Chapter 28
Chapter 28
ana Dole ne? Bafa yarinya bace ba tasan me take so da abinda bata so, Shima Abdallah zan Kira sa na fad'a Masa ya bar maganar sabida na lura ya na neman sata a Rai daga jiya zuwa yau" "Uhmn Alhaji Kenan yanzu duk abinda mukayi masu da abinda zata saka Mana Kenan, Alhaji dama don mu ba wallahi nasan inda Bata mutu ba da ta kusa mu...... " A tsawace yace "Ke Zaki kashe ta? Nace ke Zaki kashe ta?" Ta girgiza Kai had'e da sunkuyar da Kai, iska ya hura kana ya sassauta Muryar sa yace "Maryam zaki goge ladan da Kika Samu idan Kika cigaba da fad'an haka mun taimaka Mata don Allah Ne ba don ta biya mu ba, kar ki manta fa kece Kika kawo shawarar taimaka musu har Kika sa na dawo na su cikin gidan nan, Dan Allah idan na Isa dake ki bar maganar nan ban yarda ki sake Mata maganar ba bare ki nuna Mata a fuska" " Insha Allah zanyi yanda kace kayi hakuri" Ma'isha da Meerah Havilla Ice cream suka nufa, Bayan Meerah ta tabbatar da ta kwantar wa da Isha hankali, ice cream suka Sha har sai da akayi la'asar tayi suka koma gida, sai da Isha ta ajiye ta a gida kana ta wuce gida. Haisam kuwa school ya Shiga, Duk da bayi da Lectures jiran ta yayi ta gama Lectures suka Sha hiran su ya samu hankalin sa ya kwanta , sai Kuma yayi sa'a yau bata fito da motar ba hakan ya bashi kaita gida. Bayan sallar Isha Umma kasa zuwa gun Mummy tayi suyi hirar da suka Saba, Ma'isha na d'akinta taji Duk bata jin dad'in zaman hakan Yasa ta fito parlor ganin ba kowa ta nufi d'akin Mummy da sallama ta shiga Tace "Mummy ya na ganki a kwance yau baza a yi hiran parlor bane?" "Uhmnn bani Jin dad'i ne" "Subhannallah me ya same ki?" "ciwon Kaine ba wani Abu ba" "Amma kinsha magani ko?" "Eh Nasha" "To Allah ya sauwaka" "ameen" Mikewa tayi Tace "Bari naje part d'insu Umma" "Okay" tab'e baki Isha tayi ta nufi part d'insu Umma. Ganin Umma Bata parlor ta wuce d'akin ta cike da mamaki Tace "Umma kema a kwance ko kema bakya Jin dad'in ne?" Kirkirerren Murmushi tayi tace "Eh wallahi bana Jin dad'in jikina" "Oh ikon Allah sai kace Kun had'a baki ga mummy ma a chan ta kwanta wai kanta na ciwo" Umma a ranta Tace "Oh Allah kar dai ita ma tasa maganar a ranta kamar Ni" a bayyane ta ce "Lallai kamar mun had'a baki" "Allah ya baku Lafiya" "Ameen" "Ya Haisam fa yana Nan?" "Ki duba shi a d'akinsa d'azu dai baya Nan ban San ko ya Shigo ba" Ta amsa da "Ok sai da safe Allah ya sauwaka" "ameen daughter nagode." 'dakin Haisam ta nufa ta shige d'akin taga wayam Bayanan, kwan kwasa kofar d'aki tayi ko Yana ciki taji shiru hakan ya tabbatar mata da Bayanan d'aga kafad'a tayi irin I don't care, ta fice. A hanyar ta, ta fita suka had'u da Isha yace "Princess kin dawo Kenan?" "Eh na dawo tun d'azu" "Su Umma fa" "Suna kwance wai Basu da lafiya" "Duk su biyun?" " Eh Umma wai zazzab'i take ji Mummy Kuma Wai ciwon Kai" "Hmm kin San d'azu bakyanan me ya Faru?" "A'a sai ka fad'a" Nan ya jero Mata abinda ya gani da idon nunsa , cike da mamaki tace "eh Lallai no wonder biri yayi Kama da mutum, to Amma me ya faru haka?" "Allahu a'a lam, Umma taki fad'a min amma ki gwada tambayar mummy muji ko menene" "kaji ka ya Haisam mummy ce zata