Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a, to Shima dai d'an uwan soyayyar ne, amma taya za'ayi nayi soyayya da Kanwata?" Cikee da farin ciki tace " Au dama kanwar kace? " "Eh kanwatace da me Kika d'auka?" "Na d'auka budurwar ka ce" "To ki ajiye Kanwata ce,ai Ni bank da budurwa ban ma tab'a soyayya ba" "Na dai ji ban yarda ba" "Allah kuwa trust me ba wasa nake Miki ba,sai dai idan ke zaki nema min Yanzu" "A a idan Kuma na nema maka waccce Bata maka ba Kuma fa?" "Zata ma yi insha Allahu" "To Insha Allah zan nema maka waccce zata dace da kai" "Da kuwa naji dad'i sosai" Nan sukayi ta hirar su kusan na mintuna 20 kana ta Masa sai da safe suka sauke wayar a tare, kwanciyar ta tayi yayin da Haisam ya cigaba da abinda yake yi. ________________________ Ba na ganin comment d'inku Please kuyi sharhi sannan kuyi sharing. Taku a kullum Milhat Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 23&24 *...............WASHE GARI* Kamar kullum a tare suka shiga school tun karfe 7 na safe, Yau Haisam ya Riga Ma'isha Gama lectures hakan yasa ya zauna zaman jiranta a Mango garden na cikin School. Kiran Aysha ne ya Shigo wayar sa, picking yayi da sallama daga d'ayan 'bangaren ta amsa da "Wa'alaikassalam yallab'ai kana lafiya?" "Ina lafiya ke fa?" "Nima haka" "Masha Allah ka Shigo kuwa?" "Eh na Shigo" "Ok please kana ina ne nazo na same ka" "Ina mango garden" "Okay muna kusa ma gani Nan karasowa" Ya Masa da " okay" ya kashe wayan. Girgiza Kai Aysha tayi Tace "Qawata Kinga bawan Allan Nan, Yana da wani habit d'in da bana so wallahi" "Me Kenan fa?" "Bai tab'a Kirana ba tunda Amma idan na kirasa shi yake fara cutting call d'in which is very bad" ta karasa maganar kamar zatayi kuka. Mardiya Tace "It's not a big deal qawata tunda in Kika kirasa yana d'agawa Kuma yana sauraron ki ai Shikenan Kuma Nan gaba da kansa zai Rika neman ki" Huci tayi tace "Shikenan tunda kince Haka shiyasa a ko wani lokaci idan ina bukatar shawara Kai tsaye ke nake nema nasan zan samu solution" " I will always be here for you Qawata,yanzu dai tashi kije ki same shi before it's too late" Aysha tace "I thought tare zamu" "A a kaaai, kamata ai daga ke sai shi zaki fi fahimta" ta kashe mata Ido d'aya,duka Aysha ta Kai Mata ta kauce. Mikewa tayi ta Masa sai anjimu da jaddada mata idan ta gama zata kirata sai su koma gidan tare,tayi tafiyar ta, ba d'au lokaci mai tsawo ba kasantuwar LT d'in da take da mango garden ba nisa hakan yasa tayi saurin Isa inda yake. Da sallama ta karasa inda yake bayan sun gama gaisawa Nan ya mata umarnin da ta fito da handouts d'inta, Nan ya zari d'aya ya Fara mata tutorial d'in sunfi awa d'aya yana mata, Amma fa hankalin sa na Kan wayarsa minti minti yake dubawa daga bisani Tace "Akwai abinda kake jirane? Naga sai faman duba time kake" "Hmmm eh, Time nake dubawa kar princess tayi ta jirana karfe 3 zata gama lectures" Tab'e baki tayi Tace "Wai dole Kai Zaka kaita gida ne?" "Eh Mana to wa zai kaita in bani ba?" Ganin yanayin sa ya canza