Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 41

Chapter 41

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kwanaki a kwai wani buri nawa Wanda nake so na cika, Wanda Wannan burin nawa burin mahaifinane, Wanda na cika Masa burin sa Amma na rasa dalilin da yasa bana farin ciki da hakan" Amma "Ayrah me ya Kai ki aikata irin Wannan d'anyan aiki tunda kinsan ba auren shi zakiyi ba, me yasa Kika had'a harda asiri?" "uhmn Qawata Kennan to ai da ba don ke ba ai bazan samu damar Shiga ransa ba, kinga Kenan amfanin bokan Kenan ko" Mardiya mikewa tayi cikin rashin fahimta Tace "I don't get you please ki Kara min Karin haske Akan abinda ban sani ba" "zauna kiji" Zama sukayi Nan ta Fara Sanar da ita duk abinda mahaifin ta ya Sanar da ita da hanyan da tabi har akayi maganar aure, Kama baki Mardiya tayi Tace "Innalillahi Ayrah Amma gaskiya banji dad'i ba Kuma Ni gaskiya ina kokonta Akan maganganun kin Nan Haisam Sam bazai aikata hakan ba" Rai a d'an 'bace Ayrah tace "Kina nufin kice Daddy na makaryaci ne?" Cikin inda inda tace "A....A'a Ni Sam ba Haka nake nufi ba Amma..... " Murya Mamy sukaji ma'ana mahaifiyar (Ayrah) tana fad'in "Tabbas karya ya miki" A razane ta Mike jikinta na kyar ma Tace "Mamy dama... dama kina Jin mune?" "Kwaraai Yanzu ke Ayrah kin kyauta wa Kanki Kenan? Ashe dama abinda kuka aikata Kenan ko da yake Banga laifin ki ba kina amfani da abinda mahaifin ki ya d'aura ki a Kaine, to bari na fad'a miki gaskiyar maganar, mahaifin ki shi ya kashe Yayan sa, sannan ya kwace komai da komai nasa........ " Nan ta Sanar da ita komai da komai harda yadda ya aika a kona Haisam da mahaifiyar sa. Ayrah Zama tayi a kasa, kasa motsi tayi sai hawayen dake gangarowa daga fuskar ta bakin ta rawa ta ma rasa me zata ce, Mardiya ce ta karasa inda take tasa a hannu ta d'aga ta ta zaunar da ita a kan gado fashewa tayi da Kuka tana fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un me na aikata wa kaina, me nayi na Shiga uku" Tsaki Mamy taja Tace "Kuka ba? Baki ga komi ba tunda kin biye wa ubanki zaki ji dashi" tana Kai Nan ta fita, Mardiya ce tayi ta rarrashin ta tana Jin jina lamarin tabbas mahifin Ayrah abun tsorone. Ayrah tun daga Wannan ranar ta Shiga tashin hankali mara misaltuwa tundaga wannan ranar take kiran layin Haisam Amma baya Shiga tayi kuka tayi kuka har ta godewa Allah. Yau ta kudiri aniyar ko ta halin Kaka sai ta ganshi, har asibitin da yake aiki taje aka tabbatar mata da bayi da lafiya, jiki ba karfi ta fita a hanyar ta ta fita sukayi kicibus da Farukh. Farukh na ganin ta ya kawar da kansa Kamar bai tab'a ganin ta , da sauri ta bi Bayan sa tana Kiran sunan sa baiyi niyar kulata ba ganin yadda take kiran sunan da ya ja attention d'in Mutane yasa ya tsaya, kallon ta yayi kana ya kawar da kansa had'e da fad'in "Lafiya kuwa kike ta bina?" "Am Lafiya lau dama Kaima anan kake aikine?" Kallon ta yayi yasa hannu a aljihun wandon sa kana yace "umm umm a specialist nake, tambayar Nan ce ta sa Kika tsayar Dani?" Jiki a Sanyaye Tace "A a dama ina Kiran layin sa ne baya Shiga shine nazo neman sa aka ce min bayi da lafiya me ya same sa ne Haka?" Ciza leb'en sa yayi cike da takaici