Chapter 14
Chapter 14
cewar yace zai kirata dafe kansa yayi yace "Am so sorry Aysha na d'anyi busy ne gafar ce ni" Murmushi tayi ko ba komai bai manta sunan ta ba, tace "Bakomai yallab'ai Ni da na damu da nayi magana da kai ai na kiraka" Murmushi yayi yace "Afwan ina jinki" "ummm dama ba wani abu bane ba, so nake Dan Allah ka Zama Tutor na" "Tutor dai? 'dan Ni d'in Nan bani da wannan ilimin ai Ni dolo ne fa" Yar karamar dariya tayi Tace "na amince ka koya min dolon cin naka, duk da nasan Kai ba dolon bane ba sai dai in rowa zaka min Kar na karu da kai sai na hakura" Murmushi yayi yace "Toh yaushe kike so mu Fara?" Tace "Ko gobe ma" "A a gobe Sunday ba inda nake zuwa ina gida, ki dai bari idan muka had'u Monday mayi maganar" Cikin murna Tace "Toh nagode sosai" "Bakomai sai da safe" Ya katse wayar Aysha bin wayan tayi da kallo tace "Mtssw ya katsewayar kamar shi ya Kirani" wurga wayan tayi akan gado ta kwanta ta fara sharar baccin ta dama ta Riga ta shirya cikin kayan baccin ta. Ma'isha kuwa ganin bai mata reply ba tayi tunanin ko bacci ne ya d'auke sa, ta shiga kiransa Amma busy, ji tayi kamar ta kurma ihu, cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga wanka ta d'aura da alwala,bayan ta fito tayi shafa'i da wutiri bayan ta idar ta shiga rokon Allah da ya yaye Mata sayayyar da take Masa in shi d'in ba alhairi bane a gareta ba, in ko alhairi ne yasa ya Sota kamar yadda take son. Wayar Tace ta fara ringing tana dubawa taga yayana Yar karamar tsaki tayi Tace "wato ya gama waya da ita" Sai da ya kusa yankewa ta sa hannu ta d'aga ta Kara a kunnen ta, yace "Haba princess kin shanyani bacci Kika yine?" "a'a wanka na shigane" "Shine baki fad'a min ba?" "gani nayi kana wayar da tafini muhimmanci" " Ki daina fad'in haka princess waya nake da wata course mate d'ina" "Oh mace ce ma ko?" Yace "Eh" "Na sani ai" "Me Kika sani?" "Babu komai" " To hau online d'in mu cigaba da hirar mu" Tace "Nikam bacci zanyi kaina ke ciwo" Babu yanda baiyi ba ta hau Amma taki hakan yasa ya kyale ta,katse wayar yayi, yayi wurgi da ita Yana tsaki yace "Yau na kasa gane Kan yarinyar Nan ko me ya same ta oho" Da wannan tunanin bacci yayi awun gaba da shi. Ma'isha kuwa kasa bacci tayi, tana kuncewa sa sakawa idan har bata mallaki Haisam a matsayin miji ba zata iya samun matsala, Kila ma ta rasa rayuwar ta a dalilin hakan, Amma meyasa haryanzu bai nuna Yana sonta ba? A bayyane Tace "Ya Allah kasa Yayana Yana Jin abinda Nima nake ji akan sa, Allah yasa ba Ni kad'ai nake haukataba" a Haka har bacci ya d'auke ta. WASHE GARI Ma'isha tunda tayi sallar asuba ta koma bacci bata tashi ba har sai da aka Fara Kiran sallar azahar, tana farkawa wayarta ta fara dubawa taga missed calssy da dama, amma na haisam yafi yawa harda texts shi a tunanin sa fushi ta Kuma yi dashi. Murmushi kawai tayi ta tura Masa text *"am sorry Yaya na bacci nake , wayar na silent ne shiyasa banji ba"* Yana gani ya Mata reply da *"okay idan kin shirya ki Sanar dani Ina d'akina sai na kai ki saloon d'in"* Ta amsa reply da *"Alright"* tashi tashiga wanka,sai da tayi sallar azahar kana tashirya cikin wasu lallausar riga da siket na voyel