Chapter 16
Chapter 16
tunda hakan ba halin sa bane ba." Haisam sauri yake sosai sabida saura minti biyu kachal time ya cika, Yana Shiga LT zaman sa kenan zai ga shigowar malami, ai kuwa yana Shiga yasa aka rufe Masa kofofin, Nan ya Shiga arranging d'insu zaman da sukayi babu Wanda zai iya magana da wani inko kayi za'a jika sanan baka Isa Kati satar amsa ba layin medicine ba wasa kwata kwata su sha Tara ne a ajin bayan mutum sama da talatin ne suka samu admission sauran tun a aji d'aya aka zubar dasu GSU Kenan ba wasa. Alhamdulillah test yayi wa Haisam dad'i mintuna 30 aka basu Amma shi a cikin sa'a ya gama cikin mintuna 20,bayan sun gama duk suka fita, wurin motar sa ya nufa jin an Kira sunan sa yayi saurin juyowa Murmushi yayi yace "Kaga manyan mutane" "Su ku Kenan ko?" Hannu suka Sha yanda samari suke Haisam yace "Ya test d'in dai?" Yace "Alhamdulillah" "Masha Allah, Allah ya bamu sa'a ya amsa da amiin. Haisam yace "Dama cafeteria zanje ban samu na karya a gida ba muje Mana" "Wallahi Nima ban karya ba muje d'in" Sai da ya ajiye jakarsa a mota kana suka wuce suna tafiya suna Hira sabida dakwai d'an tafiya daga College of medicine zuwa commercial area. Inda ya Saba cin abinci Suka nufa, as usual chips and chicken yace a kawo Masa, abokin tafiyar tasa Kuma ya ce Fried Rice suna cikin cin abincin su ya hango Aysha Wanda itama tana d'ago Kai Kennan suka had'a Ido dashi Murmushi ta sakar Masa Shima ya maida Mata. Karasowa sukayi da ita da kawarta sallama sukayi suka amsa musu, Tace "Zamu iya Zama?" Haisam yace "Bismillah Ku zauna" Bayan sun gaisa Tace "Yallab'ai wannan kawatace Sunanta mardiya a pharmacy take" Murmushi ya Wanda a ko da yaushe shine abun yinsa yace "Nice to meet you pharmacists" Ta amsa da "Nice to meet you too" Ya maida kallon sa ga Aysha yace "Yallab'iya wannan abokina ne sunan sa Farukh a medicine yake" Yar karamar dariya tayi Yallab'iya da yace ne ya bata dariya Tace "Sannu Dr Farukh" Zaro Ido yayi yace "Dr? Da saurana tukunna, cemin Farukh d'in ma kad'ai ya wadatar" "Hahaha to shikenau Sannu Farukh" Yace "Yauwa ai yafi dad'i ko? " Dariya sukayi dukkan su, suna cin abinci suna Hira, wayar Haisam ce ta Fara ringing ajiye spoon d'in hannun sa yayi, Yana picking cikin Muryar Shagwab'a Tace "Yaya" Ya amsa da Na'am "Princess" Cikin sauri Aysha ta d'ago kanta suka had'a Ido da mardiya, ji tayi kanta ya fara sarawa a ranta take maimaita sunan Princess? Shin Yana da matane ko kuma budurwa,inaa duk yadda akayi budurwar sace taya ma za'ayi ace wannan yarin santalelen Saurayi ace bayi da budurwa? Lallai aikina ya jiku zanyi fafutakan neman soyayyar sa sannan ne rabashi da so called princess d'in nasa. Haisam yace wayan sa yake hankalin sa kwance, tunda ya fara wayar bai daina Murmushi ba alamun Yana Jin dad'in wayan, yace "To princess kizo Mana ki sameni a cafeteria Sai kici abincin" Dariya yayi yace "Na Amince zan saya miki duk abinda kikaso Kuma sai kin cinye ehe." Bata d'au lokaci Mai tsawo ba ta karaso cafeteria dake dama ba wani nisa tayi ba tun daga