Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 69

Chapter 69

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ke wurina nayi amafani dasu wurin gina maka asibiti, sannan na zuba maka ma'aikata aciki Ana gudanar da aiki yanda ya Kamata, a gaskiya Haisam ka samu aboki na Kwarai, da taimakon Farukh ne komai ya tafi dai dai tun Bayan wannan lokacin shi yake kula da komai, a halin Yanzu asibitin yana d'aya daga cikin manyan asibitocin da ake ji dasu a garin gombe, sannan na gina maka gida, na zuba maka dukkanin abubuwa na more Rayuwa" Mikewa Haisam yayi ya rungumi daddy yana kuka kamar wani karamin yaro Yana ta Nagode Allah ya saka, daddy Murmushi kawai yake Yana d'an bubbuga Masa baya alamun rarrashi, Umma ma godiya ta Shiga Masa, tana Kara godewa Allah da Ma'isha sabida itace silar komai, shiysa take matukar son Isha, fiye da ka yadda take son Haisam d'in, Abba yace "Kan mu shigo, mun biya gun Dr Ali yace anjima da Yamma za'a sallame ka" "Alhamdulillah dama Wallahi na gaji da asibitin Nan, Yamma tayi ai Abba" Duk dariya sukayi. Suna cikin maganar ne sai ga shigowar Dr Ali, Bayan sa biye yake da wata nurse hannun ta Kuma rike yake da patient file, Bayan sun gaisa ya Shiga Duba Haisam, Bayan ya gama ya rubuta Masa magunguna da za'a saya ya mikawa Ma'isha had'e da fad'in "Pharmacists a samawa patient magani" Karb'a tayi tana dariya tace "Ai na samu hutu" " Yet ke staff d'inmu ce" Charafff Haisam yace "She was dai, don Canza mata wurin aiki zanyi" girgiza Kai Isha tayi Dr Ali yace " Fatan alhairi" sai ya fice nurse din tabi Bayan sa. Tattara kayan su Umma da Mummy suka farayi Isha ma bata zauna ba da ita ake had'awa su Daddy da Abba Kuma suna Kai kayan mota, farin cikin da Umma take ciki bazai misaltu ba yau Bayan shekaru 4 d'anta zai Koma gida, har kuka Saida tayi mummy na ta aikin rarrashin ta. Bayan sun gama kai tsaye gidan Umma suka nufa Haisam zai zauna a gunta Kan ya gama murmurewa, Isha dama already tana gidan Umma, Ni ko nace Anya zaman Isha, Haisam ga Kuma mardiya zaiyu kuwa a gida d'aya? Muje zuwa. Mardiya Bayan ta koma gida ta shirya cikin doguwar rigar atamfamfar ta, Atamfa less ne, brown an Masa Flowers da kallan ja da yellow sannan less d'in Jikin farine hakan yasa tayi Rolling da d'an figegen gyale fari hannun ta Kuma rike yake da labcoat d'ayan hannun ta Kuma fashion bag d'intane shima fari Sannan takalmin ta ma fari, a gogon hannun ta take Kallo sai Kuma tayi Tsaki , a bayyane Tace "wannan Wace irin Rayuwa ce, a gaskiya zan d'auko mota na tun d'azu nake ta jiran abun Hawa Amma babu." Wata dankararriyar mota ce tazo ta faka a gaban ta, ta kawar da Kai Jin an Kira sunan ta Yasa ta kalli Wanda taji ya Kira sunanta Tace "Laaaa Adnan" Murmushi yayi yace "Mardiya manyan gari ana ganin ku dama?" Itama Murmushin tayi Tace "Gashi kuwa" "Hakane, ina zaki ne haka?" "Gun aiki ina ta jiran napep Amma ban samu ba" "Hoop In Mana mu rage Miki hanya" Ba musu ta bud'e gidan baya sabida daf take da yin latti,jaan motar yayi yace Mata "Wani asibiti kike aiki?" "Specialist hospital" "Okay " Babu Wanda yace komai sai chan yace "Wannan abokina ne sunan sa Abdallah" "Barka" Shima ya amsa da yauwa barka,nan suka fara hirar yaushe gamo,suna Isa specialist hospital har ta bud'e marfin motar Tace "Baka tambayeni mutuniyar ka ba?" Sai da yaji kirjin sa ya fara duka uku² cikin rawar murya yace " Wa Kenan?" "Ayrah Mana" "Ummmm...... Ya take ne? Tayi aure ko?" " Wai kana nufin baka ji abinda ya same ta?" Gyara zama yayi ya waigo Yana kallon ta kana yace " A'a me ya same ta?" _______________________ Please comment And share Milhaat ce Yar Terawa [8/17, 1:06 PM] Miilhaat Writer✍🏻: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 73&74 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation.......``` Ba Adnan Kad'ai ba hatta Abdallah sai da yaji zufa na sassafo Masa, Adnan kuwa wani abu ya ji ya bi ta makoshin sa ganin irin kallon tuhuma da take masa, Dakyar ya aro jarumta yace "Umm umm bani da labarin komai" Ajiyar zuciya tayi kana Tace "Ta 'bata ba a San inda take ba" Gyara zama yayi kamar Bai San komai ba yace "Whatttt!!!! Da d'an karfi kana yace "when, how? Yaushe hakan ta faru,taya ma za'a ce ta 'bata sai kace Yar tsana?" Ya maida kallon sa ga Abdallah kana yace "kana Jin wani zance ko,wai ta 'bata kamar babyn roba?" "Wallahi da mamaki Kam" "Umhn to maganar da ake ma ta kai 4 months ba a San inda take ba" Adnan yace "Ashhha abu baiyi Dad'i ba, Allah ya bayyana ta" Duk suka amsa da Amin. Ficewa tayi daga motar Bayan ta bawa Adnan Number wayar ta, Motar ya tada suka Kama hanya, Abdallah ne yace "Abokina I think is high time fa da zaka bar yarinyar Nan haka ta koma gida, ina gudun abinda zai biyo baya gaskiya" "I wish zan iya hakan, I wish zan iya cire ta a Raina I wish lokacin da ta nemi mu na shirya na amince da duk ba a Zo Nan ba" " Bar maganar wish wish d'in Nan ka bar yarinyar Nan haka ta koma gida" "Bazan iya" Yana maganar ya maida hankalin sa kan tukin da yake. "Ka fahimce ni Adnan, wallahi idan asirin ka ya tonu abun bazai Mana kyau ba sabida duk abinda ya shafe ka Nima ya shafe Ni" " Nima ka fahimce ni, wallahi Allah ina son yarinyar Nan har cikin Raina" "Ita Kuma Tace Bata son ka just let her be" "Kana ganin idan na barta ta tafi zata rufa min asiri ne?" Shiru Abdallah yayi na Yan sakanni kana yace "No, I don't think so" "Good that's my point, ina so na jefi tsuntsu biyu da dutse d'ayane you understand what I mean?" " Yeah I do, Allah ya shige Mana gaba"

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});