yace "As if you care ta ina ruwanki da lafiyar sa bayan burin ki Kenan? To Haisam ya Shiga comma a dalilin ki kinyi farin ciki ko? Mtswww" ya tafi ya barta a tsaye a gun baki a bud'e. Ta dad'e a tsaye a gun kana ta wuce gidan su mardiya ta sanar mata da halin da Haisam ke ciki "tab wai yanzu a dalilin ku, a gaskiya Wallahi Allah bazai bar ku ba, idan kuma ya Rasa ransa a dalilin ki kema kin Zama Kamar mahaifin naki" "look mardiya nasan mahaifina ba mutumin kirkii bane ba, Amma that's not give you the right to disrespect him kin gane ko" "Am sorry am sorry abun ne ya dameni, yanzu mene ne abinyi?" Cikin Muryar kuka Tace " I don't know, I don't know am in a mess Wallahi, idan Haisam bai yafe min ba Nima bazan yafe kaina ba" "kiyi ta istigfari Sannan muyi fatan Allah ya bashi Lafiya, kin san fa Allah ba ya yafe laifin wani wa wani" "Ba Wannan ba, asirin Nan nake so a karya shi, don kin San Boka yace bazai tab'a daina Sona ba har ya mutu sai dai idan Mun tone abinda muka binne" "Ta kwana gidan sauki sai muje mu cire shi" "Shikenan hakan za'a yi zamu had'u gobe Insha Allah" Ta Mike kana ta Tace "Ni zan tafi sai anjima Amma Banga Mama ba bata nan ne?" "Eh sun fita da Ya Ma'aruf" "Oh Ya Ma'aruf d'in kin Nan yaki aure ki had'a ni dashi Mana" "Taaab d'i" " Me na wani tabd'i?" " umm babu babu muje na raka ki" a zuciyar ta Kuma Tace "Allah ya sauwake mu had'a jini da ke" Har jikin motarta ta raka ta, sai da taga fitar ta ta koma cikin gida. Ma'isha tundaga Wannan ranar kullum a asibiti take kwana take ta wuni idan ta koma gida to dalili ne Mai karfi dake a kwai bathroom na staffs hakan yasa ta kanyi wankan a Chan Amma ta fiye yi a gida, Bayan likitocin dake kula dashi ita kadaice ake bari ta Shiga kansa Nan ma sai ta sa wani irin rigar Wanda baya Kara dama an tanadar dashine sabida Shiga ICU sannan suna da takalmi na musamman idan ta Shiga takan d'auka wa Umma hoton sa ta tura mata ko kuma in taje gidan ta nuna Mata. Duk sanda ta Shiga gunsa idan ta fito Sai tayi kuka, ga Nan mutum amma ba Hali yayi magana. Kwan a tashi asarar Mai Rai, wasa wasa Haisam ya kaie shekaru har biyu bai tab'a motsi ba. Daddy,mummy da Ma'isha ne zaune a parlor, gyara Zama Daddy yayi yace "Daughter na Kira ne don ina so muyi wata muhimmiyar magana" "Toh daddy ina sauraron ka" " Yaron Nan Ma'aruf magabatan sa sun Zo nema Masa auren ki Amma nace sai na ji ta bakin ki tukunna, kina son sa?" Ma'isha ji tayi gabanta na duka uku uku baki na rawa Tace "Daddy aure Kuma?" Mummy Tace "Eh Mana Ma'isha so kike mu zauna mu zuba miki ido kina abinda Kika ga Dama? Isha idan ma bacci kike ki farka kina neman kusan shekaru 29 a duniya Amma har yanzu kin kasa fidda miji Kuma bawai kin rasa mane ma ba" Cikin Muryar kuka Tace "Mummy ni gaskiya ban shirya aure yanzu ba" Mummy Tace "Kana ji ko Alhaji, kana ji ko? Yarinyar Nan so take ta jaa Mana zagi a gari shiyasa tun farko nace ba sai kaji ta bakin ta ba asa rana kawai" "Hakane Hajiya sai yanzu na fahimci abinda Kika hango sabida haka Isha zan sa ranar auren ki da Ma'aruf Nan da 2 weeks ki Fara Shiri" Yana Kai Nan ya mike ya Shiga

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});