less dark blue wanda aka mata ɗinkin tamkar ajikinta aka dinka yayinda adon jikin kayan pink ta yafa pink din mayafi da takalminta hill da kuma handbag ɗinta pink yar karama ,ta saka wayarta aciki ,Batayi wani kwalliya ba abisa dabi'arta na rashin damuwa da ɓata fuskar ta wajan ciki masa hayaniyar kwalliya ,Ta fesa turaren ta mai kamshi ta fito. Tana fitowa ta samu mummy da Umma a parlor suna Hira sannan suna Kallo sama sama Umma tace " masha Allah daughter kinyi kyau" Ma'isha kanta akasa tana murmushi tace "Nagode umma " Mummy Tace "Yau sai ina Haka?" "Saloon zani" "uhmnn" kawai Tace Tace "Sai mun dawo" Mummy kallon ta kawai tayi Umma Tace "A dawo lafiya,Allah ya tsare" Ta amsa da Ameen, part d'insu Haisam ta shiga Kai tsaye d'akin sa ta nufa,ta tarar ya gama Shima hakan yasa basu 'bata lokaci ba fita sukayi atare, sadaddiyar mota suka shiga da Alama sabuwace an wanke ta sai sheki take. Bayan sun shiga motar ya kalleta ta yace "Princess irin wannan kyawu Haka, kamar Zaki je gasar sarauniyar kyau" Turo baki tayi cikin Shagwab'a tace "Sai yanzu ka ganni?" Dafe Kai yayi yace "kefa na lura Sam bana Miki gwanin ta ko?" "Ni dai bance ba, ai tun Shiga na d'akin yakamata kace nayi kyau"for "kyau din naki ne yayi yawa baki ga sai kallon ki nake ba na kasa magana,Kuma nayi maganar baki ji bane, yanzun ma dakyar maganar ta fito" Dariya kawai tayi tana Jin dalilin kalaman sa masu sanyaya zuciya, shiyasa Bata gajiya da magana dashi bataki ace tana tare dashi ba a ko wani lokaci ba. Sunyi tafiya kusan na minti uku sai Tace "kaima fa kayi kyau sosai Yaya" "Au ramawa zakiyi? Sai yanzu Kika ganni Kennan?" "A a na Isa ramuwa Kuma, tun d'azu nake son fad'a maka cewar kayi kyau sosai Amma ya kasa fita yanzun ma dakyar sai da na dage na furta" Dariya ya Shiga yi, itama tana dariya tuki yake a hankali har suka Isa saloon ta fita shi Kuma ya zauna a mota Yana jiran ta. Fitar ta ke da wuya wayar sa ta Fara ringing Yana dubawa yaga Aysha, picking yayi bayan sun gaisa ta Fara Jan shi da Hira har ta a ka Gama wanken Kan nata suna waya da Aysha bud'e motar tayi ta zauna, yace "Aysha am sorry please zan kira ki anjima" Tace "Tohm bye" ya katse wayar. yace "Princess har kin Gama?" " yau Kuma Yaya? " "Yau Kuma me? " "To ai ka Saba cewa na dad'e ne,yau Kuma nayi sauri ko?" Dariya yayi yace "Wallahi Aysha ce ta ke ta bani dariya" "Wace ce Aysha Kuma?" "course mate d'inace" " Wato da ita yake waya Kennan jiyan ma koma wacece ke baki Isa ki rabani da Yayana ba,baki Isa ki rusa min ginin da na dad'e ina ginawa ba" take ayyanawa a ranta. Tafi yayi Tace "Na'am" "Lafiyan ki kuwa tunanin me kike haka?" "Bakomai bacci nake ji yaya" "Shopping d'in fa?" " Na fasa mu koma gida kawai" "Ikon Allah yau wa zai Mutu princess ce tace Bata son shopping" Kirkirerren Murmushi tayi yace " Your wish is my command" Ya tada motar suka bar gun. Suna Isa gida bata tsaya jiran sa ba ta bud'e motar ta fita, tarar da su Mummy ta musu sannu ta shige d'akin ta. Umma Tace "mutanen ki sun fara" Mummy Tace "Chan ta matse mu Basu da damuwa ne ko kad'an" __________________________ Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76