Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tayi Tace "Alhaji bari na Shiga daga ciki" ya amsa da "Toh." Ya rage daga Abba sai daddy a parlor ,gyaran murya Abba yayi yace "A gaskiya Yaya bazan yi shiru na cuci kaina ba Umman Haisam ta kwanta min a Raina,da fatan zaka bani auren ta?" Yar karamar dariya daddy yace "Ikon Allah daga ganin ta sau d'aya kace min ka kyasa?" "Eh Mana love at first sight kake ji,look Yaya ka daina min dariya Kai da ya kamata kayi farin ciki ma" "Sosai Kam,naji dad'i sama da 20 years kaki aure ai abin a duba ne,Kuma Insha Allah baka da matsala sabida Zainab bata da matsala ko kad'an tana da kirki" Shafa kirjinsa Abba yayi had'e da fad'in "Alhamdulillah abinda nake son ji Kennan tunda ka yabe ta magana ta kare,yanzu dai ya za'ayi?" "kar ka damu zansa Maryam ta Mata magana Insha Allah,Allah dai yasa ta amince" "Amiin ya Allah Ni da kaina zanyi Mata magana ma, Maryam Uwar Maryam" Fitowar Mummy Kennan ta ce "To me Kuma ya Faru naji ana Maryam Uwar Maryam nasan cuta ta za'ayi" Dariya sukayi daddy yace "A'a ba cutar ki za'ayi ba alfarma Zaki Mana ko ince taimako" Zama Mummy tayi Tace "Ahaaaf na sani ai da wala kin goro a miya, nasan ba a banza ba wannan kirarin" Daddy ya Sanar mata da abinda Abba yake bukata, Murmushi tayi Tace "Kai Alhamdulillah finally addu'ar mu zata karb'u, a gaskiya idan ka auri Zainabu zan ji dad'i sosai sabida mutuniyar arziki ce, gata da tsoron Allah, mace Ce ta gari, fatana shine Allah ya Sanya alhairi yasa Kuma ta amince kasan dai baza'a mata Dole ba" Abba yace "Nima ban bukaci hakan ba, in dai Bata so ki kyaleta Amma fa zanzo ki sa mata ra'ayi na gaskiya" "Kar ka damu Insha Allah ma zata amince kaga Shikenan ta Zama ta gida Duk da dama Yan gida ne" Nan sukayi ta hirar su har karfe 9:30 daddy da kansa ya kaisa Airport yaso ganin Umma Kan ya tafi Amma bata fito ba, Ma'isha Kuma da Haisam d'akin Haisam suka nufa suna ta Shan hirar su. Suna cikin hiran ne Tace "Yauwa Yaya Kace Akwai maganar da kake son fad'a min, mene ne?" "Yauwa kin tuna min, ba kince kina so na sama Miki aunty ba?" "Eh hakane" "To burin ki ya kusa ciki" "Ban gane burina ya kusa cika ba? Soyayya ka fara ne?" Murmushi yayi yace "Dad'i na dake kanki naja sosai princess, hakane soyayya nake Kuma ina sonta sosai" Ma'isha jin maganar Nan dai dai yake da kamar wuka aka dab'a Mata a kirjinta ji take d'akin na juya Mata, shiru tayi kana tace "Wace Ce haka Yaya?" Murmushin Jin dad'i yayi yace "Kin santa ai" "Haba dai ya sunan ta?" "Aysha!!! A razane ta Mike Tace "Aysha?" Shima mikewa yayi yace "Eh Aysha lafiya naga kin razana haka?" Ma'isha a ranta ji take kamar ta shake mishi wuya ya Kuma cewa "Princess kuka, meyasa ki kuka?" "Yanzu duk soyayyar da nake maka baka gani, da abun da zaka saka min Kennan? Baka san cewa ina sonka ba, me zakayi da wata Aysha? Dame ta fini? Kiran sunan ta da yayi da d'an karfine yasa ta dawo daga tunanin da take ya Kuma cewa "Princess tell me please what happened, why are you crying?" Cikin Muryar kuka Tace "Yaya ba Kai bane?" "Me nayi princess?" "Har zaka Fara soyayya ba tare da ka fad'a min ba" Dafe Kai yayi ya sauke wani ajiyan zuciya "Na d'auka maganar Farukh