Chapter 43
Chapter 43
tashin hankali anan ai dama tare da na Yayan ki za'a had'a rashin lafiyan naki ne yasa aka d'aga, ma'aruf sunan saurayin naki ko?" 'dan tab'e Baki tayi tace "Eh" "Amma Isha me aibun sa naga yaron na da nitsuwa tunda yasha zuwa gidan na ganshi" Cikin Muryar kuka Tace "To Ni Umma yaushe ni zan Sami abinda na ke so ni Wallahi bashi nake so ba, Ya Haisam nake so kuma shi nake so na Aura" Umma Tunda Isha ke magana Baki a bud'e take kallom ta Muryar Mummy suka ji daga bakin kofa tace "Biri Yayi kama da mutum, Ashe dama Soyayya kuke da Yayan naki?" Wuri ta samu ta zauna Umma tana mata Sannu da zuwa ta amsa a gaggauce kana ta maida hankalin ta ga Isha dake kuka tace "Isha dama kina son Yayan ki? Kika cuci Kanki Kar dai ma shine Wanda a dalilin sa Kika kamu da ciwon zuciya?" Kai ta d'aga alamun eh, Umma Tace "Haba Isha Amma baki kyauta Mana ba, Kuma kin cuci Kanki" Cikin kuka tace " Umma ya kuke so nayi ne? Baku ga yanda Yaya yake sonta bane? Idan ma ya sani babu abinda zai Canza tunda ba Sona yake ba" Umma Tace "Ai mune gaba daku Isha da kin sanar damu da Duk Wannan bai faru ba, Kuma da Yayan naki Bai Shiga comma ba" "uhmn Umma Kenan, zafa ku raba su ne kuma yana sonta yanzun ma ai rashin natan ne yasa ya Shiga comma, Kinga da ko an gudu ba lallai bane a tsira." Mummy Kam shiru tayi tana Jin tausayin Yar tatan chan sai ta ce "Idan bakya son Ma'aruf d'in zan fad'a wa mahaifin ki a kyale ki kawai" Umma tace "A kyale ta Kamar yaya? Kina nufin ta cigaba da zama haka tana jiran babu?" Cikin rashin fahimta mummy Tace "Ban gane babu ba?" "Babu man Haisam da shi da Babu ai duk d'ayane, gaskiya to me a bar yarinyar nan tayi auren ta, wa yasan ranar da zai farka?" Mummy Tace "Haba Dan Allah meyasa kike fad'in hakan, Haisam fa d'anki ne" "Isha ma 'yata ce" kallon Isha tayi Tace "Daughter kiyi auren ki kiyi fatan hakan shine alhairi a gare ki dake da Haisam d'in baki d'aya" Kirkirerren Murmushi tayi Tace " Shikenan Umma nagode Sosai Kuma na amince da auren Ma'aruf d'in" Umma Tace "Masha Allah, Allah ya miki Albarka" Ta amsa da "Ameen." Girgiza kai mummy tayi tace "To dama Nazo ne muyi list na abubuwan da ya kamata mu saya mata in yaso zuwa next week sai muje turkey, muyi sayayyan a Chan" Umma Tace "Ai a gani na ba sai munyi list bako?" " Gara dai ayi kin San Akwai mantuwa" "Eh hakane Kam" Nan suka shiga listing kayan d'aki da kayan kitchen d'in Isha mikewa tayi Tace "Nikam zan Shiga bacci nake ji" ta shige ciki abinta ba tare da taji abinda zasu ce ba. Kwanciyar ta ke da wuya Ma'aruf ya Kira wayar ta da Kamar ba zata d'aga ba har dai da ya kusa yankewa ta d'aga bayan sun gama gaisawa yace "Am sorry Isha na tura gidan ku ba tare da sanin ki, Isha na gaji da ganin ki a haka ina sonki kuma ina tausayin ki sabida halin da Kika tsinci kanki a ciki" Tashi tayi ta zauna Tace "Bangane kana tausayin halin da na tsinci kaina a ciki ba?" "Uhmn Isha Kenan na Riga na San komai, Meerah ta Sanar dani halin da kike ciki and please Karki yi fushi da ita ko ranki ya 'baci a Kan hakan nine na takura ta Akan ta fad'a min Nan ma da kyar ta Sanar dani irin Soyayyar da