Chapter 25
Chapter 25
d'aura da fad'in "Yaya nane uwa d'aya uba d'aya muke dashi shi ya sha nono ya bar min kaga Kennan Ni Abban Ma'isha ne zanzo ka Kirani da Abba kamar yadda Isha take Kirana" Murmushi Haisam yayi yace "Insha Allah Abba" Daddy Har cikin ransa ya ji daddy, hakan zai tabbatarwa da Haisam ya zama d'an gida. Daddy yace "Daughter jeki ki Kira su Mummyn ku" Mikewa tayi had'e da fad'in to, tana Shiga d'akin da sallama ta Sanar dasu cewar daddy na Kiran su a tare suka fito, gaisawa suka Kuma yi Nan sukayi ta Hira tare yayin da Alhaji Abdallah sai Satan kallon Umma yake ta lura da hakan, hakan yasa duk take jinta wani iri, sai da karfe 11 tayi ya mike da zummar zai tafi daddy da mummy sukayi duk yanda sukayi suka sa ya Kwana. *TSOKACI* ```Shin wane ne Alhaji Mus'ab Aminu??``` Alhaji Mus'ab Aminu d'ane ga Alhaji Tahir Mus'ab da Hajiya Maryam Muhd, Tahir Mus'ab cikekken bafulatanin Gombe ne gaba da baya, shaharen Mai kud'i ne Wanda yayi suna a fad'in Nigeria suna da 'ya 'ya biyu dukka maza Mus'ab Wanda yaci sunan mahaifin sa sai kanin sa Abdallah sun taso cikin gata dukkanin su kuma sunyi karatu ne a kasan waje Sannan dukkanin su Business suka karanta, Bayan Mus'ab ya gama karatu a India ya dawo gida Nigeria, Bayan ya dawo ne ya da Yan kwanaki karayar arziki ya Kama mahaifinsa kasantuwar asarar da yayi zuciyar sa ta buga. Tun daga sannan mahaifiyar su ta kwanta rashin Lafiya yau da lafiya gobe ba lafiya a haka har ta shekara daga bisani ita ma ta rasu, da Taimakon Allah da na Mus'ab ya farfad'o da business d'in mahaifin nasu har ya samu Abdallah ma ya Zama mutum Shima ya fara business d'in. Tare suke koman su har suka samu sukayi aure, a Rana d'aya suka yi aure, Shi Mus'ab Yar Gombe ya samu ya aura Mai suna Maryam, shi Kuma Abdallah a yawon business d'insa ya had'u da fauziya, fauziya bahaushiyar kano ce, Bayan shekara biyu Fauziya ta haifi d'a na miji sai yayi wa Yayan sa Mus'ab takwara, Bayan shekaru uku ta haifi Yan biyu dukka mata wata hassana da Hussaina,daga Nan suka koma Kano da Zama sabida ya cigaba da lura da business d'insu na Kano d'in. Maryam hankalin ta kullum a tashe yake bata da wani buri da ya wuce ta samu ciki, kullum cikin kuka take Mus'ab shine Mai rarrashin ta. Cikin Muryar kuka Tace "Mus'ab Zaka rabu har dani ko? Ko Zaka karo min kishiya" Rungumeta yayi tsam a jikin sa yace "Bani da wacce ta fiki maryam, bazan tab'a miki kishiya ba insha Allah, kullum ina fad'a miki ki daina tada hankalin ki shi fa Haihuwar Nan na Allah ne" "Amma ai ganan Fauziya a Rana d'aya akayi auren mu yanzu yaran ta uku yanzu haka tana d'auke da cikin wata hud'u Ni ko 'batan wata ban tab'a yi ba, sama da shekaru 7" ta karasa maganar cikin kuka. Bubbuga Bayan ta yake yace "Amma ai ba dabarar ta bane Kuma kema ba laifin ki bane, tunda munsha zuwa asibito ci da dama har kasar waje munje duk zancen d'ayane dani dake duk bamu da matsala Kinga Kenan lokacin Haihuwar ne bata Zo ba, ki daina tada hankalin ki mu cigaba da addu'a" *AFTER 10 YEARS* Maryam ta tashi da zazzabi Mai zafi banda amai babu abinda take, cikiin