Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rage a makarantar, Kuma har na bar gun ban ganta ba" "Zaka yimin Shiru a wurin Nan ko Sai na buge maka baki? Kaje ka Nemo min 'yata....." Kan ta karasa maganar da zatayi ta hango Mai gadi ma Bud'e gate,Yana Bud'ewa sai ta ga shigowar Ma'isha, da gudu ta nufi inda take. πŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒπŸƒ Milhat ce Yar Terawa Please comment and share πŸƒ *DANGIN UBA*πŸƒ Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–Š* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.πŸ€™πŸ»``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobiπŸ—‘οΈπŸ—‘οΈπŸ—‘οΈ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 5 and 6 WASHE GARI Haisam bai je makaranta ba, hakan ya tadawa Ma'isha Hankali, duk ta rasa sukunin ta a makaranta har aka tashe su. Bayan an tashi musu ta ce wa driver ya kaita gidan su Yar ajin su, ta karb'i assignment ba musu ya amince ta Masa kwatancen gidan ya kaita gidan su Haisam. Haisam karar motar yaji ya tsaya a kofar gidan su hakan ya sashi fitowa don ganin wane ne, ga mamakin sa yaga ma'isha ce. Rai a d'an 'bace yace "me kike yi anan? And how on Earth did you trace my house?" Ma'isha tace "Am I forbidden from coming to your house? Sannan Kai kuma irin salon naka Kenan na karb'an baki?" " Ba haka bane, kawai ban tab'a sammanin ganin ki anan bane anyway you're welcome" "Thanks, meyasa yau bakaje makaranta ba?" Kan ya bata amsa, yaji mahaifiyar sa na tari da gudu ya koma ciki, Ma'isha bin bayan sa tayi, mahaifiyar sa a kwance tana matsanancin zazzab'i. Ma'isha na ganinta ta gane itace matar da ta sayar musu da kosai ranar. Cike da kulawa tace "Me ke damin ta?" "Ban sani ba tun jiya take fama da zazzab'in Nan" "Ka kaita asibiti kuwa?" Shiru yayi ya kasa bata amsar tambayar sai hawayen da yake zubowa daga idanun sa. Kan kace me ita ma ta Fara kuka, ta rasa abinyi hakan yasa ta koma cikin mota tana kuka, driver na ganin tana kuka hankalin sa ya tashi, cikin sauri ya Shiga cikin gidan su Haisam a tunanin sa Haisam ya dake tane, Amma yana ganin mahaifiyar Haisam sai jikinsa yayi sanyi, ya fito ya Maida ta gida. Idanun ta a cike yake faal da hawaye suka Isa gida, mahaifiyar ta na ganin ta hankalin ta ya tashi, a tunanin ta wani abun aka mata, tayi tambayar duniyar Nan taki fad'a Mata daga bisani driver ne ya mata bayanin dalilin kukan nata, tana jin haka ta Shiga rarrashin ta. Tace "Nasan yanda kike ji daughter, Amma Kar ki damu zanyi wa Mahaifin ki magana idan ya dawo, so that we should know how to take your friend's mother to the hospital" ma'isha tayi mutukar farin ciki da jin hakan. Mahaifin ta na dawowa ta Sanar dashi halin da Haisam ke ciki Shi da mahaifiyar sa, ta karasa bashi Labarin cikin kuk,hakika sun bashi tausayi sosai, yace "Karki damu Ma'isha, Babu abinda zai Sami mahaifiyar Haisam, Kuma Kinga gobe Saturday ne Babu inda zanje Kinga gobe da safe sai ki kaimu gidan su Haisam d'in, sai mu kaita Asibiti" "Thanks Dad, Amma meyasa baza mu kaita Asibitin yau ba, ina tsoron Kar wani ya same ta" "Kar ki damu Insha Allah babu abinda zai sameta, Kuma Kinga dare ta Riga tayie, Amma na Miki alkawari gobe da sassafe zamuje." Ma'isha na