Chapter 53
Chapter 53
d'inki" tsaki Ayrah tayi ta shige motar, girgiza kai Mardiya tayi a zuciyar ta tace "Zanyi maganin kine" motar ta Shiga suka bar asibitin. Su Ma'isha kuwa tunda suka bar wajen napep suka Tara suka wuce gidan su Isha, a parlor suka tarar da Mummy da Umma gaishe su sukayi suka nufi hanyar Shiga d'akin Ma'isha Murya mummy sukaji tana fad'in "Ku Dawo Nan" Isha kallon meerah tayi itama ta kalle ta alamun Lafiya ta Mata da Ido Isha ta girgiza Kai alamun ban sani ba, jiki ba karfi suka Dawo had'e da neman Wurin Zama mummy tace "Isha ina miki kallon mai wayo da sanin ya kamata Ashe Baki da hankali ban sani ba?" Cike da rashin fahimta take kallon Mummy tun da ta fara maganar cikin rashin fahimta Tace "Kiyi hakuri Amma Dan Allah me Nayi?" "Kinci gidan ku Isha, nace Kinci gidan ku, uban me ya had'a kie da tsinanniyar yarinyar Nan Yar gidan matsiyata wacce bata gaji arziki ba?" Isha kallon Mummy tayi kana ta maida kallon ga Umma da fuskanta ya bayyana damuwa karara. Mummy ta ce "Ina Miki magana kin min shiru? Ko bakya jina ne?" "Mummy itace tazo har inda nake kawar Mardiya ce kanwar Ma'aruf shiyasa suka Zo tare Ni ban ma San ta santa ba sai da suka Zo d'azu" Meerah wani irin Kallo ta Mata hakan yasa mummy ta fahimci akwai abinda sume 'boyewa, "Meerah!!!" A 'dan razane ta kalli inda mummy take had'e da fad'in "Na'am" Mummy Tace "Akwai wani matsala ne?" "Umm mummy Dama..... Dama....." Isha tayi saurin katseta da fad'in "Dama Ya Haisam ne ya farka yanzu ma daga gunsa muke." Zumbur Mummy da Umma suka Mike a tare suka ce "Yana Ina?" Kai a kasa Isha Tace "Yana asibiti" Mummy Tace "Shine baki Sanar damu ba" Umma Kuma Tace "Alhamdulillah" Isha Tace "Mummy akwai wata Yar karamar matsala ce shiyasa ban Sanar daku ba" Umma Tace "wace irin matsala Kuma Bayan Wanda muke cikin ta?" "Ya farka har na ga kwayon idon sa Amma ya sake rufe idanun sa" Cikin rashin fahimta mummy tace "Ban fahimta ba me hakan ke nufi?" "hakan na nufin ya kusa farkawa" Umma zama tayi had'e da dafe kanta, mummy ma zaman tayi Isha kuwa mikewa tayi ta haura d'akin ta, Meerah ta bi Bayan ta. A bakin gado suka zauna Meerah Tace "meyasa baki Sanar musu Gaskiyar dalilin zuwan su ba?" Shiru tayi kamar baza ta amsa mata ba sai Kuma Tace "sabida dalilai guda biyu" "Me Kenan?" "Na farko Idan su Mummy sukaji dalilin zuwan su maganar fyade da aka miki da taimakon su zai zama ba sirri ba don tabbas Abba da Daddy zasuji harga Allah Ni ban so ma Ma'aruf yasan maganar ba sabida wannan sirrin ki ne" "Haka ne to mene ne dalilin ki na biyu?" "Dalilina na biyu shine idan daddy yaji abinda Kanwar Ma'aruf ta aikata na tabbata zai wargaza batun aure na da Ma'aruf Kuma bana son hakan gaskiya" Meerah rike habarta tayi kana Tace "I thought ba son auren kike ba?" "Eh bana so Amma su Daddy suna so ,so I have no option Dole nayi abinda suke so" "Toh Allah ya tabbatar Mana da alhairi, ranar ma ai tazo tunda saura Yan kwanaki ne, ya kamata mu Fara shirya events d'in da zamuyi" " Babu event d'in da zanyi Bayan walima, bani da ma lokacin wani abu bayan shi, Kuma kin San jibi zamu wuce Turkey da su mummy" " Hakane har na manta ma Allah ya nuna Mana, amarsu ta ango" ta karasa maganar cikin tsigar tsokana. Murmushi kawai Isha tayi suka cigaba da hirar su. Mardiya Bayan tayi dropping d'in Ayrah ta juyo ta koma domin zata gun aiki, Ayrah na Shiga cikin harabar gidan ta hango mahifin ta Yana rugume da wata yarinya matashiya wacce baza ta wuce sa'ar ta ba, Kan ta karaso inda suke har sun Shiga mota, ta gefen ta suka wuce waigawa tayi tana kallon motar , Mai gadi ya wangale gate d'in suka fita, Saida Mai gadi ya rufe gate d'in kana ta Shiga cikin gidan da d'an sauri sauri. Nabila Kad'ai ta tarar a parlor tana kallo Amma Sam hankalin ta baya Kai, magana take mata Bata ma jinta sai da ta tab'a ta a d'an razane Tace "Aunty kin dawo?" Ba tare da ta bata amsar tambayar da ta mata ba Tace "Wace ce wacce naganta tare da Abba?" Tab'e baki tayi had'e da fad'in "Karuwarsa Mana" Wani gigitaccan mari taji ya sauka a fuskar ta a razane ta Mike tana kallon wacce ta mare ta hannunta Akan kumatun ta sabida zafin Marin da taji. _________________________ Da fatan anyi sallah lafiya , Allah ya maimata mana , ameen. Milhaat ce Yar Terawa [7/18, 8:33 AM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 57&58 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ https://www.wattpad.com/1246873923?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp ```Continuation.......``` cikin Muryar kuka Tace "Mamy Mari?" Cikin hargitsi da d'agawa tace "Eh Mari idan na kuma Jin makamanciyar maganar nan daga bakin ki sai na sab'a ki wawiya Mara hankali, mahaifin ki kike had'awa da mugun kalma irin wannan" Ayrah cikin sanyin Murya Tace "Amma Mamy gaskiya ta fad'a Kuma kema kin San gaskiya ne, why won't you fight for your right?" Mamy tunda Ayrah ta fara magana ta kawar da kanta tayi kamar bata jinta, Ayrah ganin tayi shiru Kuma bata ga alamar zata kulata ba ta Kuma cewa "Mamy Dan Allah kiyi hakuri ha horo Haka Mamy, da wanne zanji Dan Allah da rashin kulani da kike zanji ko kuma da matsalar da take tsakanin ku da Daddy Wanda Nasan duk nice sila" Ajiyar zuciya Mamy tayi kana fuskanci Ayrah dake tsafe a bayan ta tace "Sam ba Wai bana son kulaki bane sabida abinda kuka aikata da mahaifin ki ba a'a so no na nuna miki kuskuren ki" Langwabe kai tayi Tace "Mamy Wallahi na gane kure na, 3 years ba wasa ba, Dan Allah mamy ki yafe min Kuma yanzu daga gun Haisam d'in nake ya farka" Murmushi Mamy
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76