Chapter 10
Chapter 10
bane" Umma Tace "uhmm yaro yarone baza ki tab'a ganin abinda nake hangowa ba" Haisam yace "Umma Me hakan yake nufi, kina nufin akwai wata matsalane idan akayi hakan?" "babba ma kuwa Haisam, Baffan ka mutum ne Mai had'ari ni dukiyar Nan wallahi bataw dame ni ba , dama don kai ne nake so a karb'a maka hakkin ka, ina ji ajikina akwai abinda yake Shirin aikatawa" Ma'isha Tace "Insha Allah babu ma abin da zai faru Umma, aniyar shi ya bishi" Ta amsa da "Amin Allah ya shiga tsakanin mugu da na gari" duk suka amsa da Amin.Nan dai Haisam da Ma'isha sukayi ta kokarin jaan ta da Hira tun bata kulasu har aka fara hirar da ita. "Ka gani ko malam ai tun farko Haka nace maka kayi Amma kayi kunnen uwar shegu da ma baza a kai Nan ba" "Kinga Rabi ni bana son Mai maita magana, Allah ya kaddara hakan Sai ya Faru in ma maganar kulleni da akayi ne ai ba yau na fara shiga cikin cell ba so Dan Allah ki kyaleni naji da abinda yake damina ko Kuma na sauke 'bacin ran a Kan ki" Rabi na jin hakan ta shi ta fice daga d'akin ba tare da tace komai ba, binta yayi da kallo ya ja wani dogon tsaki. 'dakinta ta nufa tana Zama Kenan taji an turo kofa, kallon kofar tayi ganin irin kallon da take mata tayi kirkirerren Murmushi Tace "Ayra Shigo ciki mana" Wacce aka Kira da Ayra naga ta Shigo ta zauna a bakin gadon dake d'akin Tace "Mamy wai Dan Allah me ke faruwane, naga duk kina cikin tashin hankali, nasan hakan bazai rasa nasaba da Abinda ya faru da daddy bane ba, Dan Allah me daddy yayi har aka Kama shi" "Babu komai Ayra, ai daddyn naku ma ya dawo komai ya Riga ya wuce kar ki tashi hankalin ki" "Amma Kuma Mamy ke naki hankalin ai a tashe yake just in 2 days ki duba Kika yanda Kika rame Kika lalace" "Ayra kin San fa bana son ina magana Kuma kema kina yi sabida haka ko ki bar maganar Nan ko ki fice min daga d'aki bana son Shir........" "Me yasa baza ki fad'a mata ba, ai Ayra ba karamar yarinya bace ba, ta girma ya kamata ta San halin da ake ciki tunda baza ki iya sanar da ita ba Ni zan fad'a Mata" Wuri ya samu ya zauna, yace " Ayra" ta amsa da "Na'am Daddy" "Kin tuna cousin brother d'inki Haisam?" "Eh daddy d'an Uncle Ahmad" "Good" Nan ya shiga jero mata abubuwan da ya Faru shekarun baya kamo yanzu, Murmushin gefen baki tayi tace "Daddy wai dama suna Raye na d'aukan sun mutu fa" "Suna Nan a Raye" "To shi Alhaji Mus'ab d'in me had'in shi dasu da yake son taimakon su kalen dangi kawai" Mamy Tace "Na Allah Kenan ba, tun ba yau ba nake nuna wa mahaifin ki abinda yake ba dai dai bane ba, Yana ciyar damu da haram, sanan yana tufatar da mu da haram" "Haba Mamy so kike daddy ya kashe kansa da wanne zaiji? Ni daddy dama mu gudu mu bar kasan wallahi" Mamy yarfa hannu ta shigayi tayi tana sallalalami ta ce " Ayra Ashe baki da hankali ban sani ba? Kina nufin goyon bayan mahaifin ki zakiya bayan Kin San abubuwan da yake yi haramun ne, dukiyan maraya fa yake ci, nasan kinyi karatu kinsan kudin da mahaifin ki yake ci wutane Amma wallahi kin bani Mama....... " "Ke ke ke, me haka nace me haka? " Mikewa yayi ya nufe ta yace "So Kika kisa mata tsanata a ranta ko me kike nufi, wannan wani