Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 62

Chapter 62

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

'bangaren yace "Kina kusane? Haisam ya farka" kashe wayan tayi da saurin gaske ta bar gun. ICU ta nufa daga nesa ya hango ta kasantuwar yasan ita d'in kawar Isha ce yace "Ina take?" Nan ta Fad'a mishi incident d'in da ya faru, yaji tausayin ta matuka, Nan ta nemi alfarma ya bari ta Shiga a madadin Isha, bai Musa Mata ba, suka Shiga, suna Shiga taga Haisam a kwance sai rarraba idanu yake Yana son gane inda yake. Idan sa ya sauke a Kan Meerah, Cikin tsarkewar murya yace "Prin.... Ceessss" (Princess) Kama baki Meerah tayi Nan da nan hawaye suka Fara kwararowa daga idanun ta, "wannan Wace irin shakuwace a tsakanin Ma'isha da Haisam,sabida nasan da sunan Princess yake Kiran Isha,tabbas ita yake son gani,tunda ya farka bai yi magana ba,sai da yaga kawar ta" Dr Ali ne yake ayyana hakan a ransa. Da gudu Meerah ta fita, ta nufi ward d'in da Isha take, tana Shiga d'akin ta fashe da kuka su, mummy da Daddy suna tambayar ta ko Lafiya Amma sai kallon Isha kawai take, Isha ma kallon ta take. ________________________ Please Vote and comment Milhaat ce Yar Terawa 65&66 '''Continuation........''' daddy kallon ta Meerah yake cikin Muryar mai Sanyi yace "Meerah speak up Mana, what happened?" Mummy ce ta karasa inda take, hannunta ta rike hadey da fad'in "Kina Lafiya tsorata mu Meerah, me ya farune kike kuka Haka? Wani mugun abune Kuma ya Faru, sabida a cikin Yan shekarun Nan duk kullum cikin tashin hankali muke da ga wannan sai wanchan" Daddy yace "Kar kiyi sab'o Mana, Ko wani bawa da tasa kaddarar mu Tamu Kenan muyi fatan Allah ya bamu ikon cinye jarrabawar" Meerah hannun tasa ta Shiga share hawayen ta, murmusawa tayi had'e da fad'in "Mummy wannan karon ba mumunar labarine ba, abinda Muka dad'e muna jira ne" Cike da mamaki suke kallon ta, musamman ma Isha da ta kosa taji maganar dake bakin ta,mummy Tace "Please stop beating into the bush,just go straight to the point Mana" "afwan mummy......" Kallon Isha tayi Tace "Haisam ya farka" Isha da Bata San sanda ta Dirko daka gan gadon asibitin ba,bata tsaya tambayar ta komai ba ta yi hanyar fita,Duk suka bita da Kallo,Mummy Tace "Are you sure of what you're saying?" "am sure mummy har sunan Isha ya Kira" daddy yace "Ta fita fa a haka jikinta ba ko mayafi" ai kuwa a sannan ne mummy da Meerah suka bi Bayan ta,a guje Mutanen dake gun sai aikin kallon su suke, suna Kiran sunan ta Amma inaaa kamar cewa suke ta Kara gudu. Tana Isa ICU,zata Shiga aka hanata,ganin yanda take a birkice kamar mahaukaciya,Dr Ali ne ya karaso gun sabida hanyaniyar da yake ji,Yana ganin Isha ya bi Jikin ta da Kallo da ga sama har kasa ,a cikin kwana d'aya har ta lalace tayi baki ta rame, tabbas tana cikin damuwa. Muryar tane ya Dawo dashi duniyar Mutane tana fad'in "Dr ka Fad'a musu su barni na Shiga please" tana maganar tana kuka hawaye ya wanke mata fuska, Dr Ali yace "Ai Haisam baya Nan Isha" "Ban gane baya Nan ba?" "Ina nufin Yana ward,an fitar dashi daga Nan,kizo muje na kaiki inda yake shima Yana tambayar ki" a dai dainan su mummy da Meerah suka Isa inda suke,suna ganin sun juya suka bi Bayan su ba tare da sunce komai ba,Isha tafiya take har tana kokarin fad'iwa. Da sauri Dr Ali ya taro ta cikin sanyin Murya