Chapter 17
Chapter 17
daddy ne, akan Kar na barki kiyi driving sai kin Kara girma" "Yanzun wai ni yarinya ce?" "Eh Mana sosai ma Amma..... " Farukh ne ya dakatar dashi da fad'in "Malam kana da niyar Shiga lectures d'in Nan kuwa ko kuma na tafi na Barka da kanwar ka ku gama surutu?" "A a tashi muje, princess ki jirani kinji?" Kai ta d'aga Masa alamun to basu fita ba sai da ya biya su kud'in su, a tare suka fita ta nufi Lt din da zata yi lectures Suma suka nufi nasu. 'Bangaren Su Aysha Aysha Rai a 'bace ta nufi garden d'in cikin makaranta inda d'alibai sukan zauna su Sha iska, wasu suna karatu wasu Kuma hirar su suke Maza da mata. Zama tayi ta dafe kanta da hannun bibbiyu, ji take kanta ba tsarawa Kamar zai rabj gida biyu, mardiya ce ta zauna a gefen ta tana kallon ta ba tare da tace Mata kala ba. Aysha ta d'ago kanta ta kalli mardiya kana ta maida kanta kasa cikin Muryar kuka Tace "Mardiya I need your help ki taimaka min wallahi Ina son gayen Nan har cikin Raina Dan Allah give me advice" Cike da mamaki take kallon ta tunda ta Fara maganar,Baki a bud'e ta ce" Wai ke dama dagaske son gayen Nan kike?" Hararar ta tayi Tace "Eh Mana" "ikon Allah Amma ya akayi Haka bayan ranar Asabar d'in Nan kika ce min kun had'u ko dama kin San shine?" "Ba wani sanin sa nayi ba, kawai dai ina yawan ganin sa a cafe ne tun ina ji yana burgeni har naji na fara son sa, ranar Asabar d'in ne Naji bazan iya jurewa ba na tinkare sa har na samu damar karb'an Number sa" Kad'a Kai mardiya tayi had'e da fad'in "Eh lallai gayen Nan na daban ne, nifa duk tunani na shi ya tinkare ki ashe kece, Amma wallahi ba girman ki bane ki zauna kina kuka akan na miji ba, ki dube ki fa kyakkyawa dake babu na mijin da bazai so ki ba sabida kina da duk qualities na kyau" "Hmm mardiya Kenan ai wallahi duk kyawuna yau da naga yarinyar Nan na Raina Kai na, kamar ita tayi kanta,moreover ki ga yanda yake rawar jikin akanta, alamu sun nuna Yana sonta sosai" "Gaskiya Allah yayi halitta a wurin Nan,kamar ka sace ta,Amma Ni a gani na ai wannan ba babbar matsala bace ba, kawai ki mata snatching just shot your short, Amma kamin Nan ki fara tabbatar da cewar ba Soyayya suke ba tukunna" Cikin damuwa ta maraice fuska Tace "Tayaya Kenan zanyi hakan? Guy d'in Nan fa haryanzu ba wani sake min yayi ba bare har na sa ran samun soyayyar sa" "hmm Qawata Kennan, sai kace ba mace ba ai kiransa kawai zakiyi cikin dabara irin Tamu ta mata Zaki tambaye sa" "Shikenan zan kirasa zuwa anjima insha Allah" "Yauwa ko kefe, idan Kuma bamu samu yanda muke so ba sai mu had'a shi da malamai su mana maganin sa" Wata shu'umin dariya sukayi suka tafa Aysha Tace "Shegur Qawata shiyasa nake yinki ta hannun damana" Dariya mardiya tayi Tace "Sa wasa ni d'in ai ba daga Nan ba" "Tabbas Ni shaidace" Mardiya Tace "Ya labarin mutuminki?" "Wa Kenan fa?" "Wa kuwa banda Abdul" Doguwar tsaki tayi tace "Please spare me wa ke ta tashi Yanzu?" "Hahahaha Qawata ba ji,kice Haisam ke ruling yanzu" "ai fad'a ma 'batawa,shi Yana ruling anan" ta nuna kirjin ta,ta d'aura da fad'in "Shi kuma wachan Abu ke ruling a tasa zuciyar" "hahaha ki yayyafawa zuciyar ki ruwan sanyi Qawata Haisam da kansa zai nemi soyayyar ki, alkawarina ne wannan" "Nagode Qawata" Mikewa Tayi Tace "mu tafi ko?" Cikin rashin fahimta mardiya Tace "Ina zamuje?" "Gida Man" "Lectures d'infa" "na yafe" tana kaina ta fara tafiya,bakiea bud'e mardiya ke kallonta,ganin da Gaske take ta Mike ta bi bayanyanta da d'an sauri had'e da gudu, motar Aysha suka nufa,tada motar tayi suka bar cikin school d'in, dropping d'in mardiya tayi kana ta wuce gida,dage unguwar su d'aya hatta layin su ma d'aya hakan yasa bata 'bata lokaci ba ta isa gida. Karfe 4:10pm Bayan ta gama lectures ta tsaya jiran sa har sai karfe 6 da Yan mintuna ya Zo suka Kama hanyar gida, yana driving sunan sharar hirar su. Chan Tace "Yaya Ayshan Nan a ajinku take ne?" "a'a Yar aji d'ayane?" "To how comes Kuka Saba?" "Sabawa a hakan? It's just this Saturday muka had'u fa, itace ma ta karb'i number na" "sabida me?" "Wai so take na Zama Tutor d'inta" "Tutor kuma, Kuma ya yarda Yaya?" " So kike nace Mata bazaiyu ba? Nifa Musulmi ne itama haka so hakkina ne Akan taimakawa ko wani Musulmi tunda ina da halin taimaka Mata me zai Hana naki amincewa" Iska ta hura Tace "Hakane" "Amma irin tambayoyi Haka princess am I safe?" Murmushin yake tayi Tace "You're safe Mana Yaya, kawai dai naga sai aikin kallon ka take Kuma bata ji dad'in bani abinci a Baki ba, nayi tunanin ma itace auntyn tawa" Dariya yayi yace "Haba princess ai da kece Zaki Fara sanin hakan,ni ba Soyayya muke da ita ba,hasali ma ban tab'a zaman minti 30 da ita ba" "Amma fa Yaya Na lura Kamar son ka take" "ah haba Dan Allah?" "Allah kuwa" "Lalle d'an Ni d'in Nan?" Murmushi kawai tayi yace "Well bani da wannan lokacin Yanzu idan na tashi soyayyar ma ke zansa ki nema min Matar aure" " Kamar dagaske" "Allah kuwa dagaske nake miki na rantse miki da kauyen kakana" Dariya tayi sosai Harda tafi, a Haka suna Hira har suka Isa gida. Har cikin ranta taji dad'i ko ba komai hankalin ta ya kwanta, tunda tasan ba sonta yake ba, Bata da sauran damu sai na soyayyar sa da fatan ya fahimci hakan. Suna isa gida suka tarar da su Mummy da Umma shigowar su gidan Kenan Suma, bayan sun gaisa ta wuce d'akin ta Shima Haisam ya wuce nasa d'akin, dake dukkanin su biyu suna da assignment basuyi kallon da suka Saba ba, hatta chat d'in ma basuyi ba. Haisam na zaune akan gadon sa yana browsing yaga shigowar Kira ba wayarsa kallon time yayi yaga Karfe 11:38pm a bayyane yace "Aysha da Daren Nan?" Picking yayi ya Kara a kunnen sa daga d'ayan 'bangaren tace "Barka da war haka yallab'ai" Murmushi yayi yace "Yauwa Barka dai Yallab'iya" Yar karamar dariya tayi Tace "da fatan dai ba bacci Kake ma tashe ka ba?" "umm umm ba bacci nake ba, assignment nake yi" "Oh so sorry na dame ka,duk da ma na ce ka Zama Tutor d'ina kaki ko?" "No Kar ki damu, ba ki nayi ba ai na fad'a miki idan kin shirya ki Sanar dani" " To na shirya gobe idan Allah ya Kaiimu" "To Allah ya Kaiimu" Ta amsa da "Ameen ya Allah" Yace "ya kike d'azu kawai Kika tafi ba sallama" "Uhmnn gani nayi ka fad'a lambun soyayya baka ji baka gani" Dariya yayi yace "Soyayya Kuma Ni d'in?" "Eh Mana Kai da princess d'inka harfa abinci naga kae Bata, nace lallai kud'in masoyan asaline" Girgiza Kai yayi Kamar tana gaban sa yace "Ni ba Soyayya nake ba" "Kiyayayya Kake yi Kennan?" "Hahaha a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76