irin mumunar hud'uba kike Mata haka" "Amma malam kasan....." " Amma me, nace Amma me wallahi tallahi Rabi zan sab'a miki akan wannanw maganar wallahi daf kike da rasa auren ki" Mikewa itama tayi Tace " In rasa Mana ai auren Nan da shi da Babu duk d'aya" Cike da mamaki yace "Oh haka ma Kika ce ko?" "Eh Haka nace" "toh Shikenan kije ki na sak....." Ayra Tace "A'a daddy kayi hakuri Dan Allah, kar ka aikata, Dan Allah kar ka saki mamy" ta karasa maganar tana kuka. Tsaki yayi yace "Kinci Albarkacin Ayra, Allah ya miki Albarka Ayra" Ta amsa da amiin, yace "Naji dad'in maganganun ki hakan ne yake kara tabbatar min da cewar bazan wahala wurin d'aukar fansan da nake sonyi ba, Akwai aikin da nake so kimin, idan Kika min hakan na yafe Miki duniya da lahira." "Inshallah zan maka ko ma mene ne Daddy don samun albarkar ka" "Malam kar ka saka yarinyar Nan acikin matsalar ka ka fama Kai kad'ai" "a'a mummy mahaifina ne fa, matsalar da ai tawa ce, so kar ki damu" Murmushi daddy yayi yace "Good My Girl wuce muje kafun tayi poisoning mind d'inki" Ficewa sukayi a d'akin a tare suka bar ta ita kad'ai, Mamy ta rasa abinda yake mata dad'i, ajiyar zuciya tayi Tace "Ya Allah ka shirya min su ka ganar dasu gakiya." *BAYAN KWANA BIYU* Daddy na zaune a parlor shi da Haisam suna kallo suna Hira sama sama kasantuwar Yau lahadine yasa bai fita office ba, Mai gadi ya shigo bakinsa d'auke yake da sallama, suka amsa. Cikin girmamawa yace "Yallab'ai kayi baki" "Baki Kuma su wane ne Haka?" "Wai DPO ne da malam Hassan" "okay Ce musu su Shigo" " To yallab'ai" ya fice. Daddy yace "Son wai ina mutanen gidan Nan suke ne?" "Suna part din Umma" "Okay je ka Kira min su duka" Mikewa yayi tare da fad'in "to daddy." Tun daga bakin kofar parlor yake jiwo muryar su suna Hira suna dariya , da sallama ya shigo shima Yana daruyay duk da bai San dariyar me suke ba, yace "Nima nazo ne ayi hiran Dani" Umma tace "A'a you're not welcome here, yau ranar ta Mata ne" Yar karamar dariya yayi yace "Nikam dama nasan ba'a yina a gidan Nan Ma'isha kawai ake so" Ma'isha Tace "Ji Yaya fa dan Allah ni Kuma me ye nawa acikin maganar ku?" " Oh ma baki sani ba?" "Eh ban sani ba" "To ki taso Mana kawai ki shake min wuya na fad'a maki" Taso wa tayi ta nufe shi tana dariya yace "Ki karaso Nan kiga abinda zan Miki" Mummy Tace "Yaran Nan Basu da kunyan wallahi,Amma alhaji duk baya gani" Haisam yace "Laaa Kinga na Manta wallahi daddy ne ma ya aikoni wai nazo na Kira ku" Umma Tace " Kuma ka tsaya shirme ba" Mummy Tace "Lafiya dai ko? Nifa bana son irin Kiran Nan" Murmushin yayi Wanda ya kara bayyana kyawun fuskarsa yace "Lafiya Lau, Baffan hassane suka Zo" Dukkanin su Saida suka ji gaban su ya fad'i kallon juna Mummy da Umma sukayi a tare suka Mike suka fice a tare suka shiga dasu Malam Hassan. Mummy gefen daddy ta zauna yayin da Umma, Haisam da Ma'isha suka zauna a Kan three sitter dake d'akin DPO da Malam Hassan suka zauna a one one sitter dake kusa da su Daddy. Daddy yace "DPO shine kazo da kan ka? Ai da ka kirani zuwa office d'in" " A a y'allabai kasan an rufe case d'in Kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76