Chapter 66
Chapter 66
karmuyi tunanin ko irin nakane azo ba hakaba, Dan Na kula yafika yawan laulayi shikam, Abdurraheem baya had'a sati biyu da isashsshiyar lafiya”. Jin jina kai Galadima yayi, tausayin d'an nasa Na ratsashi, ya had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi da k'yar yana amsar Abdurraheem d'in daga hannunta. Abie daya shafa addu'a ya maido hankali garesu. Mik'ewa Galadima yay yakoma inda yake yana gaisheshi, Abie ya shafa kansa hakama Abdurraheem, cikeda tsokana yace, “Like Father like son”. Dariya Momma tayi, yayinda Galadima yay Murmushi mai k'ayatarwa har hak'oransa Na bayyana. Yace, “Abie ai dakai suke kama duka, Amaturahman cema tad'an d'ebo mamansu kad'an”. [8/19, 6:14 PM] 🙇🏻♀Da Rarrafe🙇🏻♀: Abie yay Murmushin jin dad'i, yana shafa kan Abdurraheem da yay barci, gaskiya Galadima ya fad'a, dan shima tun randa yafara ganinsu ya lura da haka. Sund'an ta6a hira, har Galadima ke kawo maganar Aunty Mimi akan yakamata tayi aure hakanan, domin zaman bashida amfani haka, ko wani yamaka k'yak'yk'yawar fahimta wani bazai makaba, tunda ba wuce auren tayiba. 100% iyayensa sun gamsu da zancensa, sunkuma amsa masa da isha ALLAH zasu zama Na musamman da ita. Kwantar da Abdurraheem yay musu sallama akan zaije yad'an rage barci. Tunda ya shigo yay tozali da Munaya barbaje a gado, murmushi yad'anyi yana cire Bottoms d'in rigarsa harya k'araso cikin d'akin, hanging d'in rigar yay sannan ya zauna saman sofa yana cire takalmansa, mitsawar da Munaya tayi tana juya kwanciya yad'ago ya kalleta, aransa yace hajiyata ko an farajin azuminne?. Harya gama hidimarsa yazo gefenta ya kwanta bata saniba, dayake ba motsi mai k'arfi yay tayiba, Dan yasan batada nauyin barci, gudun karta tashi yay tayin komai a sannu. *********** Duk musulmin ALLAH Na k'warai daya wadatu da ibada inhar lokacin salla tayi ko barci yake saiyaji a jikinsa, kokuma yayta mafarkin ana sallar, hakance ta kasance ga Munaya da Galadima, kusan atare suka farka, kowanne bakinsa d'auke da addu'ar tashi barci. mamaki ya kamani ganinsa gefena, Dan bansan yama dawoba, ya min murmushi nima Na mayar masa da murtani ina shafa fuskarsa. Cikin lumshe ido nace, “Yaushe ka dawo?”. Hannunsa ya d'ora saman nawa dake kan fuskarsa, yad'an rufe ido ya bud'e akaina, murya k'asa-k'asa yace, “Tun d'azun mana, kinata barci abinki”. Yatsine fuska nad'anyi ina zame hannuna da k'ok'arin tashi. Nace, “Wlhy barci bai wani isheniba shiyyasa nad'an rage yanzu kafin time d'in shiga kitchen”. Shima tashi yay zaune yana jinjinamin kai. Shiya fara shiga wanka, saida ya fito sannan nima Na shiga nayo. Koda ya fita salla ya dawo bai koma cikiba, sai suka zauna a harabar gidan shi da Abie suna hira, dayake kullum Galadima cikin bashi labarin abubuwan da suka dingi faruwa yay lokacin yana jiyya, wani yay murmushi, wani dariya, wani kuka, yana kuma yabama Galadima bisa ga gwarzan takar dayayi ta kare mutuncin ahalinsa da rik'e martabarsa. Har time la'asar suna zaune a wajen, da taimakon Galadima Abie yataka zuwa massalaci, dan inhar yana gida haka sukeyi, bayan sun dawo awajen suka sake zama, Galadima ya kirani nabama Samha System d'insa takai masa. Da to Na amsa, Na hau sama Na d'akko nabata. K'arfe biyar dai-dai muka shiga kitchen ni da Samha da kuku, sai Hadiman gidan guda biyu dake taimaka mana da wasu ayyukan. Cikin nutsuwa muka gabatar da dad'ad'an abincin bud'a baki, wasu namu Na Hausa wasu kuma Nan. Gab da magrib muka gama, munbarsu k'arasa komai Na k'imtsa kitchen d'in da shirya abincin. Wanka nakesonyi ga Amaturrahman Na kuka, Momma kuma tace babu inda zani saina shayar da ita. Dole Na zauna ina dungure kanta. Oho batasan ma inayiba, itadai