Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wayan yayi ya Mike,ba tare da ya bashi amsar Tambayar da ya Masa ba,har ya Kai bakin kofa Daddy yace "Ka dawo musu da dukiyan su ko Kuma mu had'u a kotu,kuma idan kace zaka bar gari wallahi tallahi duk inda ka shiga a fad'in Duniyar Nan zan Nemo ka" Waigowa yayi, yayi tsaki yace "To hell with you mu had'u a kotun" Sai ya fice, motar sa ya shiga duk hankalin sa a tashe Sai zufa yake ta goge wa da hannun sa, farar shaddan da ke jikinsa duk ya jike, Kai tsaye gidan sa ya nufa, yana parking d'akinsa ya shiga matar sa na ganin sa ta gane ba lafiya don ko sallama baiyi ba ya shige. Cikin sauri tabi bayan sa tarar dashi tayi a d'aki yana kaiwa Yana kawo wa, cikin nuna kulawa da damuwa Tace "Malam lafiya me ya Faru na ganka haka sai safa da marwa kake?" Murya na rawa yace "Rabi akwai matsala, akwai matsala wallahi" "Malam zauna ka fad'a min me ke faruwa?" "Zama? Ai banga ta Zama ba, ina naga ta Zama bayan asirina yana kokarin tonuwa?" "Asirin ka? Ban fahimta ba Malam me kake nufi da hakan?" "Ashe dama Munafukar matar Nan tana raye? Ashe bata mutu ba ita da d'anta?" Cikin rashin fahimta take kallon sa, yace "Dad'i na dake kanki baya ja wallahi ko kad'an Zainabu nake nufi Zainabu na Raye ita da d'anta" Dafe kirjin ta tayi Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, suna raye Malam? Amma ya akayi ka sani, na d'auka kasa an Kona inda suke?" "eh ni da ido na, na gani to Amma abinda ya d'aure min Kai hakan na nufin fa basu cikin d'akin don Babu yanda za a yi su tsira gas fa nasa aka sa hatta Wanda yasa wutan ya mutu da idona na gani fa" "ka gani ko Malam tun wanchan lokacin na Hanaka Amma kaki ji, yanzu gashi wa gari ya waya" "Rabi yanzu fa ba lokacin wannan bane..... " Nan ya sanar Mata yanda sukayi da Daddy, Rabi Tace "Malam ka maida musu dukiyar su, ai yanzu ka samu fiye da abinda ka samu agun su, idan ka bari ya kaika kotu duk abunda ka Tara za a Basu" "inaaa bazaiyu ba kin San tsawon shekaru nawa na yi ina tara kud'aden Nan kuwa?" " Ni kuwa na sani malam, ko dai barin garin zamuyi ne Kam?" "ai cewa yayi ko na bar gari Sai ya Nemo Ni" "Nikam wane ne haka? Da yake kokarin tozartamu?" "chairman ne fa Mus'ab Aminu" Zaro Ido tayi Tace "Eh lallai malam baka nemi zaman lafiya ba wallahi in dai baza ka maida musu ba, kasan mutumin Nan yanda yake da taimakon al'uma baya bari a cutar da kowa" "Na San da hakan, dole zan nemi mafita amm....." Kwankwasa kofar da akayi ne ya katse maganar da yake niyar yi. Cikin tsawa yace "Waye anan nace Waye ne?" Cikin sanyin murya Tace "Daddy wani mutumine ya kawo sako yace a baka" Rabi Tace "Shigo" Tana Mika Mata ta fita, Yana bud'ewa yaga tsammaci daga kotu kallon paper da yake ne yasa ta karb'a don ta gani girgiza Kai tayi Tace "lallai malam mutumin Nan dagaske yake, ranae Monday fa zaku shiga kotun" Tashi yayi ya fice ba tare da yace Mata uffan ba, ya shiga motar sa kenan ya hango Yan sanda guda biyu, jiki na rawa ya fito Yana kallon su, bayan sun gaisa 'daya daga cikinsu yace "Kaine Malam Hassan Umar?" Murya na rawa yace "Eh eh nine" ID card d'insu suka zaro suka nuna masa, "Yan sanda ne an turo mu da warrant arrest