Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 55

Chapter 55

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,231 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saura 3 days biki shiri ake both families, sosai suke shiri ba kakkautawa, Isha dai sunan zatayi aure ne amma Sam bata farin ciki da auren babu abinda tayi na gyara jikin, Umma ce ta zage dantse wurin ganin ta gyara yar ta. A yaune dubannin Mutane suka shaida Auren Ma'aruf da Ma'isha, Bayan an d'aure aure walima akayi a gidan su Amarya, karfe 8 na dare aka kaita d'akin mahaifin ta nasiha ya mata sosai mai Shiga jiki da fatan Allah ya basu zaman Lafiya, mummy Kam kasa magana tayi tana kuka Isha na Kuka rungumar ta tayi tana fad'in "Daba don aure ba babu abinda zai rabani da ke 'yata Allah ya miki Albarka ya baku zaman Lafiya" karar motoci suka fara ji alamun an Zo d'aukan Amarya Nan take sautin kukan Isha ya Karu mummy na taya ta Umma ma Saida ta zubar da kwalla, dakyar ta 'ban'bari Isha a jikin Mummy aka sata a mota , Mummy,qawayen Mummy Guda biyu,da Meerah da kawayen Isha guda biyu na wurin Aikin sune suka Rakata har gidan ta. Umma nasiha ta Kuma mata tana mata fad'a akan tabi Mijinta sau da kafa, wani sabon babin kuka ta bud'e ganin Umma zasu tafi su bar ta, Dakyar ta bari suka fita aka barta da ga ita sai kawayen ta. Karfe goma da Yan Mintuna Ango ya shigo tare da abokanan sa bakin su d'auke da sallama suka amsa ba 'bata lokaci sukayi duk wani abinda al'ada ya tanadar kana suka fice, Ma'aruf raka su yayi har gun motar su, Cikin kawayen ta babu wacce ta fito da motar ta hakan yasa Dole sai sun Kai su gida. Sai da yaga fitar su kana ya shige part d'insu, Zama yayi kusa da ita a hankali ya d'aga mayafinta, wani ajiyar zuciya ya sauke had'e da fad'in "Alhamdulillah Allah na gode ma ka da ka mallakamin wannan kyakkyawar baiwa taka" Isha lokaci guda ta tsinci kanta da jin haushin sa, surutan sa yayi tayi bata tanka Masa ba, ganin bata da niyar kulashi sai yayi tunanin ko kunyar sa take ji, hakan yasa umurce ta da taje tayi alwala bata Musa ba ta Mike ta shige ban d'aki ta d'auro alwala bayan ta fita shima ya Shiga Bai dad'e ba ya fito sallaya ya shimfida musu Sannan ya jaa su sallah bayan sun idar da sallan ne ya dad'e yana roka musu zaman Lafiya a gun mahaliccin su sannan ya mata Duk wani tambayar da ya kamata Ango yayi wa Amaryar sa a, dukkannin tambayar da ya mata ta bashi amsar su dai dai yadda ya Dace hakan yasa yaji ta Kara Shiga ransa. Ledan kajin da suka shigo dashi ya janyo ya ajiye a gaban ta mikewa yayi ya nufi kitchen bai dad'e ba ya shigo hannun sa d'auke yake da plate sai Kuma glass cup, da kanshi ya fara bata abincin Duk da taso tayi masa rigima, sai da ta koshi kana ya tsiyaya mats yogurt ya bata tasha kana shima ya sakar wa cikin sa shima. Plate d'in ya mayar kitchen parlor ya nufa ya sa key kana ya dawo d'akin ganin ta yayi har ta kwanta, Canza kayan jikin sa yayi ya Sanya jallabiyar sa shima ya haura Kan gadon, hannunta ya rike kana yace "A haka zaki kwanta?" Tace "Eh" a takaice "Amma kayan Nan basu miki nauyi ba?" "Basu yi ba" " A a dai bari na rage miki su" hannu yasa zai tab'a ta da saurin Gaske ta Dirko daga Kan gadon tana kallon sa, cikin rashin fahimta yace "Isha Lafiya?" Cikin Muryar kamar fad'a Tace "Me kake shirin aikatawa ne?" Murmushi yayi kana yace "Babu komai kwanta abinki babu abinda zan Miki" Gani kawai yayi ta d'auki Pillow da bargo ta nufi hanyar fita da sauri yasha gaban ta had'e da fad'in "ina kuma Zaki?" "Zan bar maka d'akin ne, don ni gaskiya bazan iya had'a jiki da Kai ba" Cikin sanyin Murya yace " Amma meyasa Isha Kar ki manta fa ni mijin ki ne ina da iko Akanki" Fashewa tayi da Kuka Tace "Dan Allah kayi hakuri ban shirya ba" "Kar ki damu ni bazan miki Dole ba, Kuma Dama ba dalilin da yasa na auri ki ba Kennan soyyayar da nake miki yasa na aure ki zan iya jiran ki har zuwa ranar da Kika shirya" sa hannu yayi karb'i pillow da bargon dake hannun ta yace "Je ki kwanta ni zan kwana a parlor" Yana Kai Nan ya fice abinsa. Isha jikinta ne yayi sanyi tabbasa tasan bata kyauta masa ba, tunda Yana da hakki akanta Amma fa alkawari ta d'auka wa kanta babu wani mahalukin da zata bashi kanta in ba Yayan ta ba, da wannan tunanin ta kulle kofar ta koma ta kwanta abinta. Ma'aruf kwance yake Akan kushin ransa Duk ba Dad'i a bayyane yace "Yau fa ranar da na dad'e ina jira Kenan Amma a parlor zan kwana, hmm bazan miki Dole ba Isha sabida nasan halin da kike ciki" tunani kala da iri yayi tayi har dare ya raba ya kasa bacci, ji yayi bazai iya hakura ba, mikewa yayi ya nufi d'akin da Isha take Wanda shine d'akin su Tura kofar yayi yaji ta a rufe Murmushin takaici yayi kana ya juya ya koma ya kwanta a haka bacci 'barawo yayi awun gaba dashi. _________________________ Masu tambayar complete book d'in Nan Babu pls sabon book ne Milhaat ce Yar Terawa https://www.wattpad.com/1248497695?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_pageb=create_on_publish&wp_uname=Milhaat&wp_originator=yyYOiPWOf9d70htdRqg7I1%2F4ucy6HsOlgByapt3Dnb2JGUd5QVGMPXeC%2Bp0YdiBDdt6TP4swRtJhg2tXkbgWfc9O3T2b4yf1jRUCMIvqFOmhE71dThk0eS8%2FT5G%2F00JG 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 59&60 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *WASHE GARI* Alarm d'insa ne ya fara bugawa mikewa yayi ya kashe, d'akin su ya nufa ya Shiga babbuga mata kofa, zumbur ta mike a d'an tsorace, bedside lamp ta kunna kallon d'akin ta shigayi tana mamakin a wani d'aki take, sunan ta da taji ya Kira ne kamar rad'a yasa ta kalli kofan shiru Bata komai ba, a karo na biyu ya Kuma cewa "Isha!!! Cikin Muryar bacci Tace "Na'am" "d'an bud'e kofar asuba tayi" Mikewa tayi jiki ba karfi ta bud'e

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});