Chapter 74
Chapter 74
murmushe da share hawayensa da Handkerchief. “Na tsinci kaina cikin zumud'i da firgici dukda k'ananun shekaruna, Dan lokacin bazan wuce 17years ba nake tunani, hawaye Na zuba a idona nace da gaske zaka musulinta Doctor?. Cikim jinjina kai ya tabbatar min. Ban tsaya 6ata lokaciba nace doctor addinin musulunci ba'a biyan ko sisi domin kasantuwa a cikinsa, imani da ALLAH da yarda da manzonsa shine babban farashi mafi daraja a duniya. Yace to a ina zan samo imanin?. Nai dariya da fad'in ta hanyar ambaton Kalmar la'ilaha illallah muhammadurrasulullh. Yace to ya shirya. Duk da k'arancin shekarunan nawa baiyi Girman kaiba ya kar6a kalmar shahada yana mai jaddadata a harshensa har saida tari ya sark'esa, rikicewa nayi Na mik'e da nufin nemo doctor amma saiya hanani, yamin nuni dana bashi ruwa, haka nadawo na bashi ruwan, kur6arsa hud'u ya janye kansa yana fad'in___”. _“Sameer, tabbas yauce ranar tafiya koda shiri ko babu, ina rok'onka koda sau d'ayane ka gudanar da salla a kaina, sannan karka yarda wani d'an uwana ya san da musuluntata, badon komaiba sai Dan gudun tozarta ku, ka sanarma Anania ina matuk'ar k'aunarta, karta manta dani”_. Daga nan ya shiga maimaita kalmar shahada yana wata irin zufa maiban tsoro, na rik'ice inata ambatar sunansa da girgizashi, sai kawai naga jikinsa ya saki. Sakinsa nai Na fita da gudu kiran doctor sai mukaci karo da Momma dataji shirun yayi yawa tabiyo sawuna. Rik'eni tayi tana tambayar lafiya?, jikina Na rawa nasanar mata abinda yafaru da Hausa. Dan nasan mawuyacine asamu maijin yaren a kusa damu, hanani kiran doctor tayi taja hannuna muka k'oma d'akin tana share hawen farin ciki Dana kewar Dr Arjun, tai addu'a mai yawa akan gawarsa sannan tace Muh'd zaka iya masa wanka?. Bak'aramin tsorata nayiba, jikina Na k'yarma nace Momma wankafa?, nidai tsoro nakeji. Ta dafa kafad'ata cikin k'aramin kwarin gwiwa tace yarona karkaji tsoro, tunfarko ubangijine ya za6eka ya k'addara Dr Arjun ta hannunka zai zama musulmi, ka daure ka cika masa wasiyyar daya barmaka ta sallatar gawarsa, Dan kasandai su ahalinsa ba irin wannan jana'izar zasuyi garesa ba, ina tare dakai kaji. Bisa Umarnin Momma da koyarwarta naima gawar Dr Arjun wanka, itakuma tana bakin k'ofa tanamin gadi, Ubangiji kuma saiya ara mana dogon lokaci harna gama na maida masa Uniform d'in asibitin a jikinsa, sannan na sallacesa ina kuka. Saida muka gama komai sannan muka fito mukabar gawarsa cikin d'akin, bamukoyi nisa da k'ofarba mukaga doctor ya shiga d'akin da hanzari, mintuna kad'an da shigarsa maganar rasuwar Dr Arjun ta fara Shiga kunnuwan Mutane. Wannan rasuwa ta matuk'ar ta6a zuciyata, har a yau d'innan da nake gabanku ina jinta, kuma ban gaza wajen yimasa addu'oin samun rahama ba”. Galadima ya share hawayensa dake zirara tamkar fanfo, ya kalli mutane yana fad'in “kakannina, iyayena, yayyena da k'annenna kunsan hikimar baku wannan labarin kuwa?”. Jiki a sanyaye, wasuma hawaye sukeyi suka amsa da a'a. Galadima yay murmushi yana kuma share hawayensa da gyara tsayuwa, “Wannan labarin yana mana nuni muzama masu nagarta aduk inda muka tsinci kanmu, babu irin k'yawawan halaye da addininmu bai koyar damuba, amma son zuciya da burukan duniya saisu sauyamu, miyasa muke mantawa damu su waye? Ina kuma zamu koma?, dalilin ruk'o da gaskiya mahaifina ya fad'a hali mai tayar da hankali na tsawon shekaru, babu wanda ya ta6a tunanin sake ganinsa anan, amma kuma sai gashi, kunsan wane irin hali mai firgici da ciwo da muka tsinci kanmu kuwa? Mahaifiyata itace silar komawata jarumi, da taimakonta nazama jajirtacce, a halin k'uruciya har tunani nake anya kuwa tana sona? Ajiye sosayyar nan ta d'a da uwa tayi ta kutsani cikin talakawan daba yarena ba, ba addinina d'aya dasuba, ba k'asa