Chapter 72
Chapter 72
and please ke Kad'ai zaki Zo." Ya katse wayar ba tare da yaji amsar da zata bashi ba. Farukh ji yayi kansa Yana mugun sarawa, ji yayi duniyar tana juya Masa, ji yake kamar ya fasa auren Amma wani 'bangare na zuciyar sa tana matukar kaunar Meerah. Isha ce naga ta fito, ta nufo su da d'an kuttun cikin ta, Bayan motar Haisam ya bud'e Mata, ta Shiga ta zauna kallon su take tana Jin gaban ta mugun Fad'uwa sabida yanayin da ta ga Farukh a ciki, murya na rawa Tace "Ya Haisam Lafiya?" Wayar Farukh d'in dake hannun sa ya Mika Mata, tana kallon video ta rike baki tana ambaton sunan Allah. "Inna lillahi, wannan videon a ina kuka same shi?" Da sauri Farukh ya waigo ya kalle ta yace "Kin San da videon dama?" Kai a kasa ta amsa da Eh. Farukh baki a bud'e yake kallon ta wasu sabbin hawayene suke gangarowa daga idanun sa yace "Kin sani fa Kika ce Isha? Amma kuma baki Sanar dani ba? Na d'auka ina matsayin Yayan kine kamar yadda kike Kirana Taya za a ce kin San halin kawar ki Amma ki bari na aure ta, Bayan kin San ita d'in ba alhairi ce a gareni ba" Isha cikin kuka tace "Tabbas Meerah tayi kuskure da ta 'boye maka, duk da nasan tayi hakan ne gudun Kar ta rasa ka kamar yadda ta rasa Bashir" "Ban gane ta rasani ba, me kike nufi da hakan?" "Wallahi ko kaffara bazanyi ba nasan wannan aikin Mardiya ne, ita kadaice zatayi hakan, Mardiya da kake gani ya Farukh, babu abinda baza ta iya ba don ganin ta 'bata Meerah, na rasa dalili Haka kawai ta d'auki Karan tsana ta d'aura mata, 8 years ago there where friends, Amma........ Nan ta bashi labarin yanda akayi mata fyad'e da yanda suka mata video da Kuma yanda suka mata barazana sannan suka rabata da mijin da zata aura a satin da Za'ayi bikin su. Ajiyar zuciya tayi Bayan ta gama bashi labarin, Jikin sa ne yayi sanyi , kallon Haisam yayi yace "Dama kaima kasan da maganar?" "Eh not long ago, bayan na farfad'o Isha take Sanar dani, nifa ko shiyasa duk na tsani yarinyar nan wallahi, bana son ta kwata kwata, Dole ma ta bar gidan Nan yau d'in Nan" "A a Ya Haisam Kar kayi haka Dan Allah su Umma baza suji Dad'i ba" "Amma Princess Kinga dai abinda tayi ko? Kika San mene ne Shirin ta na gaba?" " Ban sani ba , Amma inshallah ta Allah ba tata ba" Shiru yayi baice mata komai ba. "Ya Farukh" ta Kira sunan sa cikin sanyin Murya. Had'a Hannayen ta tayi wuri guda alamun roko Tace "Dan Allah, Dan Annabi, Kar kace zaka fasa auren Meerah wallahi tallahi ba laifinta bane ba, Bata San komai akai ba, wallahi duk sharrin Mardiya da Ayrah, idan kace ka fasa auren ta zuciyar ta zata karye Dan Allah" ta karasa maganar tana kuka sosai kamar ranta zai fita,haisam hankalin sa yayi mugun tashi,don shi idan akwai abinda ya tsana shine yaji ko ya gani Isha na cikin damuwa bare ma ace tana kuka. Murmushi gefen baki Farukh yayi yace "Ki daina kuka Isha, bazan fasa auren ta ba, hasali ma labarin da Kika bani ya sa naji ina bukatar na rayu da ita zan goge Mata wannan bakin tabon da aka Mata, Kuma zan miki wani alkawari sai Nasa an d'aurte wallahi wallahi bazan tab'a kyale ta ba" Murmushi Haisam yayi yaji dad'in maganar abokin Nasa,su isja sarkin kuka Kuma Aka cigaba da kuku. "Ya Salam Princess,kukan Nan fa na mene ne,inace ya fad'a miki baza a fasa auren ba,meyasa Kuma kike kuka,kin San