Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 39

Chapter 39

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ayyanawa a ransa, ganin Shirun yayi yawa Ma'isha cikin kuka Tace "Daddy me ya sami yayan, me ya faru haka har ya suma? Kuma naji kace yana aman jini how comes" Daddy kasa magana yayi haka ma abba, dukkanin su basu tunanin kowa sai Umma. Inda Farukh yake ta nufa cikin kuka Tace "Ya Farukh Dan Allah ka fad'a min me ya faru nasan kana gun kasan me ya sa meshi" Nan ya Sanar mata da komai Duk da shi bai San me dangantakar ta da Haisam ba, Umma fashewa tayi da Kuka Kan mummy ta karasa inda take tsaye ta Fad'i a sume, da gudu sukayi kanta, mummy Ce ta fara Kiran sunan "Nurse Nurse" nurses biyune suka karaso inda suke da gudu, gado suka d'auko suka tura ta suka kaita d'akin da yake kusa da Haisam,Nan Nan likitoci sukayi kanta. Abba Zama yayi a kasa ya fashe da kuka, kuka yake Sosai Kamar karamin yaro daddy ne ya durkusa a gaban sa yace "Haba Abdallah mene haka kake kuka Kamar wani karamin yaro, be a man mana." Cikin kuka yace "Dole nayi kuka Yaya Dole nayi kuka, why me? Why me wani laifi nayi wa Allah da yake horani Haka first was fauziya with my four kids and now Zainab and Haisam sannan fa Tana da karamin ciki, Yaya ina tsaron rasu Suma don wallahi idan na rasa su kuma zaku rasani" Daddy yace "Subhannallah haba Abdallah Kar kayi sab'o Mana, Allah Yana sonka Allah Yana jarraba bayin sa da yake so ne, ka d'auki hakan amatsayin kaddarar ka" "I can't Yaya bazan iya ba, fi kowa Sanin halin da nake ciki I was a sad and lonely man over 25 years sai yanzu da na fara samun kwanciyar hankali Kuma ace na rasa wannan am back to square one" Ma'isha kasa jurewa tayi ta bar gun ta na kuka mai tsuma zuciya, Farukh ne yabi bayan ta don ya samu ya kwantar mata da hankali kasantuwar yasan tana da ciwon zuciya. Abba sai surutai yake Kamar ya fara zarewa, mummy itama kukan take daddy ya rasa yadda zaiyi mikewa yayi yana safa da marwa ji yayi Mummy ta fashe da "Ihu Innalillahi wayyo mun Shiga uku da gudu tayi Kan Abba da ya Fad'i Daddy shima yayi kansa yana jijjiga shi yana Kiran sunan sa, nurses d'in da suke Kan Umma ne suka fito da gudu da taimakon Daddy suka kai shi d'akin da mummy ke ciki suka kwantar dashi a gadon dake gefen nata dama d'akin gadaje biyu ne aciki, Nan da nan wani likitan ya shigo shima ya fara duba shi. Mummy kuka take Sosai daddy ne ya rike ta suka fita suka zauna a kan kujera irin Wanda ake ajiye wa a ko wani ward, kwantar da ita yayi Yana d'an bubbuga Bayan ta yace "Ki daina kukan Nan please addu'a suke bukata a yanzu Dan Allah kiyi Shiru" "Alhaji taya za'ayi na daina kuka, son fa da Zainab Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ga Nan Abdallah shima Wallahi tausayin sa nake ji, a cikin Yan awanni ta fita hayyacin sa" "To ya zamuyi? Haka Allah yaso Dan Allah I need you now kukan ki na tada min hankali Dan Allah Kar ki daina kina karya min zuciya" shiru tayi bata sake cewa komai ba ta cigaba da kukanta, shi Kuma bai daina bubbuga Bayan ta ba a haka har ta d'an samu relief. Likitocin Dake d'akin Su Abba da Umma ne suka fito a tare d'aya daga cikin su yace "Ku kwantar da hankalin ku, Suma sukayi duk su biyun, munyi