Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 42

Chapter 42

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dacin hak'k'in kowa koda kwayar zarrane😭😭👏🏻._ _Kumuje zuwa asibiti, danjin wane hali Munaya take ciki itada Nuren kuma?.😔_ *_Nagode sosai da addu'oinku gareni, da mahaifina, ALLAH ya bada ladan zuminci Yakuma kar6a mana baki d'aya, bansan yazan nuna godiyata ga masoyanaba, saidai nace kuma ALLAH ya biya muku buk'atunku, kaini har mak'iyinama ALLAH ya biya masa buk'atarsa ta alkairi, dan saida mak'iyi duniya ke dad'in zama🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀, idan babusu tamkar miyace lami babu gishiri da magi🤨😝😂.🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [8/22, 8:25 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ________________________ *_K'atotuwar gaisuwa a gareku my sweet friends_* _Shamsiyya Yahaya D/Z, Farida Muh'd gadanya (y'ar farida😝), Umma Yahaya /D/Z, Sadiya Abdullahi S.A, Hadiza 'Dayyabu Fama, Bahijja Musa Tyw, Hadiza yakubu Tyw, Fatima 'Dayyabu Fama, Hadiza isyaku Gurun, Hadiza Umar fama, Ummi Sani Tyw, Fa'iza Zakari Tyw, Sadiya Sulaiman SS, Hauwa'u Muhammad Nsw, Nafisa Ibrahim G/mutun 1 (I miss you y'ar gidan baban😅) Rabi'a Lawan Tyw (ho y'ar kwana🤣) Ruk'ayya Muhammad Tyw, Zainab Ado Tyw, Zakiyya Liti Tyw, Sadiya Lawan Fama, Bariya Salisu yashe, Umayya Yusuf R/gado, Zahariyya idris R/gado, Naja'atu Rabi'u R/gado, Zuwaira Abdullahi k/giwa, Nafisa kabir Tuge, Shamsiyya Kabeer Tuge, Zainab Adam Bichi, Amina Rabi'u N/iya, Ummi k/giwa, Maryam Tasi'u Tyw (ALLAH ya gafarta miki, ya raya abinda kika bari😭)._ *Aradun ALLAH yawane daku, wasuma sunansu ya 6acemin😔, I miss you all. Kai duk wadda ma yay GGASS D/ZABUWA ina mik'o gaisuwar fatan alkairi a gareshi, Musamman ma y'an 2010 Graduation boko and Arabic, Alkairin ALLAH yakai gareku baki d'aya. Bilkisa Ibarheem Musa (Bil-Gur) kai malam basheer lamba ya iya sa suna🤣, Na gaisheku irin trillions d'inan wlhy, nasan kunata missing tuwon Malam kabiru da koko mai saka barci, ga fatan wake mai kwari (nama a wancan lokacin🤣😜) Yaya kwad'on tuwo da shayi mai kauri🤸🏻‍♀, kai duniya, komai Na rayuwa labari, INA missing d'an sirri d'ebo ruwa wlhy😔😂.* _________________________ *_BOOK 3_* 👉🏻2⃣0⃣ .................Galadima ganima yake kamar Sarkin mota baya Sauri, amma baiyi maganaba, zuciyarsa tamafi motar gudu, dan bugawa take da sauri-sauri tamkar zata fito. Suna isowa bai saurari an bud'e masaba ya bud'e da kansa yay cikin asibitin, dayake k'aramin asibitin ne, na kud'i su Ahmad suka kaisu, da sauri Nurses d'in dake reception suka masa sannu, tare da gaisheshi, dan 6atancin da aka musu Shida sh Munaya a wancan lokacin yakuma sakawa wad'anda basu sanshiba ma suka sanshi, ga kuma abinda ya faru a kwanakinnan. Uffan baice da suba yay gaba abinshi, cikin takunnan nasa Na k'asaita da izza, Wanda a yanzu yak'ara armashi da 6acin rai. Su Ahmad da suka hango tahowarsa duk suka mik'e a tare suma suka nufosa, kallon mamaki yake binsu dashi, suma duksun lura da hakan. Gebiral yace, “Uncle!”. Kallonsa Galadima yayi idonsa sakaye cikin eyeglasses daya 6oye jajayen idonsa, kafin wani ya sake rmagana a cikinsu doctor ya iso wajen, duk hankalin su suka maida ga doctor d'in suna tambayar ya jikin Aunty?. Doctor yace, “ku kwantar da hankalinku, insha ALLAH komai zai zama normal, Ranka ya dad'e barka da zuwa”. Hannu kawai Galadima ya iya d'aga masa, a lokacinne suma su Abba Hayatudden suka k'araso wajen. A hankali Galadima ya bud'e baki yace, “Ina matata da d'an uwana?”