zai tabbata ne Ashe ba hakan bane ba?" " Me Farukh d'in yace?" Girgiza kai yayi had'e da Murmushi yace "Nevermind Amma princess Allah ya shirye ki komai kuka komai kuka gaskiya mijin ki zai Sha fama Kam, don wallahi aka Kai Masa ke raino zaiyi" Murmushi tayi "Nikam bari na tafi Kan Abba...... " Ganin agogon dake d'akin yasa Tace "Wayyo karfe 10 da rabi" ta nufi kofa da gudu Haisam yace "Lafiya me ya Faru?" "Abba zai tafi bamuyi sallama ba Kuma idan ya tafi sai yafi 3 years bai dawo ba" Ta fita da gudu, parlor ta nufa, tana Shiga ta tarar da Umma da Mummy a zaune mummy da d'an fad'a fad'a Tace "lafiyan ki Kike Mana gudu a gida haka?" "Mummy Abba da Daddy fa?" "mtsww sun fita" kawai Tace Mata had'e da kawar da kanta. Dafe goshin tayi Tace "Kai Amma naso mu yi sallama wallahi Amma ba komai zan kira shi a waya" tana Kai Nan ta shige d'akin ta, ba ta dad'e ba ta fito ta shirya cikin sutura mai kyau Tace "Mummy zanje gidan su Ameerah" "Aikin Kenan ai bare yanzu kinyi mota" Murmushi tayi Tace "Sai na dawo Umma sai na dawo" Umma Tace "Ai Ni munyi fad'a dake" Kama baki tayi Tace "Na Shiga uku Umma laifin me nayi kiyi hakuri" "Uhmn wai ace a miki babbar kyauta haka Amma baki fad'a min ba" Fad'awa jikin Umma tayi tana fad'in "Kiyo hakuri Umma wallahi d'azu ma da na Shiga da niyaan fad'a miki ne Amma Yaya yasa na manta kiyi hakuri kizo muje kiga motan" "To na sani dai Dole mantawa kikai, kar ki damu kije sai kin dawo ki kaini d'ani" Da murnar ta ta Mike Tace "To Umma sai na dawo d'in" Ficewa tayi tana ganin Haisam hannu kawai ta d'aga Masa ta shige motar ta key ta sa wa motar ta fice abin ta girgiza Kai yayi ya Koma ciki wayar sa ya d'auka yan kirata tana gani taki d'auka a bayyane Tace "Chaap ina driving d'in zan d'aga call d'in ka sai na Isa" Har ya katse Bata d'aga ba text ya tura Mata yace ```"Wato yanzu na Zama 0 a gun ki kinyi mota ba komai nagode"``` Bud'e text d'in tayi ta karanta Murmushi tayi parking tayi ta Masa ```"reply da ba Haka bane Yaya zanje gidan su Meerah ne, Kuma zan dad'e sai na dawo"``` ta ajiye wayar tana Isa gidan su Ameerah ta nuna Mata motar ta ta taya ta murna sosai, sai da suka gama kallon motan kana ta suka koma d'akin ta, wani irin Kallo Ameerah takeyi Mata Wanda yasa har ta Fara tsarguwa Ma'isha kallon kanta tayi Tace "Lafiya me ya Faru kike min Kallo haka?" Cike da kulawa Ameerah Tace "Isha wai ke Dan Allah baza ki cire damuwa a ranki ba? Haka Zaki cigaba da Zama?" Kirkirerren Murmushi tayi Tace "Me Kika gani ni Lafiya na Lau fa" "Haba Isha na sanki fa over 10year you're my best friend ko da baki fad'a min ba na miki sanin da zan iya gane farin ciki da bakin cikin ki, tell me maganar Haisam d'in ne haryanzu?" Ajiyar zuciya tayi sannan Tace "Shine kin San d'azu yake fad'a min wai Ashe soyayya suke da Aysha?" "I said it, ai na fad'a miki ki cire shi a ranki ko Kuma ki fad'a masa Amma kinki and now it's late" "Anya Ameerah kin San soyayya kuwa? Kar ki manta fa shi so halittace ba yin kaina bane wallahi abun ya fi karfi nane" ta karasa magani cikin kuka. Hannu Ameerah tasa a goshin Ma'isha Tace "Akwai zazzab'i a jikin ki" Mikewa

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});