tashin hankali ya kaita asibiti, Likita ya Sanar dashi labari Mai dad'in da ya dad'e yana son ji, farin ciki fal ransa ya Kira Abdallah ya Sanar dashi, dashi da Fauziya sunyi muran matuka, Bayan wata 9 Maryam ta sami yarta, yarinya kyakkyawa kama take sak da ubanta Amma da d'auki hasken fatar Maryam, kasantuwar Mus'ab ba wani haske yake dashi sosai ba. Abdallah najin labarin Haihuwar ya sa suka shirya dashi da matar da yaran sa hud'u , Mus'ab, hassana da Hussaina sai Autan su Faisal, Wanda a lokacin Mus'ab nada shekaru 10, Hassana sa Hussaina 8 years sai Faisal a lokacin bai cika shekaru 4. A Ranar suna Mus'ab ya Sanar musu da yarinya taci sunan mahaifiyar su wato Maryam Amma ana Kiran ta da Ma'isha, tun da sassafe suka shirya suka Kama hanyar Gombe a hanyar su ta zuwa gomben sukayi hatsari,Fauziya da 'ya'yan ta duk 4 suka rasu,yayin da Abdallah ya bugu sosai Yana kwance a asibiti Rai a hannun Allah. ________________________ Please comment and share Milhaat ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 31&32 _Continuation........_ Tun daga Nan Abba yake kwance a asibiti, Rai A hannun Allah buguwar da yayi ne ya sa bai farka ba yayi dogon Suma, Satin sa d'aya a kwance. Su Fauziya Kuma da 'ya'yan ta tun a ranar aka kai su makwancin su, bayan ya farfad'o mutuwar tasu ta girgiza shi Kennan, tun daga Nan ya ji baya bukatar aure sabida gudun kar ya sake rasa su, hakan yasa ya bar kasan gaba ki d'aya ya Koma dubai, Yana kula da harkokin su na chan,sai lokaci zuwa lokaci yake zuwa duba su, Nan ma kwanaki biyu zuwa uku kawai yake musu ya koma,wani lokacin Kuma ya kwana hotel. Wannan Kenan. *CIGABAN LABARI* Abba ba don yaso ba ya Kwan,washe gari kuwa Ma'isha Bata sa Lectures a ranar akayi sa'a Haisam ma bayi da shi, a tare sukayi breakfast karfe 10 na safe flight d'in su Abba zai tashi. Bayan sun gama karyawa Abba yace dasu su fito waje akwai abinda zai nuna musu,Bayan sun fitane ya zaro key a aljihun sa ya mikawa Ma'isha, sa hannun tayi ta karb'a had'e da fad'in "Abba ajiye maka zanyi?" Yar karamar dariya yayi yace "A a My Isha,Taki Ce na Saya mikine sabida kokarin sa kike a school" Benz Ce baka sidik sai sheki yake wani uban ihu tayi had'e da salle,da gudu ta rungumi Abba had'e da yi Masa godiya "Abba Thank You Thank you" Shima rungumeta yayi Yana "fad'in mention Not Daughter, ki dai Kara kokari akan Wanda kike yi kinji?" Ta amsa da toh da gudu ta nufi gun Mummy tana nuna Mata,Duk sukayi Masa Godiya, Sannan suka koma cikin,Abba lokacin tafiyan sa ya kusa Amma bai ga Haisam da Umma ba,cike da kulawa yace "Yaya ya Banga sauran mutanen gidan ba?" "Eh suna part d'insu Amma yanzu nasan zasu Shigo" Aiko Yana rufe baki sai ga shigowar Haisam cike da girmawa ya gaidasu Duk suka amsa. Ma'isha da saurin ta Tace "Yaya ka gani Nima an Saya min mota babu ruwana da jiran ka bare ka jaa min ajii" Murmushi yayi yace "Masha Allah , congratulations gaskiya na tayi ki murna" Mikewa tayi Tace "Kazo muje kaga motar" wucewa tayi shi Kuma ya bi Bayan ta mummy girgiza Kai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76