tayi saurin fad'in "Lallai kana ji da ita sosai Naga karfe 2 yanzu da sauran time ai" Yace "Eh gashi wayata ta kusa d'aukewa ba chaji Kuma na baro cable a gida Dana saka a mota, kar ta Kira bata same Ni ba" Ta amsa da "Hakane" Yace "Anyways mu cigaba ko?" Ta amsa da "Toh" Nan ya cigaba da Mata tutorial d'in, ganin hankalinsa yayi nisa a abinda yake koya Mata tasa hannu ta kashe wayar tasa sannan ta maida ta ajiye. Sun dad'e a zaune a gun ya d'auki wayar sa ya Danna yaga a kashe tsaki yayi yace "Damn it!!!" Tace "Lafiya kuwa?" Yar karamar tsaki yayi yace "Wayar ta d'auke" "In time ne bari na duba maka a wayata" Yace "Yauwa please duba min." Aysha na duba time taga karfe 3 da kwata Tace Masa "2:30" Zaro Ido yayi yace "Wai tun d'azun Nan 30 mints kawai mukayi?" Tace "Eh" "Lallai time baya gudu" "Ko dai ka gajine? Mu bari sai gobe?" "A a kar ki damu mu cigaba kawai." Murmushin kyeta tayi ba tace Masa komai ba ya d'aura daga inda ya tsaya. Ma'isha tafi minti 20 tana jiran sa, Kiran wayarsa take Amma switch off sai ta tuna tana da Number Farukh ta shiga dialling har kusa yankewa ya d'auka cikin Muryar ta mai dad'in sauraro Tace "Ya Farukh ina wuni?" Ya amsa da "Lafiya" cikin Muryar bacci, Tace "Am sorry kana bacci na tashe ka ko?" Yace "Eh wallah but kar ki damu ya akayi?" "Dama na d'auka kuna tare da Yayana ne" "A'a mun rabu tun d'azu da mukayi sallar azahar but yace min zaiyi wa Aysha tutorail but ki kirasa ki ji" "Uhmn number a kashe, Amma Bakomai nagode sai anjima" ta katse wayar tayi ba tare da ta ji amsar sa ba. Girgiza kai yayi yace "kishi kumallon Mata, Amma guy d'in nan don ya raina min hankali yace min ba Soyayya suke da Ma'isha ba mtss" ajiye wayar yayi ya koma baccin sa, Ma'isha kuwa Mango garden ta nufa dake tasan wurin zaman sa Kenan yawanci. Tun daga nesa ta hango su suna zaune dai dai lokacin da Aysha take dariyan sunan wani scientist da ya fad'a dariya take sosai Shima ya fara taya ta a Fili Tace "Tutorial d'in kenan" har ta nufi inda suke sai Kuma ta Canza shawara ta koma, gate na makarantar ta nufa tana fita ta tari napep ta wuce gida, ita kanta taji ta wani iri sabida shine karo na farko da ta shiga napep sannan shine karo na farko data Koma gida ba tare da Yayan ta ba. Kiran sallah da akayi ne Haisam ya Mike a zabure Aysha ma mikewa tayi tace "Lafiya?" "Kamar kiran sallah fa nake ji?" "Eh Kiran sallah ne" Ajiye Mata handout d'in yayi da saurin ya bar gun ba tare da yace mata komai ba, baki bta bud'e ta tsaya kallon sa har ta daina ganin sa bata bar mamaki ba, wa'anda suke zaune a gefen su Kuma suka tsaya kallon ta, tsaki tayi ta wurga musu harara da sauri suka kau da kansu Tace "magulmatan banza kawai Mtssw" ta d'auki Jakarta da handout d'in da Haisam ya ajiye ta bar gun. Ma'isha na Isa gida ta tarar da su Mummy suna part d'insu Umma, hamdallah tayi ta shiga d'akin ta wanka ta fara yi ta d'auro alwala bayan ta idar da sallah ta kulle kofar d'akin ta

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});