Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wa" " To Alhaji, auu daddy nagode" Duk sukayi dariya, Maida kallon sa yayi ga Ma'isha yace "Daughter kuje kuci abinci, don zamu fita da Haisam din" Mikewa tayi Tace "Ya Haisam Tashi muje ko?" Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya bi bayanta, Umma tace "Alhaji, hajiya nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, ban San wani irin godiya zan Muku ba" Mummy Tace "haba ke kuwa tun dazu fa kike ta godiyar nan, ya Isa haka, mu Dan Allah mukayi ba don komai ba, sannan mun lura akwai shakuwa a tsakanin yaran Nan Baki ga yanda ta tada Mana hankali ba nikaina mamaki ne ya kamani" "Ikon Allah, Amma ni Haisam bai tab'a min maganar ta ba ko da da wasa ne" "Ai bazaiyi ba don na lura Haisam na da zurfin ciki" Murmushi tayi tace "haka yake kamar ubansa" Alhaji dake Danna wayar sa, jin ta ambaci uban sa, yace "Yauwa please a ina baffan Nan nasa yake?" "Ya Nan cikin garin Nan" " Kina nufin cikin garin Gombe?" "Eh" " Abun zaizo Mana da sauki insha Allah" Mummy da Umma a tare sukace " Allahu yasa" Ya amsa da amin ya daura da fad'in "Maryam ku samu kuje shopping din Nan kar dare yayi, sannan please kar su d'auko komai a chan, za a Saya musu duk abubuwan da suke bukata, sannan idan kudin Bai Isa ba ki Kirani" Ta amsa da "to Alhaji" Mikewa yayi yace "idan yaran Nan sun gama ina ciki" "To alhaji a fito lafiya" 'bangaren su Haisam da Ma'isha kuwa abinci kala kala ne aka jera su,akan dinning duk ta bud'e Masa, Haisam Kan sa ne ya kulle ya rasa ma wani abinci zai ci,daga bisani yace ta sami fried rice din, bayan ta zuba Masa a plate ita ma tayi serving kanta sannan ta tsiyaya musu juice Wanda mummy ta had'a na Banana,kwakwa da Madara, Yana ci yana Santi har Saida ya cika cikin sa tam, yayi hamdallah, Ma'isha Tace "Ya Haisam na Kara makane?" Kallon ta yayi da lulu eyes dinsa yace "So kike ki hallakani?" "Laaa yaushe abinci ya tab'a hallaka mutu?" " Baki da Labari ko?" "Eh gaskiya ban tab'a ji ba" " To yau kinji" " Na daiji Amma ban yarda ba,taya za a yi abinci ya hallaka mutum?" "Yanzu ai a koshe nake idan na Kara sa wani abincin a cikina ko da kuwa spoon 'dayane mutuwa zanyi" Kama baki tayi tace "Mutuwa Ya Haisam nikam ban shirya kuka ba" "Ma'isha ke dai kin samu sabon salo" "wani irin salo Kuma?" "Naga kin dage Sai Yaya kike ce min,ni yayan ki?" "Eh Mana ko baka ji abinda daddy yace bane?" " Naji Mana Wai ke katuwa dake ki wani Rika cemin Yaya" Ajiye spoon din dake hannun ta tayi Tace "Nice katuwar?" "Eh Mana" Nan wasu siraran hawaye suka Fara saukowa daga idanun ta,Kama baki yayi yace "ikon Allah Dan Allah ki rufa min asiri,me yasa ki kuka?" Cikin muryar kuka tace " Ba Kai bane kace min katuwa" "Shiyasa kike min asarar hawayen ki?" Bata ce Masa komai Sai sautin shesshekar kukan da take kawaii yake iya ji, cikin murya Mai sanyi yayi yace "Yi hakuri Yar Kanwata ke baki San wa bane?" "Kanwar ka bayan kace ni katuwa ce?" "Ni na Isa na ce miki katuwa tuntuben harshe ne,bazan sake ba kiyi hakuri" " To naji zan hakura Amma Sai dai in zaka dauke ni a matsayin kanwar ka sannan idan na Kira ka da yayana zaka amsa?" "Na amince Sai Kuma