alfahari da iyayen ta ganin yanda suka d'auki damuwarta tasu ce, tasani tunda yace zasuje to tabbas zasuje d'in amma yanda taga rana Haka taga dare, duk a tsorace take, gani take kamar mahaifiyar Haisam zata iya rasa ranta, Kan gari ya waye ta tashi ta Shiga ban d'aki ta d'auro alwala ta jero raka'a biyu kana ta fara rokon Allah da ya bata Lafiya bayan ta idar ne ta kwanta tana jiran wayewar gari,a Haka bacci 'barawo ya sace ta. Washe gari itace ta Fara tashi duk da ba tayi bacci da wuri ba, jiki na rawa ta gyara gidan tsaf tun kan, Mummy na fita ta rike baki tace "Oh Ma'isha ke da a weekend bacci kike sai nayi da gaske ki tashi yau me ya faru haka?" "Mummy ina so muje gidan su Haisam da wurine shiyasa, Wallahi Mummy da ita na kwana a rai, gani nake kamar wani abu zai sameta" Murmushi tayi tace "Inshallah babu abinda zai sameta, Naga kin gama gyara gidan ma" "Eh Mummy" "Toh yanzu kije ki shirya Ni kuma Zan had'a mana breakfast, Daddyn ki ma ya na wanka" Ta amsa da Toh ta shige d'aki bayan ta gama shiri ta fito ta tarda mummy da Daddy suna karyawa, cikin Ladabi ta gaida su, suka amsa, Ma'isha kasa cin abincin ma tayi, wainar indomie da kwai Mummy tayi sabida zaifi saurin gamawa. Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Haisam, Haisam na ganin su tsuman tsaye yayi cike da mamaki yake kallon su, Yana ganin mahaifiyar ta ya shaida ta, har kasa ya durkusa ya gaida su, cike da sakin fuska suka amsa, Daddy yace "Yaro ina mahaifiyar ka?" Murya na rawa yace "Tana.....tana.... d'aaaa ki" Murmushi Mummy tayi tace "To ka kaimu mu ganta ko?" Jiki na rawa ya shige d'aki Suma suka Mara Masa baya, Ma'isha kuwa sai Murmushi take har cikin ranta take jin dad'in ganin mahaifiyar Haisam na raye, suna had'a da Haisam kuwa kallon tuhuma yake mata,tana ganin haka sai ta Fara dariya kasa kasa. Banda tari babu abinda mahaifiyar Haisam keyi, cike da tausayi yace "Ki kimsa ta ku fito" hannun Haisam ya riko, sannan ya cewa Ma'isha "Daughter zo mu jira su a mota" ba musu ta bi bayansu,suna isa inda motar take yace haisam ya zauna a gaban motar,shi Kuma ya zauna a gun zaman driver,Ma'isha Kuma tazauna a baya. Bayan mummy ta gama gyara ta, da taimakon Mummy da Ma'isha suka sa Umma a mota, Kai tsaye asibiti suka nufa, likitoci sunyi matukar jajincewa wurin kula da ita hakan yasa acikin Yan kwanaki ta samu sauki kamar ba ita ba. Wata rana Mummy ta kaiwa Umman Haisam ziyara, zaune suke suna Hira zuwa yanzu sun saba sosai, Nan take tambayar ta dalilin da yasa haryanzu bata biya wa haisam Kud'in WAEC ba, Bata 'boye mata ba ta Sanar da ita cewar Mijinta guba aka sa Masa a abinci da yanda kanin sa kwace Masa dukiya, ta tausaya musu sosai, a haka har suka gama hirar tasu ta dawo gida. Cikin dare ta kasa bacci, tashin Daddy tace "Am sorry na katse maka bacci" Zama yayi cikin muryar bacci yace "Kar ki damu,me ya Faru?" Nan ta shugay fad'a Masa Labarin da Umma ta bata, bayan ta gama basa Labarin ne tace "Darling ina so mu taimaka wa haisam da mahaifiyar sa" "Ina sauraron ki" "Me zai Hana tunda Boys Quarters d'in Nan babu kowa aciki a Basu part d'aya su zauna, Naga jikin nata bai gama warwarewa ba,

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});