musu allurar bacci zuwa anjima kadan zasu farka" Daddy ne ya amsa da "Mun gode" sukayi wucewar su, Bayan sun tafine likitocin da ke kan Haisam suka fito su uku, shugaban sune yace "Me ya sami Dr Haisam Haka?" Shiru sukayi d'ayan yace "Ya kamata musan me ke damin sa sabida musan ta yanda zamu 'bullo wa al'amarin" Daddy yace "Nasan Kun San yau ranar d'aurin auren sane ko?" A tare suka amsa da "Eh mun sani" 'dayan ya d'aura da fad'in "maganar zuwa gun dinner sa ma muke aka Sanar da mu an kawo patient Emergency, ga mamakin mu da muka zo muka tarar ashe shine Mara lafiyan" Ajiyar zuciya Daddy yayi yace "Auren ne aka fasa" A tare suka ce "subhannallah Abu baiyi dad'i ba" Sai kuma sukayi shiru suna kallon junan su. Farukh ne yabi bayan Ma'isha inda Meerah take ta nufa Meerah na ganin Isha a haka ta yi saurin tare ta had'e da zaunar da ita tana fad'in "Lafiya Isha? Me ya same ki Haka? Mutuwa akayi ne?" Muka take Banda sunan Haisam babu abinda take kira, cikin kukan ta Sanar da ita abinda Aysha tayi ka karasa maganar da fad'in "I know something was fishy about her,Ya Haisam ya cutar dani Kuma ya cutar da kansa Bayan irin Soyayyar da nake Masa Amma Baya gani Akan sa fa na kamu da ciwon zuciya,Ashe haukata kawai nake akan wata fa ya shiga halin da yake ciki"ta karasa maganar cikin kuka. Farukh Bayan ya karasa inda suke Jin maganar da Ma'isha keyi ya jaa da baya ya tsaya don Jin abinda take fad'a,sai da ya gama jin maganar da take ne ya samu gu ya zauna yace "Isha Yayan ki fa ba mutuwa yayi ba Suma yayi kuma Wallahi shima yana sonki kawai na kasa gane wane dalili ne yasa ya kasa fahimtar hakan, Dan Allah ki daina kukan Kuma Insha Allah hakan da ya faru zai Zama alhairi kinji" Meerah hannu tasa tana share mata hawaye Tace "kinji ko ai na Sha fad'a miki shima yana sonki, da ace kin bi shawarata kin Sanar Masa da Duk wannan bai faru ba" Farukh ne ya amsa da "Wannan hakane Amma kin san bamu muke sarawa kanmu Rayuwa ba we plan but Allah knows what is the best for us, kawai dai sai dai muyi fatan dacewa" Nan sukayi ta mata baki har ta samu ta daina kukan, sai ajiyar zuciya take sabida tayi kuka sosai Farukh pharmacy ya nufa ya Saya mata magani kana ya sayo ruwan sanyi bai dad'e ba ya dawo ya Mika Mata ta Sha, Duk su ukun suka nufi inda Su Daddy suke, suna Isa ganin daddy da mummy a tsaye sai Kuma likitoci biyu a gefen su, Farukh Mika musu hannu yayi suka gaisa yace "Dr Musa, Dr Sani ya jikin Haisam d'in hope everything is okay?" Dr musa yace "Gaskiya Akwai matsala Dr Farukh" Ma'isha Tace "Please Dr Musa wace matsala Kuma Bayan Wanda muke da ita a yanzu? Me ya sami Haisam d'in? Ko dai ya mutu ne kuke 'boye Mana?" Ta Karasa maganar tana matsar kwalla. Dr sani yace "No no bai mutu ba Pharm isha, yana Raye" "So tell me, what's wrong?" Ajiyar zuciya yayi yace "Ya Shiga comma." Ma'isha jaa da baya tayi ta jingina da jikin bango tana girgiza Kai had'e da fad'in "Shikenan Shikenan Shikenan Nima lokacin mutuwa ta tazo" Farukh yace "Haba Isha sai kace ba health practitioner ba? Kin fa San yanda comma take wani aranar ma zai farka wasu Kuma sukan d'auki sama da shekaru 20 suna comma Kuma ana sa ran zasu farka

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});