Chapter 75
Chapter 75
sauri ya Shiga toilet d'an karamin roba ya Samu ya tari ruwan zafi ya sirka ya dawo d'akin. 'daukan jaririn yayi ya Shiga Toilet din ya wanke jaririn tass yanda dai akewa sabbin jarirai, Kaya mai kyau ya d'auka ya sakawa jaririn, ya kwantar da jaririn kana ya koma Kan Isha dake kwance idon ta lumshe duk kunya ta ishe ta Murmushi yayi ya girgiza Kai kana ya d'aga ta chak sai ban d'aki, tsayar da ita yayi kana yace "kiyi wanka bari na Kira su Mummy" Kai kawai ta d'aga Masa ya fice ya barta a ciki. Yana Fad'awa Umma Isha ta haihuwa sukayi ta fad'a wai Meyasa Bai Kira suba, Murmushi yayi yace "Umma Kennan kin manta da Dr Haisam kike magana ko?" Sai tayi shiru, fizge wayar mummy tayi daga hannun Umma tace "Sannu da kokari son gamunan zuwa" Ta kashe wayar, Kan Isha ta fita ya tattare gun tsaf, ya sa jik ya goge back yard ya nufa da blankets din da suka baci sai ga Yar aikin ta dawo, tana ajiye ledan a kitchen tazo ta karb'i wanki ta hau wankewa, ya koma d'aki yayi wanka ya sanya kaya marasa nauyi ya koma d'akin Isha ya tarar ta fito wanka har ta Sanya kayan tana tsaye tana kallon jaririn, Murmushi yayi yace "Ya dai maman baby?" Kallon jaririn yayi a kwance a inda ya bar sa, cike da mamaki yace ya Naga Baki d'auki Baby ba?" "Uhmn Wai me na Haifa ne mace ce ko na Miji?" A sume aka Kai Ayrah asibiti, yayin da Abdallah Kuma da aka wuce dasu police station,mardiya batayi kasa a gwiwa ba ta Kira Mahaifiyar Ayrah, Nabila ta kwala wa Kira Akan ta Shigo ta kula da Malam Hassan an ma yi sa'a a asibitin da Malam Hassan yake aka kwantar da ita, Malam Hassan yace suje su kawai zai kula da kansa. Shigowar mami yayi dai dai da fitowar likitan dake Kan Ayrah, inda suke ya nufa yace "babu wani damuwa kawai dai fargabane and congratulations tana d'auke da ciki na tsawon wata uku" Yana Kai Nan ya tafi ya bar su agun Baki a bud'e. ____________________________ Please comment and share Milhaat ce Yar Terwa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 81&82 *End page* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ Continuation............... Mardiya ce tsaye tana kallon d'an jaririn Isha Kuma d'a agun Yayan ta , jiki na 'bari ta d'auki d'an tana kallonsa kamar yayanta ne yayi kaki ya zubar, Kuka tayi sosai sabida mutuwar yayanta da iyayen ta sun dawo Mata sabo fil, har kasa ta durkusasa ta roki yafiyar Isha dama Mutanen gidan gaba ki d'aya, duk wani munafurcin da tayi ta kullawa ta fad'a musu hatta 'bata auren Farukh da Ameerah da tayi Niyan yi, kowa sai da yayi mamakin abubuwan da ta aikata Amma ance d'an Adam ajizine, Isha ta yafe Mata, anan take shaida musu anga Aurahi suyi murna matuka musamman ma Haisam da haryanzu Yana sonta Amma a matsayin soyayyar ya da kanwarsa. Har gida taje ta nemi yafiyar Meerah da Farukh, Kuma sun yafe Mata,duk da Farukh da kyar ya hakura sabida ya d'au alwashin sai ya d'auki fansar abinda ta yiwa meeran sa. "Ayrah me hakan yake nufi? Congratulations? Ciki kike dashi?" Duk a jere mami ta jero mata tambayoyin nan. Kallon ta kawai Ayrah take yi sai ta kawar da kanta tana fuskantar bangon d'akin. "To Wallahi Dole ne a zubar da cikin Nan, wannan abun kunyan ba dani ba Baki Isa ki haifa min shege a cikin zuri'a ta ba" "Mami!!" Ayrah ta kira sunan ta kamar ba ita tayi maganar ba, Zama tayi ta jigina jikin ta ta pillow kana Tace "Mami bazan zubar da cikin Nan ba sabida ba d'an shege bane" Baki a bud'e take kallon ta Tace "Ashe baki da hankali Ayrah ban sani ba? Ko dai kin samu tabin hankali ne?" "Ni Lafiya ta kalau au..... " Bata karisa maganar ba taga shigowar Mardiya wani irin Kallo ta mata sai Kuma ta kawar da kanta. Mardiya karasowa tayi ta dafe ta a kafad'a had'e da fad'in "sannu Qawata" ture hannun ta Ayrah tayi cikin tsawa Tace "Kar ki tab'a Ni" a d'an zabure ta jaa da baya tana mamakin abinda ke damun ta, mardiya Tace "Ayrah lafiyan ki kuwa, me ke damin ki?" "ina mijina?" Shine tambayar da ta wurga mata kallon Kallo Mami, Mardiya da Nabila suka Shiga yi kana suka maida kallon su gareta, Mardiya ta ce "Mami bari naje na Kira likita don na lura bata cikin hayyacin ta maybe ya tab'a mata kwakwalwar ta" "Ke malama da hankalina Kuma a cikin hayyacina nake nace miki ina Kika Sa aka Kai min shi" "Auuu Wai Adnan kike nufi? Yaushe Adnan ya Zama mijin ki Kuma, Ayrah na lura baki da hankali" "Kar ki Kuma cemin bani da hankali Adnan mijina ne Kuma ina son sa" mikewa tayi Tace "ina yake?" Kallon ta Mardiya tayi kana Tace "Me nake gani kamar cikine a Jikin ki Ayrah? Fyad'e ya Miki?" Zafin zuciyar Ayrah ya Shiga yi mata saisaita kanta tayi kana Tace "Kina 'bata min lokaci ina yake?" "Mutumin da ya sace ki? Ya Miki fyad'e? Sannan yayi kidnapping d'inki shi kike Kira da miji Ayrah?" Mami ne tayi karfin halin rike hannun Ayrah ta zaunar da ita cike da tausayin Yar nata don zuwa yanzu a tsorace take ga kukan da Ayrah ta fara, cikin Muryar rarrashi Tace "Ayrah ki fad'a min abinda ya faruwa tun daga ranar da Kika barni a asibiti Akan zaki je gidan su Mardiya?" Shiru tayi tana kallon ta zancen zuci take " Taya za'ayi na fad'a mata abubuwan da ya faru,Taya za'ayi na fad'a mata cewar ina son Wanda yamin fyad'e a karo na ba adadi? Taya zan fad'a mata irin abubuwan da Adnan yamin?" Sai ta tsinka kanta da fad'in "Mami a hanya ya tare ni sannan yayi barazanar zai kashe ni idan ban bishi ba,Ni Kuma naji tsoron Kar ya cutar Dani sabida nasan na yaudare
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76