Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 51

Chapter 51

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sauran mata fintinkau wajen yin dace da samunka a matsayin miji, Uban y'ay'ana, Masoyina, cikon farincikina, I love you so more irin wadda bata k'arewa d'innan har a Aljanna....” “Na gode Uwargidana a Duniya da Aljanna, kece shugabar Matan Muhammad Sameer anan duniya, kuma kece a Aljanna insha ALLAH, ALLAH yayi miki albarka wadda bata yankewa keda gudan jinina”. Hannuna naima kisses uku Na hura masa. Ya wani lumshe idanu yana dafe k'irjinsa alamar sak'ona ya isa. Wata dariya mai ida kashe jiki murus nayi masa, aiko saiya zame ya kwanta kawai cikin kujerar yana kifa wayar a k'irjinsa ya lumshe ido. Nakuma bashi wani kiss d'in mai k'arar sauti, babu shiri ya d'auki wayar da Sauri saidai kitt Na yanke kiran ina dariya. Nima zubewa nayi a gadon k'irjinna Na dukan goma-goma, dayasan tsiyar da Na shirya masa dabai yarda dani hakaba😂🤭. Dariya kawai da tafi naji akaina, nai saurin bud'e ido, sainaga Ayusher, Munubiya, da Feena akaina. Hararsu nayi ina juya fuska can gefe da fad'in, “y'an sa ido, Uwarmiye aka biyoni?”. Ayusher tace, “Yo k'arshen munafurci da cika baki mukazo gani, yaudai munga abinda ake 6oye mana da cika baki”. Suka kwashe da dariya suna tafawa. Banza namusu. Feena tace, “Aini wlhy dama tun a asibiti nace muku gayunnanfa sun d'inke, wuya tayi wuya SIRRIN ZUCIYA ya fito fili, sun gama cika bakin da jan ajin, shi k'asaita da mulki, ita jan aji, Ashe harda Mulkin bamu saniba. Kai kusamana wak'a muyi murnan K'ulluwar k'auna”. Ayusher ta saka wak'a a waya suka ko dage suna tik'ar rawa.. Dariya suka bani wlhy, nace, “y'an iska kwadaiji da munafurcinku wlhy, nan gani nan bari dai Munafuncin su innaro”.. Aiko mi zamuyi inba dariyaba gaba d'ayanmu, nikaina Innaro d'ince kawai tazomin abaki ban shiryaba. ************************** Washe gari aka gudanar da bikin tarbarmu, Wanda yay matuk'ar k'ayatar damu da sakamu farinciki, munga al'adun daba namuba, su innarmu ansha shiga ta alfarma suda su Abba, Saiga su Abbanmu da sarauta, wai tunda sune mazajensu innarmu anbasu wata sarauta domin girmamawa agaresu, hakama Yaa Marwan, dad'i tamkar zai kashemu, aiko munsha hotuna da nuniya wajen jama'a. Gashi ni banda ma sakewa, saboda yanzu banason hayaniya mai tsanani kusa dani, da za'ayi kid'a ma sai wajen nabari tilas, dama hayaniyar mutane da surutai harta fara sakani ciwon kai. Da Galadima ya kirama sai Munubiya ce ta kar6a, ta sanar masa halin danake ciki, duk saiya rikice, yaringa rok'on Munubiya ta kula masa dani sosai. **************** Kwanakinmu 7 da zuwa cif mukaga anata hidimomi a masarautar, kasa shiru mukai saida muka tambayi dalili, su Badeera suka sanar masa wai wani d'an Sarki ne zaizo dana k'asarmu ta Nigeria. Mamaki ya kamani, to wanene wannan? Dan nidai ko a jiya munyi waya da gadima kuma baicemin zaizoba, hasalima yana India, tunanin bashi bane ya sakani kauda zancen araina muka cigaba da hidimominmu. Yanzu kam a masarautar babu inda bamu saniba, Dan kulum su Badeera cikin zagayawa damu suke, har cikin gari saida muka fita sau wajen uku, gaskiya Agadaz tanada abubuwan k'ayatarwa da Tarihi, hotuna kam ai yinsu muke tamkar babu gobe. Su Hajiya Innaro dai kam an nutsu, ni harma tausayi tafara bani wlhy, Dan haka muka rage iskancin da muke mata, yanda ake bata kulawa da girmamata kawai a masarautar ya isheta kunyar abinda ta aikata, (lallai babu Abu mafi dad'i irin ka sakama mai jifanka da sharri da tarin alkairi) wlhy har Abadan bazai sake sukuniba a gabanka saboda d'unbin kunya da nadama dazata addabi zuciyarsa, Dan kullum zai kasance cikin tsarguwa da tsangwamar kansane. Kunga dai yanda innaro ta kasance a yau.