Chapter 15
Chapter 15
zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 19 and 20 Haisam na shiga parlor cikin girmawa ya gaidasu mummy suka amsa, Umma kallon tuhuma take Masa Tace "Haisam me kayi wa 'yata?" Cikin rashin fahimta yace "Umma ce Miki tayi na mata wani abun" "Gidan ku Haisam ina tambayar ka kana maida min amsa da tambaya?" "Wallahi Umma Ni ba abin da na Mata, sai dai Kuma in sharri ta fara yi" " Wani irin sharri yarinya ta fita tana walwala da farin ciki ta dawo cikin 'bacin Rai ka dai..... " Mummy ce ta dakatar da ita tace "Ki daina shiga maganar yaran Nan wataran Zaki ji kunyane Tohm" "To ai abun ne da mamaki daga fitan su ta dawo Haka?" "Da dai kinyi shiru da kin taimaka wa Kan ki sabida kunya zakiji, Ni da ranar na shiga maganar su ba kunya tani sukayi ba, ina Nan ina goyon bayan Son Ashe ya lallab'a sun shirya, kawai nazo wucewa naji Muryar su suna Hira suna dariya tun daga Nan na fita harkan marasa kunya" Haisam yace "Ma'isha dai akwai abinda ke damin ta nayi nayi da ita ta Sanar dani taki daga bisani ma kuka tayi tamin dakyar na rarrashe ta" Mummy tab'e baki tayi Tace " Kwaji dashi" Umma Kuma Tace "Nikam ai baza taki Sanar dani ba" mikewa tayi ta shige d'akin Ma'isha ta tarar tana kuka ta kwanta ruf da ciki, Bata ma San da shigowar Umman ba. Dafe ta tayi had'e da Kiran sunan ta cikin murya Mai sanyi "Daughter!!! A firgice ta tashie ta zauna tasa hannu tana share hawayen dake fuskar ta, kirkirerren Murmushi tayi Tace "Umma kece ban ji shigowar ki ba" Ganin irin kallon da Umma take mata yasa ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsunta Umma tace "Ma'isha me ke damun ki? Yayan ki ya Sanar dani kina cikin damuwa Kuma kin ki fad'a Masa sannan yace min kina kuka na d'auka shirmen sane Ashe da Gaske ne tunda na gane wa Ido na, me ke damun ki? Ki saki jikin ki Nima tamkar mahaifiyar kice" Murya na rawa tace * "Ba ... Babu komai fa Umma" "Baza dai ki fad'a min ba, ko kina ganin ban Kai ki fad'a min bane?" "A'a Umma har kin wuce ma, kawai ban San ta ina zan fara Sanar dake damuwata bane" "ki fad'a min ta ko ina zan fahimta Kuma Insha Allahu zamu samu mafita" "idan na fad'a mata dalilin kuka na tabbas nasan zata Sanar da Haisam sannan idan na 'boye Mata Kuma baza taji dadi ba Dole ma nasan yadda zanyi, na gwammaci nayi ta dakon soyayyar a zuciya ta har izuwa ranar da zai bud'i bakin sa yace Yana so na" Dafe kafad'ar Ma'isha Umma tayi hakan yasa ta dawo daga tunanin da take Umma Tace "Ki Sanar dani matsalar ki" "Umma...... Ina.... Ina son... " "Kina son me?" "Inaso na Sanar dake Amma this is not the right time idan lokaci yayi Zaki ji Insha Allah, Amma for now ina bukatar addu'ar ki please" "hmmm Shikenan Daughter Allah ya yaye Miki damuwar ki" "Ameen Umma" "To tashi muje parlor muyi Kallo" "Ya Haisam na parlor ne Umma?" Mikewa tayi Tace "Dama zan karb'i sako a wurin sa" "Ai na d'auka fushi kike da yayan naki" "Umma ai ni da Ya Haisam sai Allah" "Allah ya muku Albarka" Ta amsa da