Chapter 65
Chapter 65
masa komai ba,murmusawa ya kumayi kana yace "Am sorry Ayrah babu yanda zanyine,sabida Ina son ki Ina so na kasance Dake na har a bada,idan kin amince wallahi zan aure ki kuma na miki alkawari daga yau bazan sake kusantar ki ba har sai na mallake ki a matsayin matata ta sunnah." Mikewa tayi Tace "Bayan abubuwan da kamin Adnan? I won't fall for your lies anymore, ka cuce ni, ka wulakanta Ni, yanzu Kuma kazo kana gaya min maganar banza maganar wufi" ta karasa maganar tana kuka Mai tsuma zuciyar Mai sauraron. Ledan da ya shigo dashi ya ajiye, har kasa ya durkusa ya hard'e Hannayen sa alamun roko, hawayene suke gangarowa daga idanun sa Zuwa kuncin sa, cike da mamaki take kallon sa, cikin sarkewar murya yake fad'in "Dan Allah Ayrah, Kar ki min haka kiji tausayina Wallahi ina sonki Kuma Ina kaunar ki, bazan iya Rayuwa babu ke ba Ayrah" Tunda ya Fara maganar take kallon sa cike da mamaki, ji take kamar ta shake Masa wuya ya mutu. "Kana Sona kace?" Cikin sanyin Murya take magana. "eh Wallahi , ina sonki sosai fiye da tunaniin Mai tunanina" "Hmm to ina so ka bud'e kunnuwan da kyau kaji abinda zan Fad'a maka yanzu" magana take in a serious tune, ganin hakan ya mike ya tsaya da kafafun sa, Duk Jikin sa yayi sanyi. Matsowa kusa da shi tayi,har suna iya jin numfashi junan su, cikin Murya Mai d'an karfi Tace "Ni Ayrah Hassan na tsane ka, na tsane ka kuma bazan tab'a son ka ba" Yace "Ni Kuma ina sonki ina sonki Kuma bazan tab'a daina son ki ba" " Ohh haka kace? Haka kace?" Cikin d'aga Murya yace "Eh haka nace" "To tabbas nice ajalin ka Adnan" Murmushi yayi kana yace "Da nafi kowa Farin ciki idan Kika kashe Ni" Wani abu taji ya tokare ta a kirji, Bata Jin dad'in yanda Sam bai da mu da maganganun da take Masa ba, tsaki tayi ta shige d'akin ta. Kallon ta ya tsaya yi har ta shige d'akin, a bayyane yace "Wallahi sai na sace zuciyar ki kamar yadda nayi a baya." Kofan d'akin ta ya nufa ya tura a hankali ya hango ta zaune Akan gado tana aikin kuka, ji yayi ba dad'i, ledan hannun sa ya ajiye Mata ya fita gaba ki d'aya daga gidan. Alhamdulillah Haisam na samun sauki sosai don har ya Fara takawa, maganar sa Kuma ya Dawo normal, Duk da wasu kalmomin idan ya furta su kamar yaro. Wata Rana, Yana kwance a Kan gadon jinyar sa, Isha Kuma na zaune a gefen sa a Kan plastic chair kallon ta yake yayin da ita Kuma hankalin ta na Kan wayan ta. Muryar sa taji ya kira sunan da ya saba kiran ta dashi "Princess!!!" Ajiye wayar hannun ta tayi tace "Akwai abinda kake bukata ne?" Ta mike tana kallon sa shima kallon ta yake, da ta lura da yana kallon cikin ta, itama kallon cikin natan tayi Wanda a yanzu Yana cikin wata hud'u, ya Fara fitowa, da sauri ta koma ta zauna. Murmushi yayi kana yace "Princess Fad'a min abubwan da nayi missing Bayan na Shiga comma" Wasa ta shigayi da hannun ta kana ta Fara fad'in Duk abubuwan da ya faru, Kama daga yanda ya Shiga comma har aka Kawo shi asibiti, da shekarun da ya d'eba Yana kwance, Sannan ta Fad'a Masa tayi aure Amma Bata shekara ba mijinta ya rasu, sannan ta Fad'a Masa halin da Malam Hassan ke ciki da 'batan Ayrah. Ta karasa bashi labarin tana matsar kwalla, hankalin sa yayi mugun tashi Jin abubuwan da ya faru bayan kwanciyar sa, cike da jin tausayin ta yace "Yanzu ciki kike dashi?" Kai a kasa Tace "Eh" Ajiyar zuciya yayi kana yace "Allah ya raba lafiya" Ta amsa da amiin. Yace "ban San meyasa Baffana ya tsane ni ba , Bayan ya kashe min Uba Nima ya so ya hallaka ni, sunyi wasa da zuciya ta shi da Ayrah na kudiri aniyar d'aukan fansar abinda suka min Amma jin kaddarar da ta same su na tsinci kaina ina matukar tausaya musu, yanzu abinda yafi damuna shine Ina Ayrah take?" "An bin cika ta ko ina Amma ba labari, gidan TV da gidan radio Duk ansa cigiya Amma shiru" " Allah ya Kare ta" "amiin" " Amma ya Jikin Malam Hassan d'in?" "I don't know gaskiya but Yana nan a asibitin nan" "really tashi ki rakani" " A a Ya Haisam, babu inda zaka ce a haka Kar ka manta fa ba cikekken Lafiya gare ka ba, tunda haryanzu kafar ka na rawa, by the way meyasa ma zaka damu da wa'annan mutanen Bayan irin abubuwan da suka maka?" " It's simple...... " Mike Yana Mai gyara jallabiyar sa, ya d'aura da fad'in "They are my Family Princess, ai ba'a Canza wa tuwo suna" kallon sa ta tsaya yi tana tunaniin irin hali irin na Haisam ace Duk abubuwan da suka masa Amma ya damu dasu, ganin bata da niyar magana yace "Muje ko?" Ba don ta so ba, ta Mike tayi gaba yana biye da ita, girgiza kai yayi. Ward d'in da Malam Hassan yake suka nufa, kofan Isha ta tura had'e da yin sallama kasantuwar, uniform ne na asibiti a jikinta hakan yasa suka d'auka tazo Duba shi ne, Mamy na ganin Haisam biye da ita ta Mike tana kallon sa, shima kallon ta yake don bazai tab'a manta fuskar ta ba, sabida ta kasance tana nuna Masa so da Kauna tun Yana yaro ba kamar yadda Baffan nasa yake ba, Murya na rawa Idanun ta fal da hawaye Tace "Hai......sam!!" Malam Hassan da ke kwace Yana fuskantar bango yaji an Kira sunan Haisam ya juyo a hankali, yayin da Nabila ita ma ta Mike tana kallon sa, sabida ita Sam bata tab'a ganin d'an uwan nata ba. _________________________ Please comment & vote Milhat ce Yar Terawa [8/13, 8:26 PM] Miilhaat Writer✍🏻: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 69&70 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation......``` Murmushi Haisam
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76