Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cikin gida. Ma'aruf kuwa natsuwar sa ya rasa yace "Wannan fa Yayan kine?" "Eh Yayana Ne" "Amma ya kuke dashi?" "My cousin, meyasa kake tambaya?" "No..... Bakomai naga Kuna Kama ne shiyasa" Murmushi kawai tayi gani kawai tayi ya mike yace zai tafi, ba don taso ba ta rakashi jikin motar sa, sai da taga fitan sa ta koma cikin gida. Kamar wasa Ma'isha tana final year kasantuwar pharmacy 5 years akeyi shi Kuma Haisam saura Masa shekara d'aya ya gama, Meerah kuwa ta dad'e da gamawa har tana aikin ta a medical center dake cikin garin gombe. Bayan Ma'isha tayi graduating Abba ya sa ma mata aiki itama a medical center hakan yasa kullum suna tare da Meerah, Haisam kuwa kullum cikin bibiyar Aysha yake da ta gabatar dashi gun iyayen ta Amma taki kullum amsar d'aya take bashi zan had'a ku idan lokaci yayi. Yau ma hakan Tace Masa "haba Habiby saurin me kake Ne Kam" "Aysha!!! Jikin ta ne yayi sanyi da jin yanda ya Kira sunanta ta amsa da "Na'am" tashi yayi ya zauna daga kwanciyar da yake wayan dake hannun sa ya maida d'ayan kunnen nasa yace "Anya kina Sona kuwa?" "Wannan wace irin tambaya ce Haka, kafi ko wa Sanin irin soyayyar da nake maka Kuma kake min irin Wannan tambayar?" "I doubt much gaskiya in dai dagaske kina sona ki barni na tura su Daddy gidan ku gudun Kar wani ya shige min" "Allah kar ka damu habiby next year fa zaka gama karatun ka kaga Ni Kuma sai Nan da 2 years na maka izini kana gamawa kazo ko da kuwa baka Sanar dani ba in yaso sai na gama a gidana ko" Dad'in maganar natan yaji Amma ya basar yace "Shikenan sai anjima zan Zo gidan" Da sauri Tace "A a kar kazo" Cike da mamaki yace "Meyasa?" "Umm.... Umm... Dama.... Dama Mom ce ta aike Ni zanje gidan kanwarta sai dai idan zamu had'u a Chan" "Okay wani unguwa ne?" "Federal low cost" "Oh unguwar mu nema idan kin Zo let me know" Bai jira yaji abinda zata ce ba ya kashe wayar, d'akin isha ya nufa ya tura kofar yaga wayam Bata nan. Layin ta ya Kira tana picking yace "Yau weekend ina Kika shi ne, tun safe ban ganki ba?" "Wallahi Yaya ina gidan Umma ne" "Shine baza ki fad'a min ba mu je tare?" "Am sorry na Shiga d'azu na ga kana baccine shiyasa" "okay Nima gani Nan zuwa" Ta amsa da "okay" sai ta kashe. Haisam dama da already yayi wanka Kaya kawai yasa ta fice, ya nufi gidan mummy, sai Bayan da iya sane ya tuna ya bar wayan sa a d'akin, ganin yanda Umman sa tayi kyau tayi fresh hakan yasa shi jin dad'i sosai. Umma na zaune a kasa, gata da babban ciki Wanda haihuwa yau ko gobe, Isha ganin tana wahala sosai ta fad'awa mummy zata zauna anan har sai Umma ta haihu Kuma ita kad'ai take aikin ta ga ciki, ita Ma'isha kullum mamaki take meyasa su Daddy basa son Yar aiki a gida. Aysha kuwa ta Kira layin Haisam yafi sau a irga har ta koma gida bai kirata ba , a ranar Kam raba dare yayi Yana rarrashin ta dakyar ya Samu ta hakura. Ma'aruf kuwa Duk sanda yake son ganin Isha Yana zuwa asibiti su gaisa sama sama yayi tafiyar sa ganin ta koma gidan su Umma yasa ya Fara zuwa gidan nasu, shi Sam bai San dalilin da yasa baya son ganin Haisam ba, Kuma hankalin sa ya kasa kwanciya shi duk tunanin sa Soyayya suke, sai da Meerah ta tabbatar Masa da cewar shakuwa ce kawai irin ba Yan uwa da Yan uwa. Wata Rana, cikin dare Isha taji Umma na Kiran sunan ta , da gudu ta fita ganin Umma a cikin jini yasa tayi matukar tsorata gashi Abba baya gari Sannan Kuma karb'an haihuwa ba 'bagaren ta bane, da gudu ta d'auko wayan ta ta Kira Haisam, kasantuwar unguwa d'aya suke bai Kai mintuna goma ba ya Isa da taimakon Sa da Isha suka sa ta a mota, suna Isa asibitin aka tabbatar musu da nakuda ce. _____________________________ Please comment Vote And share Milhaat ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 37&38 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........_ Haisam da Ma'isha na zaune a reception, Haisam Kam kwata kwata ya kasa nutsuwa ya zauna ya tashi ya fara kaiwa Yana kawo wa, ya dawo ya zauna. Ma'isha tausayin sa ya kamata sai ta tuno lokacin da Umma bata da lafiya, cike da kulawa Tace "Yaya please ka zauna Mana addu'ar mu take bukata a yanzu" "Princess wallahi na tsoratane sosai, mata suna wahala sosai wallahi duk Wanda yace zai tozarta mace ko ya wulakanta ta bai san ciwon kansa bane bare Kuma ace uwa" "Uhmn hakane Kam Amma fa ga Wanda ya sani, sabida wani abun idan kaji sai kaji Kamar Duniyar Nan an Tara zallan mahaukatane, kwanaki naji labarin wani ya Mari mahaifiyar sa akan kawai Tace Masa ya aske gashin Kan sa" "kin gani ko to wannan ina zaiga dai dai fisabilillahi" "Allah dai ya rabamu da iyayen mu Lafiya" Ya amsa da "Ameen summa ameen" Tace "Amma Yaya ka fad'a wa mummy zaka zo kuwa?" "A a wallahi a birkice na fito, Amma bara na Kira daddy" "shi da baya Nan?" "Eh gara shi d'in ya fad'a mata" "Toh" Kiran daddy yayi ya Sanar Masa shi Kuma ya Kira mummy ya fad'a Mata, mummy Kiran Haisam d'in tayi, tayi ta fad'a akan bai Sanar Mata ba suna Yara sun kaita asibiti idan ana bukatar wani abu fa, cikin Daren ta bugawa driver kofa kasantuwar yana zaune ne a boys quarters shi da Matar sa, d'auko motar sukayi gidan Umma suka fara nufa ta d'auko Duk wani abunda za a bukata kana suka wuce asibitin. Bayan

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});