taji abinda take buk'ata a baki kawai. Ganin tad'ansha na d'auketa muka haye sama dan karma Momma tace saita k'ara. Na iske Galadima yana wanka, ni bammasan ya shigo cikiba, Na kwantar da Amaturrahman Na kuma sauka, nasan dole yana d'akin za'a kira salla, dabino da ruwa Na d'oro a k'aramin tire nazo Na ajiye, ina ajewa kuwa yana fitowa. Sannu da aiki yamin, Na amsa ina manna masa Sumba a hannunsa dana kama, nai saurin shigewa bathroom. da kallo ya bita yana murmushi, ya kalla hannunsa data sumbata shima ya sumbaci wajen. Fitowata wanka yay dai-dai da cikar lokacin kiran sallar magrib, a bakin gado Na iskesa zaune Amaturrahman Na kwance kusa dashi tana wuntsil-wutsil da k'afafu, idonta nakan hasken globe, shikuma yana kallonta yana murmushi da video d'inta awaya. Batare danayi tunanin komaiba Na k'araso garesa da nufin bashi dabinon, amma saiya jawoni nafad'o jikinsa, dukda laimar ruwan dake jikina. Babu wani k'arin bayani ya d'aura bakinsa saman la66ana, idanu Na waro masa Na tsorata da mamaki, amma saiya kashemin ido d'aya da cigaba da abinda yake. Kusan mintuna biyu nasamu ku6ta. Ina yunk'urin tashi ya kuma hanani. “O ALLAH, azumi fa kakai my King, shine kafara da jan magana mai makon Neman ruwa ko dabino?”. Wani miskilin murmushi yayi da huramin iska saman ido. Farfar Na fara da idanu. Yakuma Murmusawa, “Bazaki ganeba babie na nayi missing d'inkine, kinga ai lada biyu, gatakai azumi gata d'abbak'a sunna, ni ai ga dabino Na nan, yawunki kuma shine ruwana”. Ya k'are maganar yatsansa a la66ana. Tura kaina nayi a jikinsa ina Murmushi. Ya rungumeni da shafa bayana shima yana murmushin. K'arshe dai sai a d'akin mukai sallar magrib sannan muka sauka k'asa shan ruwa. Jinai gaba d'aya kewar y'an gidanmu tazomin a yau, Na tuna yanda muke had'uwa k'wanmu da kwarkwata a runfa shan ruwa, murmushi naita saki dajin kewarsu mai yawa da d'okin son ganinsu. Aunty Mimi data lura dani tace, “My K'anwa yadai?”. Nakuma fad'ad'a fara'ata ina cewa “Na tuno gidane kawai Aunty”. Murmushi duk sukayi, Galadima dake gefena ya mintsini cinyata kad'an, d'agowa nai Na kallesa ina d'an 6ata fuska, gwalo yay min kad'an yana d'auke kai cikeda basarwa tamkar bashi yayiba. Saida na tabbatar bamai kallonmu sannan nima na rama, aiko zafin yasakashi kad'an garage ya 6arar da kunun da yake sha, yay saurin rik'ewa. Sannu muka shiga masa, na Fiske abina tamkar banyi komaiba. Muna had'a ido ya cije lips da min gargad'i da ido akan zai kamanine. Nima gwalo namasa. Abinda basu saniba tun farkon fara lamarin Abie da Momma suna kallonsu, dan haka yanzu sai suka kalli juna suna murmushi. A gurguje please⛹🏻♀😏 ★★★★★★★★★ Kwan uku da fara azumi Sauban ya iso India, bak'aramar birkicewa yay da ihun ganin Abie ya samu lafiyaba, hardasu kuka rurus, Abie ya rungume Autansa d'aya zama sangamemen Saurayi yana mai jin farin ciki da k'aunarsa. A ranar sai sabuwar murna ta tashi kuma, haka muka wuni cikin farinciki biyu, na zuwan Sauban da gimama farincikin daya riska. Haka azumi yacigaba da gangarawa, kullum saina kira su Abbanmu da sauran jama'ar gidanmu namusu barka da shan ruwa, hakama y'an uwana sunta turomin sak'on massages kenan kulum namin barka da shan ruwa. Azumi na kwana 15 muka kai Abdurraheem Asibiti, Yakuma samun binciken kwararrun Likitocin zuciya, suka dubashi da k'aramin dabaru wajen kula da rainonsa, sai magunguna da zai iya sha a matsayinsa na yaro k'arami. Dukkan sayayya da Galadima zaiyi ya kammalata, harma ya tura mana kayanmu ta jirgin ruwa. A kwanakin bashida wani sukuni, yawan shigi da fici na damk'a amanar harkokinsa kawai yake ga mutane, dan zai jima
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83