d'aya muka fitoba, naringa wahalhalun koyon sana'oi da gwagwarmaya ta fahimtar rayu, ga karatu, ga damuwa da ciwon mahaifina, ban fahimci gata taminba saida na iya d'aukar nauyin ciwon mahaifina da hidimomin ahalina, na kammala karatuna bisa bigiren danake buri, iyaye mata wlhy kuzamto masu koyi da halayen mahaifiyata, matasa y'an uwana kuzama masu koyi da rayuwata, dukda ana ganina d'an ganta ban zauna gata yamin komaiba, saina tashi da k'afafuna da gumina na gina kaina, muzama masu k'yawawan halayya koda daraja martabar addininmu ga wad'anda basu fahimcesa ba, Dan k'yawawan hallaya da nagarta yaja hankalin Dr Arjun kwad'aituwa da addinin Islam, Yakuma mutu a cikinsa bisa amincewar ubangijin al'arshi, da mugayen hallaya mukeyi saidai doctor Arjun ya k'yamacemu dajin kuma k'yamar addininmu, son zuciyoyinmu shike maidamu bayan baya a Kullu yaumin, ba tarin dukiya ko gata ko k'yawune abin birgewaba, Nagarta, nagartar samun k'yawawan halaye da d'abi'u shi ake kira jarumta, matata ta ta6a fad'amin Hak'uri shi ake kira NASARA, saida hak'uri ake zama jarumi, sai an jure zafi ake tsintar kai a sanyi. Kusan shekarunta nawa kuwa?, ashirin, inhar mace mai k'ananun shekaru irin wannan tanada hikimar zance da nazari mai amfanar da wani irin haka miyasa tunaninmu ke d'aukar mace mai k'aramar kwakwalwane?, nabaku satar amsa kaje ka mu'amullanci matarka ta nagartacciyar hanya kaga yanda zaka amfanu da tagomashin tunaninta, kunga mata biyunan sun zamema rayuwata wata ginanniyar Katanga, mahaifiyata da kuma matata da auren shekara d'aya kacal zamu cika, kakata yayata k'anwar mahaifiyata rumface su dake kare martabata da zamana cikakken mutum, ina mai farin ciki mai tsanani da samun lafiyar mahaifina, da godiya mai yawa ga wasu ke6antattun mutane wadda gudunmawar suce silar ganina a gabanku, ALLAH ya albarkaci rayuwar ahalinsu ya cika musu burukansu na alkairi, Yakuma had'amu a aljanna gaba d'aya”. Duk suka amsa da amin suna binsa da tafi. Daganan sauran jama'a sukaita bayani d'ai-d'ai, taro dai bai tashiba sai kusan 3:00pm. Cikin farin ciki Galadima ya shigomin, ko kunyar su Ahmad dake zaune da Sarkin mota ya shigo dasu bai jiba ya rungumeni, saida na ankarar dashi sanann ya sakeni yana susar gefen wuya alamar yaji kunya, yayi farin ciki da ganinsu kuwa, yaran sun shiga ransa sosai, duk da abinda yayma mahaifansu basu tsanesa ba, saima zuminci mai k'arfi daya k'ullu a tsakaninsu. Ranar sashenmu saiya koma na matasan samarin masarautar, Dan shima Sauban nan ya kawo gayyarsa cin abinci, gasu Yassar kuma, itama Samha saiga tata gayyar, saikuma ga matasan gidanmu da y'ammata da banyi zaton ganiba, harda Zarah da Siyama, dad'i tamkar xai karni kuwa. duk yanda Galadima yaso ke6ewa da matarsa abin ya gagara, dansu Matawalle da Nuren da suka iso dawasu samarin masarautar suma duknan suka nufo, tsakaninsa da Munaya sai dai y'ar satar kallo, dan kwalliyarta tagama narkashi. Baniba kosu Amaturrahman sunji a jikinsa raranar, d'auka dai sun shata harsun gode ALLAH, bankuma samu damar shayar dasuba sai madara suka sha. Har dare babu wata damar samun ke6ancewa da juna. Washe gari kuma aka gudanar da hawan salla mai k'ayatarwa, wanda a tarihin masarautar gagara badau an dad'e ba ayi irinsa ba, saboda manyan sarakuna na garuruwa daban-dabanne da Governors harda uban gayya president da senators da sukazoma Abie barka da dawowa suka halarci bikin hawan sallar. Misalta muku k'yawun kwalliyar jarumin naku Galadima ai 6ata lokacine, ammafa komai zamm, y'ammata da yawa sun k'yasa, balle yau fuskarsa washe take da murmushi na musamman Wanda jama'a basu ta6a ganiba. Su Abbana ma sunzo gaida Abie, sun sami k'yak'yk'yawar karramawa mai ban mamaki, wadda tasani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83