Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 66

Chapter 66

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yayi Wanda yake Kara bayyana kyawun fuskar sa, rike shi Mamy tayi tana kallon sa daga kafan sa har tsakiyan kansa, idanun ta cike yake da hawaye, tana matukar son Haisam, tana Kuma Jin tausayinsa, hannu yasa ya share Mata hawayen da suka fara gangarowa daga idanun ta, Yana girgiza Kai alamun ya Isa. Murya na sassarkewa Mami Tace "Haisam Ashe ka farka? Kai Allah mun gode maka" Malam Hassan kallon Haisam d'in yake Yana daga kwance a Kan sick bed d'insa, a hankali a Haisam ya zare hannun Mami a Jikin Sa ta fara takawa a hankali, har ya nufi gun malam hassan, wani irin Kallo malam Hassan keyi wa Haisam Mai cike da ma'anoni, Haisam d'in ma kallon sa yake, mamy ce ta matsa kusa dasu ganin Shirun yayi yawa, Tace "Haisam!!! "d'ago wa yayi ya kalleta ba tare da yace komai ba. Tace "Yanzu Babu abinda kake ji ko?" Murmushi yayi kana yace "Eh Mami" ya maida kallon sa ga malam hassan da ya juya masa keya kana yace "Ya Jikin Daddy?" "Da sauki za'a ce kullum Babu improvement" "Allah ya bashi Lafiya" Mummy da Nabila suka amsa da Amin. Jin Muryar Nabila ne yasa ya kalli inda take a tsaye bai ma lura da ita a gun ba, Yana kallon ta ya Gane Yar Mamy ce sabida duk yaran Kama da ita suke, hatta yaranta mazan ma Babu Wanda yayi Kama da malam Hassan, duk da shid'in bafulatani ne na usul Amma bakine, Nabila ce ma ta d'an d'auki kalar fatar sa, hakanne yasa duk ta fi su kyau, Kun San ance black is beauty. Kallon ta yayi kana yace "Farida ko?" Murmushi tayi kana Tace "A'a Nabila" "oh sorry My Bad,Nabila amma Mami yarinyar Nan ta girma fa sosaiii" Yar karamar dariya Mami tayi duk da haryanzu hawayene fal a idanun ta, Tace "Eh ta girma nan ma baka ga Auta ba" Nabila turo baki tayi kamar zatayi Kuku, ita ta tsani daji ance mata wai ta girma, ganin yanda take ta kunkuni ba karamin bashi dariya yayi Amma ya gimtse dariyar tasa. Babu Wanda ya Kuma cewa komai kusan na mintuna uku, mami Tace "Baka tambayi kanwar ka Ayrah ba" Kai ya sane a kasa, kamar wani Mai nazari yayi ajiyar zuciya kana ya d'ago Kai ya kalli mami yace "Eh Mamy ban tambaya bane ba sabida ina da labarin abinda ya same ta" " kaga Allah ko Haisam? Baka da hakkin su shiyasa Allah ya Kama su, ban San me ka terawa malam ba, babu yanda banyi dashi ba Akan ya d'auke ka kamar d'an cikin sa, Amma ina son zuciya da son Kai irin nasa ya rufe Masa Ido, bai tsaya a iya Nan ba ya had'a har da Yar sa wacce bata da ji ba bata gani ba yayi amfani da ita wurin biyan bukatar sa....... " Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasa maganar, Nabila ce ta sa hannu tana d'an bubbuga mata baya alamun rarrashi, mamy hannu tasa ta share hawayen ta,kana ta had'e Hannayen ta wuri gudu alamun roko kana Tace "Haisam Dan Allah na roke ka ka yafe Mana a Karo na sau ba adadi, kila in ka yafe mana Rayuwar mu zata Koma dai dai" ta cigaba da kukan ta. Haisam da d'an saurin sa ya nufo ta Yasa hannu Yana share mata hawaye, yace "Mami Wallahi ban tab'a rike Daddy a Raina ba ko da na minti d'ayane, Kuma maganar yafiya tun a ranar na yafe Masa wannan kadara tace Ni Musulmi ne na yarda da kaddara Mai kyau da Mara kyau,a ranar