Chapter 70
Chapter 70
"Ameen" " But fa ina son kawartar Nan Wallahi" Kallon bana son rainin hankali Adnan ya Masa kana yace "To wani sabon iskancin naka xaka Fara Kenan" "A a wallahi tallahi sonta nake Kuma da aure" "Hmm lallai fa" " Kana ganin zata amince kuwa?" "Can't tell, but try your luck" Bai Kuma ce masa komai ba har suka Isa inda zasu. Mardiya ce zaune a office d'inta ta Lula duniyar tunani, ajiyar zuciya tayi kana a bayyane Tace "Meyasa nake ji kamar akwai abinda Adnan yake 'boyewa? Anya Adnan baida sa hannu acikin 'batan Ayrah kuwa? Mtswww ko ma mene ne zan bin cika" ta d'auki wayarta ta Fara latsawa. Bayan ta Dawo daga gun aiki ta tarar da su Umma, abba, Daddy, Isha, Mummy da Twins Sannan da Auta suna dinning suna cin abinci suna Hira, manta jiki tayi tana kallon su, ganin yanda suke farin ciki basu da wata damuwa, tsanar Isha ne ya sake ninkuwa a zuciyar ta. "You don't deserve to be happy, yayana ya rasa ransa Amma ko kad'an abun bai dame ki ba, hankalin ki kwance dake da ahalin ki, to wallahi Ni zan Zama sanadin rushewar farin cikin Nan tunda Ayrah ta kasa, Allah sarki Mummy da Daddy, Ina kewar ku sosai Yaya kasance kana son farin ciki Isha sama da komai a duniya Amma Bata damu da Kai" magana take a zuciyar ta tana matsar kwalla, batayi aune ba sai jin murya Umma tayi Tace " 'yata kin Dawo?" Had'e da dafe kafad'ar ta. Umma kallon fuskar ta tayi, cike da tausayi tasa hannu ta share mata Tace "Ki daina Kuka Mardiya, nasan is not easy ki d'auke mu tamkar family d'inki kinji, ki cigaba da musu addu'a kinji" Girgiza Kai tayi cikin Muryar kuka Tace "Nagode Umma" ta fashe da wani irin kuka, Umma rungume ta tayi tana rarrashin ta, Suma kallon su suke suna jin tausayin ta Amma Banda Haisam ya rasa dalilin da yasa ya ji bai yarda da yarinyar Nan ba, cigaba da cin abincin sa yayi hankali kwance, Roku hannun ta Umma tayi har dining table kaita ta jaa mata kujera ta zauna , sannan ta karb'i jakanta ta ajiye mata daga gefe, plate ta d'auka ta sa mata abinci sannan Tace "kici abinci" ta shafa kanta kana ta koma mazaunin ta, shiru wurin yayi baka jin komai sai Karan cokula, abincin take ci Amma Sam bata jin dad'in da, taci Kad'an kana ta mike had'e da fad'in "Nagode, bari na shiga ciki" Mummy Tace "Ki samu kiyi wanka sannan ki Dawo ki same mu a parlor ki daina zama ke Kad'ai" cike da kulawa take maganar, Murmushi Mardiya tayi had'e da fad'in "to mummy." Bayan ta Shiga d'akin ta ruwa ta watsa duk jikinta a Sanyaye , Bayan ta gama ne ta zauna a bakin mirror tana shafa mai, karar wayar ta taji tana ringing, ta duba don ganin wane ne, number ta gani ba suna, tsaki tayi bata d'aga ba an Kira har a karo na uku kana ta d'aga ta Kara a kunnen ta ba tare da tace komai ba daga 'dayan 'bangaren akace "Assalamualaikum" Murya kasa kasa ta and da "wassalam" " Barka da war haka Hajiya Mardiya" Jin an Kira sunanta ta d'an d'aga girar ta kamar yana kallon ta Tace "Yauwa barka dai" tana son gane ko wane ne. "Suna na Abdallah, abokin Adnan" Yar karamar Murmushi tayi had'e da fad'in "Oh Abdallah barka kana lafiya, ya gajiyan ku na d'azu Nagode fa" Shima Murmushin yayi yace "Bakomai, da fatan kina Lafiya?" "Alhamdulillah" "Ya aikin? An taso