me?" " Shikenan?" "Ah to ai hikenan baki da case kanwata" Rufe fuskar ta tayi wai ita a lallai taji kunya, Murmushi yayi yace "to kije ji fad'awa daddy na gama ko ina zamuje?" "bari naje na tambayo maka shi" "a a ni ban saki ba." Tashi tayi Tace " bari naje na fad'a Masa" Kai kawaii ya d'aga mata,d'akin Daddy ta nufa ta Sanar mishi da cewar Haisam ya gama. Bayan daddy ya shiga ciki Mummy Mikewa tayi ta d'auko makullin motar ta, Tace wa ummu "Tashi muje ko" Ba musu ta Mike a dai dai Nan Ma'isha ta shigo parlor cikin muryar shagwa'ba tace "Mummy tafiya zakuyi ku barni bayan nace Miki zan biku" "afwan daughter na sha'afane" "To Dan Allah mummy ku jira ni bari na canza Kaya" "To ki same mu a mota" Suka fice. A dinning daddy ya tarar da Haisam ya umurce sa da ya ajiye jakar sa, su fita hakan akayi, a tare Suka fito da Ma'isha, motar mummy ta Shiga yayin da Daddy da Haisam suka shiga motar Daddy, Mai gadi ne ya wangale musu gate, su mummy ne suka Fara fita sannan su daddy suka fita. A hanyar su ta tafiya daddy ke tayi masa Hira shi Kuma Sai dai yayi Murmushi idan ya Masa tambaya ne ya amsa da eh ko a'a a haka har suka Isa inda zasuje, kananan Kaya da shaddodi masu tsada daddy ya Saya Masa Sai kallan da Haisam ya zab'a a bashi, takalmomi da huluna Kuma ba a cewa komai. Haisam tsabagen farin ciki bakin sa ya kasa rufuwa don shi a iya sanin sa bai tab'a rike Kaya masu tsada haka ba bare ace nashi ne, bayan sun gama da shagon Kaya suka kaiwa telan Daddy sannan ya umurce sa da Yana son kayan Nan da kwanaki uku, ya amsa da to, ya cika Masa aljihu da kudi suka Kara gaba. Shagon sayar da waya suka nufa, daddy yace "Haisam ka zabi duk wayar da kake so anan" Haisam kallon daddy yayi yace "Daddy ka dai za'ba min ni ba sanin waya nayi ba" Daddy Har cikin ransa yaji dadin kiransa da Haisam yayi Daddy, Murmushi yayi yace "To why not mu d'auka maka iPhone 14?" Zaro Ido yayi yace "iPhone 14? Daddy naji ance wayar nada tsada sosai Kuma ma ban iya amfani da ita ba" " Kar ka damu Ma'isha zata nuna maka yanda ake amfani da ita, itama iPhone d'ince a hannun ta" " To Daddy nag....." Hannu ya 'daga Masa yace " A'a Haisam bana son godiyar Nan, daga yanzu bana so kalmar godiya ta Kuma Shiga tsakanina da kai" "Amma ai daddy masu iya magana sunce yaba kyauta tukuici ce" "Wannan Hakane Amma ni ban bukata" Shiru kawaii yayi don baya son jayayya da daddy. Kallon Mai shagon daddy yayi yace "Sa Mana iPhone 14 a leda sannan ka bani acct number ka na maka transfer" "Ai Alhaji babu wayar ba a ma samun ta anan sai dai idan kana so za a yi Muku order" "Okay to zuwa yaushe zai iso?" " Nan da sati haka" " Sati ai yayi nisa, anyways bamu iPhone 13 in yaso daga baya Sai a saya Masa wanchan d'in." Sa musu yayi leda sannan ya Saya Masa sim, had'e da earpod, Haisam farin ciki bazai misaltu ba, bayan sun gama suka wuce gida, daddy ganin mummy basu dawo ba ya "Na sani ai za a rina,Mata mata" Kallon Haisam yayi yace "Zo muje na nuna maka side Dinki" Bin bayan Daddy yayi wani d'an madaidaicin flat ne ya had'u iya had'uwa, Wanda tsaya kwatanta muku yanda take zai d'auke mu lokaci

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});