yace "Be careful" Murmushi kawai tayi suka cigaba da tafiya, suna Isa kofar d'akin da Haisam yake yace "Ki Shiga Nan ne d'akin nasa" Kasa motsi tayi tana kallon kofar, Meerah ve ta dafe ta a kafad'ar ta had'e da fad'in "isha kin dad'e kina jiran Wannan ranar, ki Shiga Mana" "Meerah ina tsoron Shiga ne, bana so ya Kuma rufe idanun sa kamar na ranar idan ya sake rufe idanun sa na tabbata bazai sake tashi ba" Dr Ali yace "No Isha Kar kice haka Mana, I told you d'an sarkin Saudi tun yana da shekara 17 a duniya yayi accident ya Shiga comma, tun 2014 Kuma a yanzu Muna 2022 bai farfad'o ba Kuma bai mutu, Kuma Haisam bai koma ba , tun da kiga mun dawo dashi nan, ya farka kenan" Mummy Banda kallon Isha babu abinda take yi,wasu zazzafan hawayene suke gangarowa daga fuskar ta tana mutukar jin tausayin Yar tata,fatan ta shine wannan ya Zama shine wahalar ta na karshe a Duniya. Ajiyar zuciya tayi ta Fara 'daga kafa a hankali, ji tayi kafar ta ya mata nauyi Duk da babu takalmi a kafarta,Jan kafar ta farayi har ta sa hannu ta murd'a kofan ta bud'e, kamar baza ta Shiga ba, sai Kuma ta Shiga da d'an sauri. Haisam naji motsin kofar ya waigo, don ganin Wanda ya shigo, Yana ganin Isha, kallon ta kawai ya tsayayi, itama kallon sa take Hannayen sa ya ware alamun come and give me a hug, cikin kuka da had'e da dariya ta nufi inda yake, ta rungume shi , wani ajiyar zuciya suka sauke a tare, Isha kuka take yayin da yake d'an bubbuga Mata baya alaman rarrashi Yana zubar kwallar Farin ciki, Shigowar su Mummy ne yasa tayi saurin janye Jikin ta. Mummy wurin Haisam ta nufa, shafa kansa tayi cikin so da Kauna irin na uwa da d'anta, Tace "Son kana lafiya?" Ya bud'e baki da niyar magana Amma ya kasa, Isha kallon Dr Ali tayi Tace "Ya baya magana Dr?" "Eh ai dama bazaiyi magana Nan take ba, sabida shekarun da ya d'iba Yana bacci, yanzu Haisam ya zama kamar yaro babu abinda zai iya yiwa Kan sa" Mummy Tace "For how long Dr?" "Uhmn I can't really say gaskiya, Haisam have been sleeping for four years, so Allah ne Kad'ai yasan sanda koman shi zai Zama normal" Haisam kallon su yake Yana mamakiin maganar da Dr Ali yake yi, Wai shi ne yayi bacci har na tsawon shekara 4,shi Duk a tunaniin sa Suma yayi ya farka, a Sannan ne ya tuna da a gun d'auri auren sa ne ya Suma, kokarin tashi ya Shiga yi, da sauri Dr yasa hannu ya kwantar da shi Yana fad'in "Calm down Haisam, Calm down" Kuka ya farayi Yana kokarin tureshi, yace "Haisam me kake so? Akwai abinda kake so a Kawo maka ne?" Murya a hard'e yace "Ayrah" Isha, Mummy da Meerah kallon juna suka Kuma suka mayar da kallon su ga Haisam d'in, Isha fashewa tayi da kuka ta fice daga d'akin, tana fita suka ci karo da Daddy, Abba da Umma. Daddy ne ya rike ta yace "Isha ina Haisam d'in" Cikin kuka Tace "Yana ciki" Umma tace "Ya Mutu ko Isha?" Kallon Umma tayi a razane ta girgiza kai had'e da fad'in "A a bai mutu ba" Abba yace "To kukan me kikeyi?" "Kawai tausayin sa nake ji" tana Kai Nan tayi gaba suka bita ta da Kallo, d'akin suka Shiga, da sallama, haryanzu Yana kokarin ture Dr Ali,Umma na ganin Haisam cikin Muryar kuka tace "Haisam!!!" Haisam naji Muryar Umman sa ya d'ago ya kalli inda yaji Muryar ta, cikin tsarkewar murya yace "Umma" Da sauri ta nufi inda yake, Dr Ali na ganin hakan

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});