da Daddy yasa wa Abba guba na ganshi,Amma yace idan na kuskura na fad'awa,kowa sai ya kashe Ni ya kashe Umma,sannan a ranar da muka Koma gidan su Isha,na fito naje gidan mu don na d'auko Abu,babu Wanda ya sani daga ni sai maigadi,da idona naga daddy yana fad'a musu su sa petir ta ko ina,hmm su mutu kowa ya huta,a ranar na gane Isha is an Angel to me sends from the almighty Allah........." Ya d'aga Kai ya kalli Isha,da take ta matsar kwalla tana jin tausayin Yayan ta, ya maida kallon sa ga Mamy yace " let the bygones be gone Mamy, Allah baya barin wani don wani but am Very sure that ya barni a Raye ne to make things right and I'll surely do that insha Allah yanzu abinda ya Kamata muyi shine mu maida hankali gun Nemo Ayrah" Fashewa Mamy tayi ta kuka Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Haisam kaga rayuwa, kaga rayuwa sabida dangin Uban ka, tun kana yaro kaga jarrabawa kalala" Murmushi yayi yace "Kuma Yanzu ya zama tarihi ba, please Mamy ki daina kuka haka, nasan kin Soni tamkar d'an da Kika Haifa a cikin ki, har Yanzu ban manta lokacin da idan Kika sayo abu sai ki ja ni d'aki a 'boye ki bani sabida Kar Ayrah ta gani duk ina tune dasu Mamy" Hannun ta ya rike ya zaunar da ita akan Plastic chair dake d'akin,ya durkusa a gaban ta Sannan ya Mika hannun ya d'auki bottle water ya bud'e kana ya Mika mata, ba musu ta Karb'a tasha, goran ta sauke kana sauke wani ajiyar zuciya, tana kallon Haisam da shima yake aikin kallon ta, shafo fuskar sa tayi had'e da fad'in "Allah ya maka Albarka" Ya amsa da "Amin Mamy" Kiran wayan Isha akayi, ta d'aga ji nayi Tace "Mun d'an zagayane Umma Amma ga munan muna dawowa" ta sauke wayan da ga kunnen ta tana kallon Haisam, mikewa yayi daga sugunawan da yayi yace "Mamy bari muje Umma ba neman mu" ya kalli Isha yace "Muje" Ta juya ta fice, Mamy Tace "Tsaya muje tare naga d'akin da kake" Murmushi kawai yayi ya rike hannun ta suka fice. Malam hassan najin sun fita ya d'ago Kai, yayi ajiyar zuciya, Nabila da sauri ta nufi inda yake tana fad'in "Daddy Lafiya? Kana son wani abune?" Girgiza Mata Kai yayi alamun a'a hawayena na zubowa daga idanun sa , da sauri ta d'auki tissue tana share Masa. Umma da Mummy sai mardiya ne zaune a d'akin Ma'isha ta Shiga, sannan Haisam da Mamy a biye da ita, Umma na ganin mamy ta Mike a d'an razane tana kallon yanda Haisam ya rike mata hannu, Rai a mugun 'bace Tace "Haisam Ashe baka da hankali me ya Kai ka gun mugayen Nan?" Saurin sakin Mamy yayi ya Shiga d'akin Yana fad'in "Haba Umma" juya Masa baya tayi Tace "Haisam kace matar Nan ta fice min daga gani bana son ganin ta na tsane ta da ita da duk wani abunda ya shafe ta" " Harda ni?" Cike da mamaki ta juyo tana kallon Haisam d'in kallon baka da hankali take Masa, ya Kuma maimaita tambayar sa a karo na biyu "hardani Umma?" "What are you saying Haisam? Are you in your normal sense?" Umma ke Masa wannan tambayar. "Of course Umma am okay, Umma have you forgotten who this woman is?" Yana nuna Mamy da d'an yatsa, "Itace fa matar da mijin ta ya kashe min miji, ya so ya kashe mu, sannan ya sa Shiga comma for almost five years" "Alhamdulillah Mijinta Kika ce ba ita ba, and wannan matar Itace

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});