fad'a min sai kace baka San halin ta ba, dama kaine maybe zata fad'a maka" "Okay muje hope tana d'akinta ba d'akin Daddy ba?" "Eh tana d'akin ta" "Alright muje" Yana tafe tana biye da shi da sallama suka Shiga d'akin mummy sunyi sa'a bata rufe ba don tashin ta Kennan zata rufe, tana ganin si tayi Murmushi Tace "ku Kuma fa daga ina?" "Daga d'akin Umma" Ma'isha ta bata amsa ba. Mummy ta amsa da "okay" Haisam yace "Mun Zo gunki ne mummy" "Lafiya dai ko?" Ta kalli Haisam ta kalli Isha Haisam murya na rawa yace "la.....Lafiya lau,kawai magana zamuyi mummy" " To ku zauna mana" ta koma ta zauna a Kan gado ta d'auki Pillow ta d'aura a cinyar ta sannan ta d'aura hannayen ta akai tana kallon su. Zama sukayi akan kushin d'in dake d'akin kasa kasa Haisam yace "kiyi magana Mana" Ita ma Tace "Kayi magana Mana" "Princess kiyi magana Mana Dan Allah" "A a wallahi Yaya ai kai kace min zaka mata magana mun Zo Kuma ka kasa" Mummy na Kallo ikon Allah, sai kuskus take ji bakin su na motsi Amma bata jin abinda suke fad'i,a d'an fad'a fad'a Tace "Idan baza ku fad'a min ba ga hanya Nan ki fice min bacci zanyi" tana nuna musu kofar fita. Haisam ne ya gyara Zama Yana wasa Yana d'an bubbuga kafar sa da hannun sa yace "mummy dama.....dama.....dama d'azu da na Shigo ne naji Abba na fad'a,naga Kuma kin Fad'i kalma wa Umma Sannan kina kuka Kika shige ita ma kukan naga tana yi,mummy dukkanin ku bamu tab'a ganin ku a cikin Wannan yanayin ba a iya zaman da mukayi daku bamu tab'a Jin Kan ku ba,shine muka zo ki fad'a mana Inda Hali,don naga duk Kuna cikin damuwa" Ajiyar zuciya Mummy tayi Tace "Son ina da niyar yi maka maganar ko da kuwa baka Zo ba, sabida nasan Kai kad'ai Umman ku ke Jin maganar ka Idan mukayi sa'a ta amince da bukatar mu,ba wani abu bane ba dama Abban kune............ " Nan ta bayyana Masa komai Kama daga Kan mutuwar Matar sa da 'ya'yan sa da kuma dalilin sa na kin yin aure. Murmushi Haisam yayi Wanda yake Kara bayyana kyawun fuskar sa yace "Mummy yanzu dama Akan wannan ne kike kuka Duk kuka tashi hankalin ku? Ni a ganina wannan abun ba abin tashin hankali bane ba, zanyiwa Umma magana Kuma Insha Allah zata amince, ko ba komai ai abun farin cikine wannan duba ga irin tsawon shekarun da Abba ya d'eba bayi da niyar aure ace Rana d'aya ya ce zaiyi, Kuma na tabbata Insha Allahu Abba zai rike ta da zuciya d'aya sabida na lura Shima Yana da son Mutane Shima kamar daddy, insha Allah zata amince fatan mu shine Allah ya tabbatar da alhairi" "Kaai Amma naji dad'in maganganun ka son, Allah yasa ta amince d'in" "Ameen Mummy" Ma'isha da tun d'azu take kallon su Tace "Ni Idan akayi auren Nan ai barka na sabida Abba na auren mummy gidan su zan koma da Zama in huta da....... " Turo kofar da akayi ne da d'an karfine yasa ta kasa karasa maganar ta Duk su ukun suka Mike a razane mummy baki na rawa Tace "Al.... Alh..... Alhali Lafiya? Tana leka Bayan sa ganin ba kowa ta cigaba da magan "Alhaji Lafiya na gan ka a Haka?" Rai a mugun 'bace yake nuna ta da d'an yatsa Yana fad'in "Haven't I warned you not to talk about it again? Haven't I?" "Alhaji Amma...... "
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76