d'inka" "Ni Ni kuma, me me Kuma nayi?" "Idan mukaje office zakaji koma mene ne" Nan take suka zaro handcuffs suna kokarin Sanya Masa a hannun sa, cikin tashin hankali yake Kiran sunan ta "Rabi !! Rabi!!! Da gudu ta fito ita da 'ya'yan ta guda uku, Yaran na kuka rabi ma na kuka, har suka fice dashi suka sashi a mota. Suna zuwa police station suka tarar da Daddy, mummy, Umma, Ma'isha da Haisam duk suna zaune, cike da mamaki yake kallon su, hannu Daddy ya d'aga musu hannu, gani nayi sun cire Masa handcuffs din. Mikewa daddy yayi yace "Malam Hassan tun wuri ka taimaki kanka ka maida musu dukiyan su yanzu zan sa a sake ka idan Kuma kaki wallahi wallahi sai ka Raina kanka" Kallon Umma yayi yace "Zainabu kina jin abinda yake fad'a ko? Ki fad'a Masa gaskiya cewar dukiyar Nan Yaya nane ya bani" Umma fashewa tayi da kuka ta fice daga gun, mummy, Ma'isha da Haisam suka bi bayanta. Daddy ciza le'be yayi yace "Na lura kana da taurin kai, Amma kar ka damu...." Maida kallon sa yayi ga police d'in dake gefen sa yace "A kulle shi Kuma ban yarda a yi bailing sa ba, sannan kar a bari kowa yazo ganin sa ko da kuwa matarsa ce" Yana Kai Nan ya fice. Tarar dasu yayi a jikin mota Umma na kuka mummy na rarrashin sa, a yayin da Haisam ji yake kamar yaje ya shake baffan sa ya mutu ko zaiji sanyin abinda ke damin sa. Daddy yace "Ki daina kuka insha Allah komai zai wuce" "Alhaji dole nayi kaji abinda yake cewa fa, shi ya kashe min miji ya kwace dukiyar sa,sannan nima ya so kashe ni da d'ana Amma yana rayuwar sa hankali kwance" Mummy Tace "Kar ki damu ranar Monday komai zaizo karshe insha Allah, ke dai kawai ki fad'i duk abinda kika sani shine kad'ai zai sa a mishi hukunci dai dai da abinda ya aikata" Haisam yace "Amma mummy bamu da wani hujja, kinsan komai sai da evidence karshe ma a nemi a karyata mu" Daddy yace "matsala d'aya zamu samu shine evidence d'in da shi ya kashe shi Amma duk sauran zaizo Mana da sauki insha Allah, ku shiga mota mu tafi" mikawa Haisam key d'in motar akan ya jaa su, karb'a yayi duk suka shige, Kai tsaye gida suka nufo. Zaune suke a parlor,duk jikin su a sanyaye yake ganin kukan da Umma take yake ci yaki cinyewa Mummy Tace "Kukan na mene ne haka ya Isa Dan Allah" Cikin shesshekar kuka Tace "Wallahi ina ganin sa hankali yayi mugun tashi, tsayuwar da yayi a gabana sai naga kamar Ahmad ne Kai hatta muryar sa ma irin ta Ahmad ce, Hassan ya cuce ni bazan tab'a yafe Masa ba" ta karasa maganar tana kuka, Haisam Tashi yayi ya fice, Kai Tsaye d'akinsa ya nufa da gudu Ma'isha ta bi bayan sa. Daddy girgiza Kai yayi yace "Allah ya kyauta" ya nad'e garen sa ya shige d'akinsa. Ma'isha har cikin d'akin ta bishi, ya zauna a baki gado ya had'a Kai da gwiwa kuka yake sosai Mai sauti, Zama tayi a gefen sa baiji shigowar ta ba sai muryarta da yaji Tace "Ya Haisam." 'daga kansa yayi a hankali ya sauke idanunsa akan ta, kirkirerren Murmushi yayi, wata farar kyalle ta Mika Masa Murmushi ya Kuma yi yasa hannu ya karb'a ya share hawayen sa, bayan ya gama ya Mika Mata yace "Thank you" Murmushi kawai tayi tace "Ya Haisam kuka fa ba naka bane, addu'a ya kamata muyi Allah

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});