ko?" "Eh" "Allah ya taimaka dama na Kira ne naji lafiyar ki" "Allah sarki Nagode sosaiii" "Goodnight" Ta amsa da Night. "Ayrah Wai meyasa kike da shegen taurin Kaine?" A tsawce yake maganar kallon sa tayi sama da kasa kana ta kawar da kanta, ajiyar zuciya yayi ya Saira kansa ya lura idan ya mata da zafi bazai tab'a samun kanta ba. Durkusawa yayi a gaban ta ya hard'e Hannayen sa alamun roko kana yace "Ayrah Dan Allah Dan Annabi give me chance na tabbatar miki da cewar ina son ki, so na Haki ka" Kallon sa tayi kana ta murmusa Tace "Naji zan amince da hakan Amma ina da sharad'i" "Ina sauraron ki just name it and Ni zan yi miki shi" Mardiya na Gama shafa mai simple duguwar Riga ta Sanya a Jikin ta kana ta fito parlor kamar yadda mummy ta umurce ta, hirar su suke hankali kwance, sunayi suna dariya. Wuri ta samu ta zauna had'e da fad'in "Mummy na d'auka Kun koma gida fa" Murmusawa Mummy tayi kana Tace "A a yau muna nan, Umman ku ta kafa ta tsare akan dole mu kwana" "har naji dadi zamu Sha Hira kam" Isha ta ce "Sai kace dama tana hirar" " Ina yi man, gashi nazo ayi Dani" "toh you're welcome" Haisam zaman ta a gun duk yasa yaji ransa ya lalace mikewa yayi had'e da Mika yace "Nikam zan kwanta, bacci nake ji, sai da safe" Duk suka amsa da Saida safe, Kallon Isha ya tsaya yi ita ma kallon sa take gira ta d'aga Masa alamun ya dai? Sai da ya tabbatar hankalin su Mummy baya kansu kana murya kasa kasa yace "I Love You" rufe fuskar ta tayi da tafin hannun ta tana Murmushi, Mardiya kuwa duk abinda suke Akan idanun ta, tsaki tayi Wanda yasa Haisam yayi saurin kallon ta, wani irin Kallo ya mata Wanda yasa tayi saurin kawar da kanta, tana jin kirjin ta na duka uku², Isha ta lura da sauyawan fuskan nasa, cikin sanyin Murya Tace "Ya Haisam what happened?" Murmushi yayi mata Kana yace " Nothing ki hau online" Yana Kai Nan ya haura sama bai tsaya jin me zata ce ba, bin Bayan sa tayi da Kallo, kana ta maida kallon ta ga Mardiya wacce ta manta kanta tana kallon Haisam d'in, Isha da d'an karfi Tace "Duk maita Mutum wannan halittan ya fi karfin sa" sai kuma tayi kamar ba ita tayi ba, Abba yaji abinda Tace Sarai Amma bai gane da wa take ba, kawai ya batsar. Mardiya kuwa hararar Isha tayi had'e da mikewa Bata ce musu komai , Babu ma Wanda ya San ta bar gun Isha kuwa Tace a ranta "sai nayi maganin Yar iska dani kike zancen" Datan ta ta bud'e suka cigaba da chat d'insu da Yayan ta, Yana nuna Mata shi sam Baya son zaman Mardiya a gidan, Isha da itama ranta a 'bace yake da Mardiyan sai ta danne 'bacin ran natan tana ta bashi hakuri. "Ayrah kinyi shiru? Fad'a min mene ne sharad'in naki?" "Na'amince zan aure ka" Wani uban tsalle Adnan yayi yana Fad'in "Yessssssss!!! Yaja yes d'in sabida tsantsar farinciki, ita kanta Ayrah abinda Adnan d'in yayi ya bata dariya, sai taji ya burge ta, matse dariyar tayi Tace "Not so soon, Kar kayi farin ciki tsaya kaji sharad'ina tukunna" Zama yayi a gefen ta Yana kallon ta yace "Uhmnn, ina jinki" "Zaka barni na koma gida daga nan sai muyi auren mu" Murmushin gefen baki yayi kana ya mike yace "Zaki koma gida Amma Nima kiji nawa sharad'in" Tana kallon sa don Jin me zai ce.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76