwa. Jitai tamkar karta k'araso, amma kowa yarigada yaganta, tadai k'araso tana masa sannu da zuwa. Amsawa yay cikin halin ko in kula. Ita Momma dariyama suka bata, hakama aunty Mimi data maidasu television. Ajiye Abdurraheem d'in yayi yatashi wai zaije ya watsa ruwa. Munaya tabisa da kallo a sace, sanye yake cikin k'ananun kaya, wando ruwan toka da farar riga mai d'ishi-d'ishin ruwan goro. Tad'anyi 6oyayyar ajiyar zuciya tana kauda idonta lokacin daya juyo, dan jiyay a jikina kallonsa akeyi, aiko saigashi ya kama yalla6iyarsa dumu-dumu. Baki yata6e ya ida hayewa yana sak'ama zuciyarsa matakin daya shirya d'auka akanta. ******** Ba'a zauna zaman cin tuwonba saida Galadima yay wanka ya sakko, duk suka hallara wajen cin abincin, Momma tama Munaya nuni da ido tayi saving nashi. Babu musu tabi Umarnin Momma, yanata latsa waya tamkarma baisan hidimar da sukeba, ga fuska cinkus babu walwala, dukda zuciyarsa na kwad'ayin fara cin abincin da k'amshin ya addabi hancinsa tun d'azun. Tana gamawa takoma mazauninta da Samha ta shiga tsakkiyarsu, ya ajiye wayar yana kuma wani d'aure fuska dacin Magani, yayi mamakin ganin tuwo, dukda dai Dama akanyi musu amma sai time to time, shiyyasa yake sonsa sosai. Hannunsa ya wanke a ruwan da aka ajiye masa, baici da tsokalin data ajiyeba. Tun a laumar farko kunnensa ya nemi tainkewa, 100% yaji yakamata ya baima mai wannan girkin maki. Momma da Aunty Mimi dai kam kasa hak'uri sukayi, suka shiga santi da yaba wannan tuwo, Galadima dai yayi tsitt, sai a zuciyarsa yake yabawa, cikeda tsokana Momma tace, “wasuma dai santin nasu na shirune, suna tsoron yin magana dad'in ya yanke”. Dariya su aunty Mimi sukayi, Munaya ta saka d'ankwali ta kare bakinta tana murmushi, dan kowa yasan dashi Momma take. Galadima da yasan dashi Momma take shima saiya murmusa yana satar kallon Munaya. Saida suka gama tsaf Momma ke cewa lallai d'iyata sannu da k'ok'ari, rabon danaci tuwo irin wannan mai dad'i tunna inno, har k'yauta yau saina miki”. A kunyace Munaya tace, “godiya nake Momma”. Dukda Galadima ya fahimci girkin Munaya tayishi baice k'alaba, saima ya d'auki waya yay kira, ya mik'e ya fice harabar gidan. Aifa nan suka shiga gulmarsa suna dariya, Samha harda cewa tana ganinsa yana lumshe ido lokacin fayakecin tuwo. Aiko mizasuyi inna dariyaba. Koda yagama wayar bai koma cikin gidanba, saiyay ficewarsa saboda gabatowar lokacin salla. *_9:30pm_* Galadima ya sakko daga samansa, fuskarsa kawai zaka kalla kafahimci yana tare da damuwa, sanye yake da kayan barci farare sol, wandon yaje har k'waurinsa amma baikai k'asaba, sai k'amshi mai sanyi yakeyi. Cikin sand'a ya tura k'ofar Momma yad'an lek'a kansa, Munaya kad'ai ya hango zaune abakin gado tana tofama yaran addu'a a tafin hannunsu tana shafa musu a jiki, ya kalli ko ina babu alamar Momma saiya ida shigewa. Shigowar Mutum kawai Munaya ta gani, tsorata tayi, ta kware baki zatayi ihu yay azamar saka tattausan hannunsa ya toshe bakin, k'amshin turarensa ya sakata fahimtar shine, d'aukarta yay gaba d'ayanta tanata mutsu-mutsu da k'afafu dason yin magana amma babu dama. Yanufi k'ofa da ita zai fice Momma ta fito daga bayi, daga bayansa kawai yaji ance, “Sannu shugaban masu iya satar mutane, to saika ajiyeta ai”. Fad'uwar gaba da kunya dukta lullu6eshi a lokaci d'aya, ya dire Munaya yana susar k'eya saboda kunya, yama kasa kallon Momma d'in. Itakam bata kuma cewa dashi komaiba tazo ta gabansa ta fita d'akko abu. Yana ganin Momma ta fita saiya juyo ga Munaya da hanzari. A matuk'ar fusace yay kanta, “K! y'ar rainin hankali ALLAH yau saikin sanarmin minayi miki, inba hakaba a d'akinan zan kwana, bar ganin Momma ta tsaya miki”. Ja da baya

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});