kikeyiwa Yayan ki since from day one na fahimci hakan daga gare ki na d'auka Soyayya ce ta jini, Amma Dan Allah ina so ki bani dama na Shiga rayuwar ki ko da kuwa bazan iya maye miki gurbin sa ba zan kwatanta baki kulawa iya bakin karfina" "Lallai Meerah wato shine ta je ta gaya maka ko zamu gamu" "Yi hakuri ban sanki da fad'a ba" "a a yanzun ma ba fad'a zanyi ba" "Yauwa nasan nayi dace ai" Murmushi kawai tayi yace "Isha Aurena da ke is in two weeks da fatan kina farin ciki da hakan?" "Hmm eh" "Dan Allah dagaske kike?" "Eh dagaske nake" "Kai Alhamdulillah ya kamata mu Fara Shiri ko?" Murmushi tayi kana tace "Eh" "Masha Allah, yanzu kina ina?" "Ina gidan Umma" "Okay ina zuwa yanzu Amma da Kanwata zamu Zo" "To Shikenan sai kunzo d'in" Bayan sallar la'asar yayi horn a mamakeken gate d'in gidan Abba, mai gadi bai tsaya 'bata Lokaci ba ya wangel musu gate d'in sabida zuwa yanzu yasan Ma'aruf da Kuma gun Wanda yake zuwa, Kamar kulluma kud'i ya zaro a aljihun sa ya Mika Masa kud'i ne sun kai kimanin naira dubu biyar murna ya Shiga yi yana kwararo Masa addu'a. Kiran ta yayi akan sun iso, Yar aikin gidan ta aika ta Shiga dasu parlor bakin, kana ta kai musu abin sha da snacks bayan yan Mintuna ta Shigo bakin ta d'auke yake da sallama, Ma'aruf da Kanwar sa a tare suka suka amsa sallamar. 'dago kanta tayi don ganin wacce take sallama, ai ko tana ganin fuskar Isha ta Mike zumbur, Isha ma tayi mamakin ganin ta, Ma'aruf mikewa yayi yace "Ya dai Kun san juna ne dama?" Kirkirerren Murmushi Isha tayi Tace "Eh kamar nasan fuskar Nan a wani wuri" shiru tayi tana kallon ta don tuna inda tab'a ganin ta, Yayin da ita Kuma jikinta sai rawa yake duk ta rasa sukunin ta, gani take kamar Isha tasan Duk Shirin su. Muryar Isha ta tsinkayo tana fad'in "Yauwa kawar Aysha ko? Ko ince Ayrah?" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Isha Tace "Zauna Mana" zama tayi kanta a kasa Isha Tace "Rankashidad'e Kai ma ka zauna Mana" Zama yayi yana kallon yadda yanayin kanwar tasa ya canza, Isha tace "Ya kike ya kwana da yawa da fatan dai an sami abinda ake so" Jin hakan tayi saurin d'ago Kai tana kallonta Isha ta d'aura da fad'in "Ina nufin an fita da result Mai kyau?" Ta maida kallon ta ga Ma'aruf Tace "kasan lokacin su suke bin mu a school" Ajiyar zuciya yayi yace "Ai ni Duk kun tsoratani ne" " Me abun tsoro anan don kawai Mun San juna" "To baki ga yadda Mardiya bta sauya ba?" "Oh dama sunan ta Kennan ai ban sani ba, ikon Allah Kenan back then ina ga sau d'aya ko biyune muka had'u dake ashe zaki Zama sister in-law na" Mardiya da tun d'azu ta kasa cewa komai kirkirerren Murmushi tayi kana ta amsa da "Allah Kenan" Wayar Isha ce ta fara ruri picking tayi Tace "Haba Dan Allah, to ki Shigo parlorn baki man muna ciki" ta ajiye wayan Ma'aruf yace "Wane ne?" Ta amsa da "Meerah ce" Ya amsa da "Oh okay" Bata d'au lokaci Mai tsawo ba ta Shigo bakin ta d'auke yake da sallama, Zama zatayi ta kalli fuskar Mardiya Tace "What me ya kawo Wannan munafukar gidan Nan?" Duk su ukun suka Mike suna kallon juna Meerah Tace "Isha me ya kawo Yar iskan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76