Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Yar karamar tsaki tayi Tace "Anya gayen Nan zai Soni kuwa?" Komawa tayi ta zauna ta Fara cin abincin ta, Haisam kuwa zuwa yayi ya tarar da Ma'isha na tsaye a jikin mota tana jiran sa, ta had'a raai, tun daga nesa ya fara dariya don yasan ta dad'e tana jiransa tun Kan Aysha tazo dama ta kirashi yace mata sai yaga cin abinci tazo ta same shi Kuma Taki. Yana karasawa yace "Yar karamar Kanwata har an fito?" Cikin Muryar Shagwab'a Tace "Ba a sani ba" "Haba Mangana me yayi zafi wai fushi kike dani?" "Nikam ka bud'e min na shiga so nake naje gida" Kai kawai ya girgiza da kansa ya bud'e mata motar ta shiga sai turo baki take ita a lallai an 'bata mata raai, Yana shiga ya tada mota suka nufi hanyar gida, sai surutu yake Yana bata Labari bata kulashi sai da Tace Umm ko hmmm har suka Isa gida, suna Isa ta fice ta shige gida ba ta Tsaya jiransa ba kamar yadda suka Saba ba, mummy na ganin ta Tace "Ke Kuma yau ko sallamar ma baza ki iya ba" Cikin sanyin murya tace " Sorry mummy na shafa'ane" wuri ta samu ta zauna tace "Mummy ina wuni" "Lafiya daughter ya school d'in dai?" "Lafiya Lau Mummy, ina Umma?" "Tana part d'inta, yanzu ma tashi a inda kike zaune zatayi wanka zamu je saloon wanke Kai" "Yauwa Mummy Nima zan biku" "Ahhh yau Kuma ba yayan naki bane zai kai ki?" "Eh zan biku" Haisam da sallama ya Shigo mummy ta amsa har kasa ya tsuguna ya gaida ta kana ya nemi wuri ya zauna yace "Ni zan kai ki, aiki nane wannan" Turo baki tayi Tace "Bana so zanbi su mummy" Yace "In ko hakane baza ki ba don bazan bari ki fita a gidan Nan ba" Mikewa tayi Tace "To an fasa wanke Kan" ta shige d'akin ta, Haisam yace " Kin ganta ko" Mummy tayi saurin fad'in "Ah ah ba ruwan nikam kun fi kusa in sa muku baki ku kunyata ni ba dani ba" ta Mike ta shige d'akin ta itama Haisam Yar karamar dariya yayi ya bi bayan Ma'isha ya tarar da ita tana kwance a Kan gado tana kallon saman d'akin. Turo kofar yayi a hankali tasan ba mai shigowa sai shi hakan yasa ta juya Masa baya, Murmushi yayiw ya zauna akan couch d'in dake d'akin ajiyar zuciya yace "Please princess kiyi hakuri duk da ban San laifin me nayi ba, don na tabbata fushin Nan da ni akeyi, Amma duk da hakan kiyi hakuri" Hmmm kawai Tace ba tare da ta juyo ba, tashi yayi ya zauna a Kan couch d'in dake fuskantar ta, Kama baki yayi yace "Laaa ila kuka Princess? Me yayi zafi har Haka Dan Allah ki fad'a min laifi me nayi haka?" A zuciyar ta Tace "Taya za'ayi na fad'a maka cewar ganin ka da nayi da watane ya sani kuka? Taya za'a yi na fad'a maka cewar bana son ganin wata mace ta rab'e ka? Taya za'a yi na fada maka ganin ka da wata da nayi cafeteria ne ya sani kuka?" Cikin wani irin salo ya ambaci sunanta "Ma'isha!!! A hankali ta d'ago kanta ta sauke su akan kyakkyawar fuskar sa kasa jure kallon da yake mata tayi ta Kuma rufe idanun ta. Yace "Ma'isha tell me please ko Nima so kike nayi kukan?" Girgiza Kai tayi had'e da fad'in "A'a" Yace "To tashi ki zauna" Ba musu ta tashi ta zauna yace "Princess ina jinki Dan Allah me ya same ki?" Shiru tayi sai kokarin 'boye hawayen da ke idon ta