Chapter 7
Chapter 7
mikewa Umma tayi had'e da Mika tana ambaton "La'ila ha illallalah Muhammaddar rasulullah" Ma'isha cikin muryar shagwa'ba tace "Umma zan biki mu kwana tare please" Murmushi tayi Tace "To Muje daughter" riko hannun ta tayi sukayi wa mummy Sai da safe suka fice, mummy Murmushi tayi ta girgiza Kai ta shige d'akin ta. WASHE GARI Bayan sun idar da sallar asuba Ma'isha ta dawo part d'in su, Kai tsaye d'akin ta tashiga ta yi wanka sannan ta fito don Taya mummy aiki a kitchen, Tana Shiga kitchen ta tarar da mummy juya ruwa a flask. "Mummy ina Good Morning" "Ahhhh 'yar Umma har Kun tashi?" Murmushi tayi Tace "Eh mummy" "To ya kuka tashi,ya Umman taku?" "Lafiya Lau Alhamdulillah" "Amma meyasa baki tsaya kin tayata aiki ba Kika dawo?" "Itace Tace na dawo, shiyasa Kuma Kinga , zamuje school, bara nayi wanke wanken" "A'a ki bari yarinyar nan zata Zo ta yi kije ki samu ki shirya naga har kinyi wanka je ki kawaii ki shirya" "mummy tun yanzu? Karfe 6 fa" "Ki dai sake dubawa 6:30 ne" Agogon bangon dake manne a kitchen d'in tace "Gaskiya lokaci yana gudu Bari naje na sa uniform" "Okay" Ta fice a kitchen d'in Bata d'auki lokaci mai tsawo ba ta dawo, a lokacin bakwai har ya wuce, a dining room ta tarar da mummy da Daddy bayan sun gaisa ta karya, a gaggauce ta fice tana musu sai ta dawo, inda ake parking mota ta nufa, ta tarar da driver da Haisam suna Hira cikin girmamawa ta gaida driver kana ta maida kallon ga Haisam tace "Good Morning Yaya" Murmushi yayi yace "Morning" Duk suka shige motar suka, ba su tsaya a ko ina ba sai makaranta. Haka rayuwa ta kasance wa ma'isha da Haisam a tare suke zuwa school Kuma su dawo a tare, sun shaku sosai haka ma mummy da Umma kusan komai tare suke, sannan daddy yana iya bakin kokarin sa wurin ganin ya cika alkwarin da ya d'auka wa Haisam, duk abunda yake so yanayi masa, a hakan har suka rubuta WAEC and NECO d'in su Kuma Alhamdulillah paper su duk yayi kyau. Daddy yayie matukar farin ciki hakan yasa bai 'bata lokaci ba wurin yi musu registration na JAMB ba,Kuma Alhamdulillah sun ci yanda a ke bukata duk su biyun a gombe state University sukayi(GSU) applying,suna zaman jiran admission. Da gudu ta shigo ta murna had'e da tsalle tana Kiran sunan Daddy da Mummy, Mummy dake kitchen ita da Umma cikin Sauri suka fito a tare sukace "Lafiya? Me ya faru?" Tambayar su yayi dai dai da lokacin da Daddy ya fito cikin Sauri daga d'akin sa, yace "Ma'isha me ya faru?" Sai tsalle take Haisam kusa hard'e hannu yayi Yana kallon ta, Umma Tace "Kai kunci gidan ku ana muku magana baza ku amsa ba?" Da gudu ta rungumi Umma tace "Admission ya fito kuma duk mun samu" Girgiza kai daddy yayi yace "Dad'i na dake ba a raba ki da shirme wallahi, shiyasa Kike Mana ihu a cikin gida?" " Daddy ai Dole ni da Yayana mun samu admission a department d'in da muke so" Umma Tace "Masha Allah, kice yanzu muna da Doctor da Kuma pharmacists a gida" Ta amsa da "Insha Allah" Mummy maida kallon ta tayo ga Haisam cike da kulawa Tace "Son ya naga Kai baka tsallen? Ko bakaji dad'in admission d'in bane?" "a'a mummy