ameen. Suka fice, suna isa parlor ba taga Haisam ba Tace "Mummy Yaya na fa?" Wani irin Kallo ta mata Tace "Sandan kiwon sa ya 'bata" Turo baki tayi zatayi magana Umma Tace "Jeki d'akin sa maybe yana chan" Tace "To umma" da saurin ta ta fice. Mummy ta bita da Kallo kana ta maida kallonta ga Mummy Tace "Kinga abinda nake fad'a Miki ko?" Umma Murmushi tayi Tace "Na gani." Babu Wanda ya sake cewa komai suka cigaba sa kallon su. Tun daga Baki kofar d'akin sa take ji yana waya yana dariya d'an tsayawa tayi Tace "Waye Yaya samu haka?" Jin ya ambaci sunan Aysha yasa taji kamar an soketa da kibiya a kirji, shiru tayi har ta juya xata koma sai Kuma ta dawo ta bud'e kofar had'e da sallama, Yana ganin ta yace "Am Sorry zan Kira ki anjima" ya katse wayar, Ma'isha Murmushi tayi har cikin ranta taji dad'i ko ba komai tana da muhimmanci a gun sa, sai wata zuciya Tace Mata "idan Kuma 'boye Miki wani Abu yake fa?" Yace "Princess ya dai kin tsaya kina kallona ki zauna Mana" "Yaya meyasa ka katse wayar da kake yi?" "Sabida princess d'ina ta Shigo lokacinta ne ba na kowa ba" Taji dad'i sosai hakan yasa ta zauna Nan fa suka fara Shan hirar su sosai suna cikin farin ciki. Aysha kallon wayan ta ke Tace "Ya Rabbi gayen Nan zai bani wahala, a hakan zan samu soyayyar sa? Amma ba komai insha Allah sai nasan hanyar da nabi na sa ka Fara Sona ko ta wani hanya ne" *MONDAY* 7:45am Kiranta yayi a waya murya cikin fad'a fad'a yace "Wai me kike haryanzu ne? So kike na makara?" "Am sorry gani n...... " Kitt ya katse wayar cikin sairi ta fito ta bud'e motar ta shiga tana Zama bata ma rufe kofar ba ya ya tada motar tana rufewa ya jaaa motar suka nufi hanyar school kana kallon fuskar sa zaka gane ransa a 'bace yake cikin sanyi murya Tace "Yaya Dan Allah kayi hakuri wallahi na tashi da ciwon Kaine" "Dama kin tab'a rasa abin fad'a ne? Inaga ma Dole na bar driver ya Rika kaiki aini ba driver d'inki bane ba" "Yaya har abun ya kai ga Haka?" "Wuce Nan ma" "Ai Yaya naga lectures d'in naka karfe 8 ne Kuma haryanzu da sauran time" "Malama test nake dashi Kuma malamin Nan ba imani bane dashi, 8 na cika yake rufe kofa ba Mai Shiga ba Mai fita, sabida Kinga baki da lectures sai 9 yasa Kika 'bata min Lokaci" "Wallahi ba haka bane Yaya" "Hakane Mana, wallahi ki ka Kuma maimata irin haka tafiya zanyi na bar ki" "Insha Allah bazan sake ba kayi hakuri" "Da kuwa kin taimaka wa Kanki, don Kanki kika taimaka bani" "Kayi hakuri" "Naji" kawai yace Mata har suka Isa cikin makaranta babu Wanda ya ce uffan a cikin Saida yayi parking Tace "Yaya ka saki ranka Mana in ba haka ba test d'in bazai maka dad'i ba" "Kin San da hakan ai Kika bata min raai? Fita yayi a motar ganin zai iya kulleta a ciki itama tayi saurin fita jakarsa kawai ya d'auka a back sit yayi tafiyar sa ba tare da yace Mata komai ba. Ma'isha mamaki ne ma ya kamata bata tab'a ganin sa haka ba, "ko da yake ni na 'bata Masa raai zuwa anjima nasan zai huce
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76