. Cikin girmamawa Doctor yace, “Ranka ya dad'e inason magana dakai idan babu damuwa”. Kamar Galadima bazaiyi maganaba saikuma ya gyara tsayuwa yana fad'in “Inason ganinsu tukunna”. Doctor yay jimm baice komaiba. Hakanne ya d'arsa tashin hankali a zukatan kowa Na wajen, Galadima ya yunk'uro zaiyi magana doctor yay saurin taresa ta hanyar fad'in “Amma ranka ya dad'e namijin kawai, dan gaskiya ita ba'ason ayi wani kwakwkwaran motsi a kusa da itane”. Kowa Na wajen ajiyar zuciya ya sauke, danjin sunada rai, Galadima daya kasa koda motsi doctor ya kuma kalla, zaiyi magana ya d'aga masa hannu alamar baison jin komai. Abba Hayatudden da Baffi da sukasan halinsa idan yana cikin damuwa suka kalli doctor, baffi yace, “doctor yakamata ko shi kad'aine ya ganta, mu saimu duba Nuridden d'in”. A sanyaye doctor ya gyad'a kai, dan inda sonsamune babu mai shigar. Nurse ya had'a su da ita takaisu inda Nuren yake, amma kar ayi hayaniyar dazai farka, dan ana buk'atar yasamu barci sosai. Doctor kuma yayma Galadima jagora da kansa, amma a k'ofar d'akin suka cire takalmansu, dagasu sai sock's d'in k'afarsu suka shiga. 'Dakine madaidaicine da gad'o d'aya, asibitin sunada Kayan aiki babu laifi, tamkar an zarema Galadima lakar jiki haka yake takawa cikin sand'a, doctor ya nuna masa kujera guda d'aya dake kusa da gadon, idonsa a kanta tunda suka shigo, harya zauba yakasa janyewa, tana kwance sam6al a gadon tamkar wata gawa, kanta nad'e da bandeji alamar taji ciwo akan, dan har fuskarta tanuna saboda kumburi da tayi, alik'a mata oxygen a hanci Wanda da alamar shike taimakawa numfaahinta fita, ya maida kallonsa ga damtsen hannunta da shima yake anad'e, sannan kuma tafin hannunta ma haka, wasu hawaye masu zafi suka gangaro tacikin eyeglasses d'in idonsa daya hana ganin tahowarsu tun daga cikin idon. Ya kalli doctor da shima yake tsaye kansa duk'e a k'asa alamun damuwa, baice komaiba ya mik'e ya fito abinsa, doctor ya biyoshi a baya shima da hanzari. Da hannu yamasa alamar ya kaisa inda Nuren yake. Nanma shine yamasa jagora, duk inda suka gitta idanun mutane akansa, oho baimasan sunayiba, abinda ya dameshi shine gabansa. Su Abba Hayatudden suna d'akin har yanzu, shigowarsu Galadima ya sakasu juyowa suna kallonsa gaba d'aya, ya k'araso gaban gadon idonsa akan Nuren dake barci shima, saidai shi babu bandeji ko d'aya a jikinsa, dan baiji rauniba, dukansa da sukayi a kai ne ya sakashi suma, anama zuwa asibitin babu dad'ewa ya farfad'o, shine sukai masa allurar barci da saka masa k'arin ruwa danya huta, sanda zai farka ya farka da k'arfi a jikinsa.. Galadima ya durk'usa a gaban gadon ya kamo hannun Nuren cikin nasa, yana k'aunar Nuren sosai har cikin ransa, danshi mutumne simple, idan yamaka wani abun bazaka ta6a cewa shi jinin sarauta baneba, ko kad'an bashida damuwa a rayuwarsa, tunba yanzuba Nuren yake bama rayuwarsa gudunmawa, baita6a k'osawa ko gundura da halinsaba, balle yace masa bazaiyiba, saidai inhar abin baida tsarine zai bashi shawaran a canja kokuma ayi haka ko haka.......... Wayarsa datai ring ce ta katse tunaninsa, yad'an karkata yana cirota a aljihun wandon yadinsa, ring d'in daya sakama papi shi kad'aine ya sakashi fahimtar waye, ya mik'e daga gaban gadon yana picking call d'in, saida ya fice a d'akin gaba d'aya sannan ya amsa sallamar da papi yamasa cikeda girmamawa da tsantsar damuwa. Daga can ajiyar zuciya papi yayi, dan baiyi zaton samun Galadima cikin k'oshin lafiya hakaba, cikin tausasa Murya papi yace, “Muhammad kana inane?”. Shiru galadima yayi, kamar bazai iya maganaba, saikuma ya bud'e baki da k'yar yace, “papi asibiti”. “Asibiti kuma? Wanene babu lafiya?”. Kasa danne kukan daya taho masa yayi, ya fice daga cikin asibitin da sauri, mota ya bud'e ya shiga, ya kife kansa a sitiyari ya fashema papi da kuka mai tsima rai da 6argon jiki, gaba d'aya jikin papi yay sanyi lakwas, saima ya kasa magana shima, yay shiru kawai yana sauraren jarumin jikansa mai yawan hak'uri da juriya akan abu, saida yay kusan mintuna biyu yanayi, papi ya tabbatar nauyin da

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});