take Amma ta kasa, daga bisani ta fashe da kuka Mai sauti. Haisam har cikin ransa baya jin dad'in kukan ta, musamman ma ace shine silar kukan nata ajiyar zuciya yayi yace "Dan Allah Dan Annabi na roke ki fad'a min dalilin kukan naki , bana jin dad'in ganin ki a hakan karya min zuciya yake Dan Allah kiyi shiru" Bata ce mishi komai ba ta cigaba da rera kukan ta. Mikewa yayi yace "Shikenan tunda ban kai matsayin da Zaki fad'a min matsalar ki ba na kyale ki, sannan yanzu nasan matsayina a wurin ki" har yasa hannu zai bud'e kofar d'akin yaji saukar Muryar Tace "Yaya kayi hakuri" Murmushi yayi yasan hakan ne kad'ai zai sa ta kula shi, kin juyo wa yayi jin ta nufo shi ya had'a raai kamar bai tab'a dariya ba Tace "Yaya na" Joyowa yayi Yana kallon ta , kanta a kasa tana wasa da yatsunta yace "Uhmn ina jinki?" "Kayi hakuri Dan Allah" "Hakurin me Kuma? Ni baki min laifi ba, kawai dai yanzu nasan matsayina a wurin ki Ni ba komai bane a wurin ki" "Wallahi Yaya ba Haka bane ba , wallahi bayan mummy da daddy bani da Wanda ya fika a wurin Kuma Kai ma ka sani" "In da hakan ne kamar yanda kikace ai da zaki fad'a min matsalar ki, da Allah fa nake ta had'a ki tun a hanya Amma kin ki kulani Kuma a hakan Zaki wani cewa ina da matsayi a wurin ki? In dai da Gaske ki ke ki fad'a min abinda ya same ki" Turo baki tayi Tace "Ba Kai bane" "Bani bane me?" "Ai Kaine ka shanyani nayi ta jiran ka, ga Rana" Murmushi yayi ya jaa hancin ta yace "yanzu dama don wannan ne kike uban kukan nan?" Ka ta d'aga Masa alamun eh, yace "Ai Saida nace miki kizo Kika ki zuwa, abinci fa nake ci princess, Amma kiyi hakuri na Miki laifi" yasa hannun sa biyu ya rike kunnuwan sa, Murmushi kawai tayi yace "Kin hakura? Idan baki hakura ba bazan sake kune na ba" "na hakura" Ajiyar zuciya yayi yace "Kai na gaji" "Laa d'an rike kunnen ka da kayi da bai Kai minti d'aya ba har ka gaji?" " Eh Mana da wahala fa" Dariya tayi harda tafi Shima dariyar ya shiga yi yace "Zo mu je dining nasan princess d'in yayanta tana jin yunwa" Tace "kamar ka sani Yaya" Shima yace "Kamar ka sani Yaya" Yana kwaikwayon Muryar ta. Dariya sukayi a tare suka fita, shigan su parlor yayi dai dai da shigowar mummy parlor baki a bud'e take kallon su suna Hira suna dariya Mummy Tace "Ahaaaf ni da sani za'a Rina ai, mutum ya shiga tsakanin ku kunya zaiji" sosa keya yayi yace "Mummy in gaya miki da kyar da makerkyasa na rarrashe ta" "Uhmnn to maza je ki d'auko mayafin ki mu je saloon d'in" Cikin Muryar Shagwab'a Tace "A a mummy sai kun dawo Yaya zai kaini" Mummy Tace "Kinci gidan ku ja'ira kawai Ni Zaki jawa raai" tsaki tayi ta fice a hanyar ta tafita suka had'u da umma hakan yasa suka juya kawai hannu Ma'isha da Haisam suka d'aga musu suna a dawo lafiya. Mummy Tace "Yaran Nan sun maida mutane kamar kakannin su" Umma Tace "Bakamar Haisam bama sai a hankali" Mummy Tace "Kin samin son a gaba wallahi ke Sam bakya ganin laifin yarinyar Nan ko kad'an" "Hmm Hajiya Kenan ai ni gaskiya nake fad'a ke dai da son d'a ya rufe Miki Ido bakya gani" a haka suna Hira har suka Isa parking

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});