nesa da ta hango Aysha taji gaban ta yafi a bayyane Tace "Itace na gansu tare ranar, ba shakka itace Aysha" Ajiyar zuciya tayi Tace "Koma mene ne zanji gaskiyar a yau" _____________________________ Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 21 and 22 Tafiya take kanta a kasa, hannun ta rike yake da Yar karamar jaka Wanda bazai wuce handout biyu bane aciki, a hankali take tafiya hankalin ta kwance har ta Isa inda suke sallama tayi had'e da jaan kujerar dake gefen Haisam ta zauna. Murmushi Haisam yayi yace "Barka da zuwa the only princess in Haisam Palace" "Uhmn Yaya Kenan princess kawai ashe da saura na" "Wa ya gaya miki? Ke Kanki kin San ke ta dabance" Murmushi tayi sai Yanzu ta maida kallon ta ga su Aysha dake aikin kallon ta Murmushi tayi Tace "Sannun ku fa" Mardiya ce ta amsa da "yauwa" Ganin Aysha tayi nisa a tunani ta d'an tab'a ta, a d'an razane Tace "Yauwa sannu ya kike" "Lafiya Lau" Haisam yace "Princess meet Aysha and Aysha this is My princess bani da tamkar ta a Rayuwa" Kirkirerren Murmushi Aysha tayi Tace "Nice To meet you, to Amma ita d'in bata da suna ne? Haisam Yar karamar dariya yayi yace "Tana dashi Mana kawai dai sunan ne yayi min nauyi bana iya Kiran sa sai on special occasions" Aysha zaro Ido tayi sannan Kuma ta tab'e baki had'e da girgiza Kai Tace "oh lallai" Yace "Sai dai idan ita zata fad'a miki da bakin ta" Aysha Tace "Ya sunan ki?" "Ma'isha"kawai Tace a takaice. "Suna Mai dad'i" " Thank you" Ma'isha ta maida kallon ta ga Farukh da aikin cin abincin sa kawai yake, Ma'isha dariya tayi Tace "Haba Ya Farukh duk don Kar naci ne kake ta sauri ko?" Sai da yasa hannu ya kurb'i ruwa kana yace "Na Isa Ma'isha kawai dai naga baku da niyar gama surutun nakune kin San ance kowa da damuwar sa Ni abincin ne damuwa ta" Haisam yace "Zaka ji da shi ai" Cikin sanyin Murya Tace "Yaya My promise yunwa nake ji" "Me Zaki ci?" "Ka zab'a min komai ma nikam" "To kin San Ni abinci na d'ayane idan Zaki ci sai a kawo miki" "Ai Yaya tun bana son chips ka sa na Fara son shi" Murmushi yayi yace "Barka na kinnga ko ba komai Zaki Rika yi Mana a gida" Murmushi kawai tayi Nan da Nan yasa aka kawo Mata ta hau ci, har ya karb'i spoon d'in ya Fara Bata baki. Aysha kamar zata had'iyi ranta ta Rasa abinda yake Mata dad'i tsinta kanta tayi da mikewa ta bar wurin ba tare da Tace komai ba, mardiya ma ta bi bayan ta. Haisam kuwa bai ma San sun tafi ba , Yana Nan Yana feeding princess d'insa Saida taci ta koshi ya lura ba su Nan, kallon Farukh yayi dake Kallo a wayar sa yace "Haa'ah yaushe Kuma suka tafi?" "To ka Zama Romeo ina zaka ji tafiyar su? Duk da ma na ga Kamar sauri suke don Nima ba kulani sukayi ba suka tafi" Tab'e baki yayi ya d'aga kafad'ar sa irin halin ko in kula d'in Nan ya maida kallon sa ga Ma'isha yace "Karfe nawa zaki gama lectures d'in?" "Karfe 4" "Ni Kuma sai 6 ya zamuyi Kenan? Zaki jirani ko Zaki koma da napep don bazan barki Kiri driving ba" d'an turo baki tayi Tace "sabida me Yaya?" "Umarnin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76