kawaiiii...... " Daddy ne ya katse shi yace "Toke Banda abunki hajiya Ma'isha tayi Shima yayi ya za a banbanta yaro da babba" Duk dariya sukayi, ya d'aura da fad'in "Allah ya taimaka, Haisam yaushe zaku karb'o admission d'in" " Ai daddy mun karb'o" "Sharp sharp Kenan, anyways congratulations to you both" A tare Ma'isha da Haisam suka amsa da "Thank you daddy." "Emmm yanzu abunda za'ayi ku biyuni sai muyi maganar kud'in registration d'in don Ina so a Fara Lectures daku" ya wuce d'akin sa su biyun suka bi bayan sa mummy da Umma Kuma suka koma kitchen. Daddy ya Basu dukkanin kud'in da suke bukata,washe gari a tare sukaje sukayi registration tun safe suka fita basu dawo har sai dab da magrib a gajiye suka dawo,hakan yasa dawuri sukayi bacci. Bayan sun gama registration,suka Fara Lectures d'insu yanda ya kamata. Daddy na gani zaune a office, kwankwasa kofar da akayi ne yasa ya d'ago kansa yace "Come in" sannan ya cigaba da rubuce rubucen da yake, Jin an shigo ya d'ago kansa don ganin Wanda ya shigo Murmushi yayi yace "Bismillah zauna" Ba musu mutumin ya zauna, hannu ya Mika Masa suka gaisa, mutumin ne ya ce "naji Labari kaje gida har Sau Uku baka sameni ba, gashi kuma ban Sanka ba" "eh hakane kamar yanda nace maka a waya wata magana nake so muyi da Kai Mai muhimmanci, shiyasa ma kaga na takura kazo office Dina" Murmushi yayi ya gyara Zama yace "Business ne Kennan, kasan na dad'e ina so na fara business da company ku Amma Allah baiyi ba" Daddy yace "Malam Hassan zamu Zo Nan d'in ma Amma kamun Nan....." Wayarsa ya zaro a aljihun gaban rigar sa gallery ya shiga ya Mika Masa wayan yace "ko Kasan wannan?" Karb'an wayan yayi ya dad'e Yana kallon sa, a zuciyar sa yace "Wannan kamar Haisam, Kai ba shi bane ya akayi ya Zama Haka maybe kamane" A bayyane Kuma yace "Yallab'ai ban sanshi ba Gaskiya" ya Mika Masa wayan, Kan wani hoto ya koma ya Kuma Mika Masa wayan yace "Wannnar fa da fatan ka gane ta?" Yana karb'an wayan yana ganin Hoton a raza ya Mike hannun sa rawa yace "Zainab, wannan kamar Zainab dama tana raye ne, Zainab ce fa matar Yayana ko? Ko dai Kama ne ya naga ta canza?" _______________________ Please share and comments Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 11 and 12 Daddy Shima mikewa yayi yace "hakan na nufin ka santa Kenan?" Malam Hassan Sai kallon sa yake ya kasa cewa komai, girgiza Kai daddy yace "calm down, calm down ka zauna" Jiki a sanyaye ya zauna Idon sa akan hoton Sai zare Ido yake Yana kallon Hoton, daddy yace "Na dad'e ina neman ka tsoratan da kayi hakan ya tabbatar min da maganar da Zainab ta fad'a min Akan ka gaskiya ce" Murya na rawa yace "me me me ta taa fad'a maka? Kar ka yarda da ita makaryaciya ce" "Give a good reason da zan gano cewar makaryaciya ce" "Ashe dama tana raye ni na d'auka ta mutu" Maganar da yake ta maimaitawa Kenan. Daddy yace "Bata mutu ba,ko ince Basu mutu ba,Ashe dama Kaine Wanda yasa aka Kona musu gida ina da labarin gidan ya Kama da wuta nayi iya tunanin Duniyar Nan ya akayi wuta ya Kama,ashe Kaine?" Mika Masa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76