😏🤷🏻‍♀ Sai wajen la'asar sakaliya labari yazo mana wai d'an Sarki nan ya iso, bushe-bushen algaitu irin nasu kawai dake tashi ya tabbatar mana da lallai yazo d'in. Cikin mu babu Wanda ya maida hankali akan lamarin, danni kwance ma nake Na kifa Absurraheem saman cikina yana barci, Feena da Deejahma suna gefena zauna suna kallon hotunan da mukayo ayawon jiya da muka fita, su Munubiya kam Na tsakar d'akin suna hira da sauran y'ammatan, Ayusher nama Zuhuriyya kitso, Wanda anayi yana warwarewa saboda gashin akwai santsi, sai wata dabara sukeyi a k'arshen kitson. Bayan sallar isha'i saiga mama Rabi'a ta shigo d'akin da muke, duk muka gaidata, fuskarta d'auke da Murmushi ta kalleni ina canjama Amaturrahman kayan barci dan an musu wanka. “Munaya ta shi kiyi wanka yanzunan”. Da mamaki nace, “wanka kuma mama? Lafiya kuwa?”. “Lafiya lau, kedai ta shi kiyi, bama Maryamu ta k'arasa shirya Amaturrahman d'in”. Nidai duk al'ajabi ya kasheni, ganin duk yawan y'ammatan dake d'akin ba'ace kowa yatashi yay wankaba saini, suma dai Kansu kallon mamaki sukemin ni da mama Rabi'a d'in. Hannuna ta kama muka fice zuwa wani d'akin. Cikin bayin gidan d'aya ta had'amin ruwan wanka, dama tunda mukazo komai yimanashi akeyi. Mama Rabi'a tacemin “Kinutsu kiyi wanka mai k'yau wlhy, inba hakaba dakaina zan canja miki wani”. Mamaki kuma kasheni yayi, nadai nutsu nayi wankan fiyema da yanda take buk'ata, ga ruwa nata tashin mayataccen k'amshi, dan wannan masarauta sunsan sirrin k'amshi kam, akwanaki 7 d'inan har turare yafara zaunawa a jikinmu saboda bala'in yawan amfani dashi, motsi kad'an sai ahau tiraraki da turarurruka iri-iri. Nafito Na iske Ayusher Na jirana wai zatamin kwalliya, zanyi gardama saiga mama Rabi'a ta shigi, dole Na zauna akamin simple, nikaina nasan nayi k'yau, kayan da aka bani Na sanya saida Na kallesu Na sake kallo, dan lafayarsuce ta buzaye datasha wani d'inki mai k'ayatarwa, aka d'oramin bak'ar alk'yabba tamkar ta larabawa, tasha golden d'in aiki daga sama har k'asa, a bud'e take dawasu igiyoyi biyu, can sama dakuma tsakkiya. Nidai narasa bakin magana, dan turarema har neman hawarmin kai ya fara, kai nidai a raina nafara tunanin ko tsafi za'ayi danine. Sai gulma muke da idanu ni da Ayusher, dan babu damar yi a fili ga mama Rabi'a a d'akin. Hannuna ta kama muka fito, aka had'ani da bayi uku nabin bayana, sai ta hud'un a gabana tana mana jagora, masarautar tayi tsit babu yawan hayaniya, saboda d'an Karen sanyi da ake zubawa, kowa ya shige ciki sai d'ai-d'aiku dake kai kawo. Wani sashe dakecan gefe shima mai k'yau muka Isa, munsha zuwa ta wajen amma bamu ta6a shiga cikiba, Baiwar tayi sallama, dukda ba'a amsaba ta shiga, mukuma muka cigaba dabin bayanta. K'aton falone mai tarin k'awa da tsari, Wanda ke tabbatar maka a gidan sarauta kake, ganinai duksun durk'ushe k'asa, Na bisu da kallon mamaki sannan Na kalli inda suke fuskanta...................✍🏻 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [8/22, 8:29 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻2⃣4⃣ .................A hakimce yake kishingid'e saman lallausan dardumar data k'awata k'yawun falon, Rabin jikinsa duk akan tum-tum, gabansa da butar shayi ta buzayen asali, gakuma mitsi-mitsin kofuna saman wani k'yak'yk'yawan tire k'arami, gefe Bowl ne Na glass cikeda kayan itatuwa, saikuma kwanika 4 dake rufe Wanda bansan minene a cikiba, gefensa yaransa ne duka ukun kwance duk nad'e cikin showals, yanda nake binsa da kallon mamaki haka shima yake bina da kallon mamakin canjawa da k'ayatarwar da shigar ta k'aramin. Sudai bayinnan sun lalla6a tuni sun fice abinsu. Cikin d'age gira ya sakarmin Murmushi yana min nuni da hannu wai

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});