Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya d'aura mu a Kan sa" " Ma'isha ba kukan dukiyar nake ba ko wani abu ba a'a ganin Umma ta a cikin irin wannan halin shi yake tada min hankali ko kad'an bana son zubar hawayen ta, ba sanin mahaifina nayi ba shiyasa bana jin kewar sa duk da cewar na San na rasa gata na Amma Umma itace uwata itace ubana bazan juri ganin ta a haka ba" "I know how you feel insha Allah komai zai dai daita" "Allah yasa." "Ameen" Ma'isha sai surutu take Haisam kuwa sai aikin kallon ta yake tun baya kulata har ya Fara kulata suka Sha Hira sosai, a yayin da Mummy na chan tana rarrashin ummu, wannan Kenan. RANAR LAHADI Daddy na zaune a garden Yana karanta jarida, yayin da Haisam da Ma'isha na daga gefe suna Shan hirar su, mummy ce ta fito cikin Sauri ta miko Masa waya tace "Tun d'azu ake ta kiran ka da sabon number" Karba yayi ya Kara a kunnen sa banji me akace ba ya Mike yace "okay gani Nan zuwa" Mummy Tace "Ina Kuma zakaje?" Bai Bata amsa ba yace "Haisam maza d'auko makullin mota akwai inda zamuje" Da gudu Haisam ya shiga d'akin Daddy ya d'auko makullin motar ya shiga ya tada motar, Mummy Tace "Alhaji lafiya?" "Lafiya Lau police station zamuje kar ki fad'a wa Zainab sai mun dawo" ya shige motar suka fice daga gidan, mummy da Ma'isha suka kalli Juna, Mummy tab'e Baki tayi Tace "Allah ya kyauta. ________________________ Watan March 2022 ya kasance wata mara Dad'i a gare ni a cikin sati biyu na rasa mutane na kusa dani. Kakata ta rasu washe gari kanwar mahaifina ta rasu, basu cika sati ba cousin brother na da abokanan sa guda uku sukayi hatsari duk su ukun suka rasu, shiyasa duk na kasa typing naso ace kamun Ramadan na gama littafin Nan Amma kana naka Allah na nashi, dole zan dakatar da Rubutun sai bayan sallah insha Allah, Dan Allah kusa Yan uwana a addu'a, Allah ya jikan Musulmai idan tamu tazo yasa mu cika da imani ameen. Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 13 and 14 Da gudu Haisam ya shiga d'akin Daddy ya d'auko makullin motar ya shiga ya tada motar, Mummy Tace "Alhaji lafiya?" "Lafiya Lau police station zamuje kar ki fad'a wa Zainab sai mun dawo" ya shige motar suka fice daga gidan, mummy da Ma'isha suka kalli Juna, Mummy tab'e Baki tayi Tace "Allah ya kyauta." Ta shige cikin gida. Basu zarce ko Ina ba Sai police station,bayan sun shiga ciki Kai tsaye office din DPO suka shiga bakin su d'auke da sallama,ga mamakin su suka tarar da Baffan Haisam a zaune a cikin office d'in,DPO ya nuna was daddy kujerar dake gaban sa yace "bismillah yallab'ai" Ba musu ya nemi wuri ya zauna,bayan sun gaisa DPO yace "Nasan kayi mamakin Kiran ka da nayie ko?" Ya amsa da "Eh sosai ma" Gyaran murya DPO yayi yace "Dama malam Hassan ne ya bakaci ganin ka shiyasa ma na Kira ka" Daddy maida kallon sa yayi ga Malam Hassan yace "Ina sauraron ka" Malam Hassan yace "Na yanke shawara ne zan maida musu da dukiyar su" a gadarance. Girgiza Kai kawai daddy yayi yace "Ni Kuma ban amince da hakan ba, a lokacin da nake ta bibiyar ka da ka dawo da duk abinda ka San nasu ne Amma kamin kunnen uwar shegu, maganar kotu Kuma bazan janye ba Sai munje" Malam Hassan yace "A lokacin da kace na bayar banji zan iya bane ba Amma a yanzu na shirya" Daddy ransa yayi mugun 'baci sabida ganin yanda malam Hassan yake magana a gadarance, mikewa yayi yace "Haisam tashi mu wuce gida" ya nufi kofar fita, DPO yace "Yallab'ai Dan Allah ka tsaya" waigowa yayi yace "Na tsaya nayi me da na San sabida Shirmen Nan ka kirani wallahi da banzo ba" "Hakane yallab'ai dole ranka ya 'baci Nima cemin yayi zakuyi Sulhu shiyasa na Kira ka" ya maida kallon sa ga Malam Hassan yace "Malam Hassan ba haka mukayi dakai ba, Ce min kayi zaka nemi gafarar su kuyi Sulhu Amma ya za'ayi Kai da kake Neman Abu daga gare su kana musu magana a gadarance? Ka bashi hakuri ka fahimci juna don wallahi idan ka bari kuka shiga kotu da dukiyar d'an uwan ka da naka duk za a had'a a karb'a, Amma fa ba tilasta maka nake ba shawarace idan kaso ka d'auka" Malam Hassan Jin za'a raba shi da komai da komai ya Fara wiiki wiki da ido Nan take zufa ya Fara keto Masa duk da AC dake cikin office d'in, Chan ciki yace "Alhaji kayi hakuri Dan Allah" ya maida kallon sa ga Haisam yace yace "Dan Allah kasa baki Haisam" Haisam dake tsaye Yana kallon su yace "Daddy mu saurare shi a gama abin Nan once and for all ko ba komai hankalin Umma zai kwanta" Ajiyar zuciya daddy yayi ya koma ya zauna yace " Shikenan DPO wani formalities za a bi don a tabbatar da zai bada komai da komai don wallahi I don't trust him ko kad'an" "Kar ka damu yallab'ai zan kula da komai, Na maka alkawari Nan da 2 days zan kammala komai,amma zamu ciga ba da ajiye anan d'in ne ko Kuma mu sake shi?" " A a no need ai Ku sake shi" ya maida kallon ga Malam Hassan dake zaune a kasa ya nuna sa da manuniya yace "Mind you if try acting smart with me I'll deal with you and make your life miserable" Yana Kai Nan ya fice Haisam ya bi bayan sa, tunda suka shiga mota babu Wanda ya sake cewa komai har suka Isa gida. Horn Haisam yayi Mai gadi yayi saurin bud'e musu kofa, parking lot ya nufa yayi parking motar, Mummy , Umma da Ma'isha na zaune a garden d'in gidan suna jiran dawowar su, daddy d'akin sa ya wuce abinsa suna mishi sannu da zuwa ko kallon su beyi ba bare ya amsa. Haisam kuwa inda suke ya nufa ya nemi wuri ya zaunan, Mummy Tace "Son lafiya me ya Faru ne haka na ga ran Alhaji a 'bace?" Gyara Zama Haisam yayi ya fara jero musu yanda sukayi a police station, tunda ya fara magana suke kallon sa har ya Gama Babu Wanda yace komai, Mummy girgiza kai tayi ta tashi ta shige cikin gida, d'akin Daddy ta shiga taje tana ta aikin rarrashi. Ma'isha ganin Umma ta shiga cikin damuwa Ta d'an dafe kafad'arta tace "Umma wannan ba abin damuwa bane ba, tunda shi da kansa yayi ra'ayin zai dawo da dukiyoyin ai farin ciki ya kamata muyi, matsalar kawai gani nake bazai dawo dasu duka

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});