fa bana son kukan ki" Cikin Muryar kuka tace "Ya Haisam, Dole nayi kuka ina tausayawa rayuwa tane dana Meerah,tun tasowar mu,bamu samun abinda muke so,idan mun gama da wannan matsalar sai wata ta 'bullo" ta karasa maganar tana kuka Mai sauti, Haisam rarrashin ta ya Shiga yi yace "Ma'isha" Cike da mamaki ta d'ago tana kallon sa,don a iya zaman su dashi bata tab'a ji ya Kira sunan ta ba,idan ma ya Kira to ta manta, Murmushi yayi kana yace "Ni Haisam na miki alkawari zan share duk wata kunci da damuwar da kike ciki,kawai dai wannan d'an nawa na cikin ki ne yake katse min hanzari" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka Isha kuwa hakan dariya ya Bata,tana kuka had'e da dariya. Farukh yace "Wa yace maka namiji ne?" "A jikina nake Jin hakan" "Mtsww dallah malama ka tada mota mu tafi ya fa rana na ce, nasan suna chan suna jiran mu" Dariya Haisam yayi ya kalli Isha kana yace "Princess ki Shiga ciki ko,zan Zo na d'auke ki anjima,kin San Umma Tace Kar na bari ki kai la'asar so ki kasance cikin shiri" Ta amsa da toh, had'e da bud'e marfin motar, Farukh ne yayi saurin fad'in "Dan Allah ki kwantar da hankalin ki auren da Meerah babu fashi sai dai idan mutuwa nayi, Sannan please bana so ki fad'awa Meerah ko ki nuna Mata cewar an turo min wani abu,ita Kuma wannan Kanwar zanyi maganin ta" Dariya sukayi dukkan su, Haisam yace "me Kuma kanwa?" "Kanwa mana,kanwa uwar gami had'a su kasa rabasu" Dariya suka Kuma yi cikin dariya Haisam yace "Princess jeki suturun sa ba karewa zaiyi ba" ficewa tayi ta shige,ai kuwa Isha na Shiga, Meerah na ganin ta ta fahimci akwai matsala,Jan ta tayi suka keb'e tana tambayar ta dalilin da yasa ta ganta a haka,Isha Tace Mata bakomai,ganin Meerah ta nace yasa Tace Mata marar ta ke mata ciwo,ta Mata sannu sannan suka Koma cikin kawayen nasu. Dubbanin Mutane ne suka shaida Auren Dr Farukh Sani Usman da Ameerah Murtala, cikin mutanen kuwa harda Daddy da Abba. Mardiya ne kwance akan gado,tana taunar chewn gum wata iriyar dariya tayi,Zama tayi Tace "waima taya Za'ayi kiyi aure Ni banyi ba? Dr Farukh? Hmm kyakkyawan saurayi haka bai dace dake ba Sam dani ya Dace,na tabbata duk inda yake yanzu yaga sakona" ta Kuma fashewa da dariya. Muryar Umma taji tana Kiran sunan ta kanta amsa har ta Shigo kallon ta Umma tayi Tace "Lafiya ke da waye?" Murya na rawa Tace "Ummmmmm....waya nake" "Ok ,ya naga baki shirya ba baza ki bikin bane?" " Wani biki Umma,Bayan an fasa bikin?" " Wani bikin ne aka fasa? Bayan tun karfe 11 aka d'aura aure" Zumbur ta Mike Tace " No no inaa bazaiyu ba, wahala na ya tashi a banza Kennan?" Umma Tace "Ke Lafiyan ki kuwa?" Shan jinin jikinta tayi ta zauna ta ce " kaina ke ciwo Umma,sai kun Dawo" wani irin Kallo Umma ta mata har ita mardiyan ta tsargu,ta fice abinta,tare da mummy zasuje tana jiran ta a parlor tana Isa parlor sukayi tafiyar su. Ciza leb'en ta tayie kana Tace "wato Farukh ya auri Meerah? Ko dai baiga sakon bane? Anyways idan ita Meerah ta tsira, Ma'isha baza ta tsira ba muje zuwa, wallahi sai na ga Bayan ku,I'll disgrace you to extend that you'll be ashamed of yourselves." Ta kwanta ta cigaba da danna wayanta tana jinra duk ba dad'i. Umma da Mummy dasu akayi bud'an Kai da kamu,a ranar amarya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76