Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ku kuka Haife Ni bani ce na haife kuba na fad'a muku ba sau d'aya ba ba sau biyu ba Akan Ku bar zancen Nan Amma kunki, ina guje muku fushin uban kune, Duk lalacin sa fa shine mahiaifin ku ya Kamata ku San da wannan" "Amma Mamy........ " Wani irin ihu sukaji ya d'auki cikin gidan Duk su biyun a razane suka mike, Ayrah da Nabila ko wacce da gudu ta fito daga d'akin su suna son ganin mene ne ke faruwa. Sunusi yace "Mamy kamar ihu na ji ko?" "Eh Nima naji" Wani ihun suka Kuma ji wannan karon Muryar mace ne take kuka had'e da ihu, Ayrah Tace "Kamar daga d'akin Daddy ne" Nabila Tace "Eh daga d'akin sane" Mamy ce ta haura da saurin Gaske Suma suka bi Bayan ta,Kai tsaye d'akin ta fad'a ba tsuman tsaye tayi tana kallon sa. Faisal Ne hannun sa rike da Adda jikin sa duk jini sannan malam hassan da Yan matan Nan Guda biyu suna cikin jini,dukkanin su tsirara,wani Kara Ayrah ta sake, Nabila Kuma ta fashe da kuka. Mamy Zama tayi da d'an karfi a kasa tana kallon su cikin jini, d'ago kanta tayi ta Kalli Faisal dake huci cikin Murya Mai sanyi Tace "What have you done Faisal? What have you done" Cikin d'aga murya yace "Abinda ya Dace dasu Mamy ya Isa Haka na gaji da ganin ki Cikin kunci da tashin hankali" "Faisal ka kisa? Faisal ka kashe su, ka kashe har Mutum uku" Jin maganar da Mamy keyi ya sanyi shi ya yatsar da addan dake hannun sa jiki na rawa yace "A a Mamy ni Wallahi banyi niyar kashe su ba, kawai inaso ne na rau nata su" Sunusi ne yayi kansu murya na rawa yace "Suna motsi Basu mutu ba mu Kai su asibiti" Nan suka Shiga Sanya musu kaya, Basu tsaya 'bata lokaci ba sai medical center suka kaisu ,a A&E (accident & emergency) aka ajiye su, likitoci na ganin su suka ce baza su tab'a su har sai hukuma sun sa hannu, babu yanda basuyi dasu ba Akan su basu taimakon gaggawa in yaso zasu je suyi report Amma suka ki sabida Haka law yake, Faisal da Sunusi ne suka nufi motar da suka Zo dashi suka wuce Police station. Bayan sun Isa police station d'in sukayi narrating abinda ya faru Nan take aka Kama Faisal, hankalin Sunusi yayi mugun tashi ganin ansa d'an uwan say cell. Police d'aya aka sa suka Dawo asibitin tare da Sunusi, sai da police d'in yasa hannu kana aka Shiga basu taimakon gaggawa, Mamy Jin an Kama d'an ta tayi ta kuka, ita kuka su Ayrah kuka Sunusi ne ke ta aikin rarrashin su. "To ya zanyi Meerah, na amince na aure Amma Wallahi gangar jikina da zuciyar ta bata aminta dashi ba har yanzu" "Yau 5 days da bakin ku Amma na Jinjina wa Ma'aruf ya kwanta dake a gado d'aya ba tare da ya tab'a ki ba?" " Mtsww ni Nace miki muna kwana tare? A parlor yake kwana" " Isha kin bani kunya wallahi Sam bata tunaniin zakiyi hakan ba, tunda kin San baza ki aminta dashi ba ai da baki aure shi ba" " Na d'auka Zan iya ne shiyasa na amince da hakan, bazan iya ce miki bana son Ma'aruf ba kuma bazan iya ce miki ina kin sa ba , I don't know what the problem is" "Dallah malama Kar ki 'bata min Rai mu bar maganar please don wallahi ji nake kamar na daka ki wallahi" "Ban fahimce ki ba Isha kina nufin baki bashi hakkiin sa ba, kinsan Allah na fushi da ke ko?" Ganin tayi shiru yasa tace "Nasan kin San abinda Kika aikata ba dai dai bane Kuma wallahi sai Allah ya tambaye ki, tunda kin San bakya son sa ai da baki bari an d'aura auren ba" " Ni nace miki bana son sa?" Cikin Muryar tuhuma " Baki ce ba Amma actions speaks louder than words" "To ina son sa shiyasa ma na aure sa kin gane ko? So mu bar maganar ya wurin aikin?" "kalau" a gajarce ta bata amsa. "Yau fa almost a week banje Naga ya Haisam ba, Wallahi Duk na Shiga damuwa" "Laa kin tuna min ma, kin San me ya Faru?" "A'a tell me" " Kina nufin baki ji labarin da yake ta yawo a gari ba?" "Umm umm banji ba, tunfa da aka kawo ni gidan Nan ko waje ban leka ba, in takaita miki ma part d'in mom kawai nake zuwa shima baifi sau uku naje ba" "To Kar kad'a kunnen ki ki Sha labari" ta karasa maganar tana Murmushi. Gyara zama tayi tana kallon ta a kage tace "Tell me, me ya Faru" "Malam hassan na kwance a asibiti Rai a hannun Allah" ta karasa maganar cikin Murya kamar zatayi dariya, zaro ido Isha tayi Tace "Wani malam Hassan d'in?" "Malam Hassan dai Wanda Kika sani" "Tooooh me ya same shi" "Wai Yan Mata ya Kawo har cikin gidan sa" " Ban gane Yan mata ba?" "To bara na fito miki a Mutum karuwai ya Kawo har cikin gidan sa, shi Kuma d'an sa ya fusata ya sassare su da Adda, yanzun Nan da nake gaya miki Yan matan sun mutu shi Kuma yaji mummunan rauni" ta karasa maganar tana dariya, Isha Tace "Meerah baki da hankali Wallahi, yanzu me abin dariya anan?" "Komai ma, this called for a celebration Wallahi" "Bai Kamata ace Musulmi ya Shiga tashin hankali ba Kuma kice ki tsaya kina murna" "Wai ko baki gane maganar wa nake bane Kam?" " Na gane mana ba mahaifin Ayrah ba, Baffan Haisam,har naji tausayin su wallahi?" "uhmnn lallai shine har kike cewa kina tausayin su?" " Uhmn gara ke" mikewa tayi ta d'aura da fad'in "Ni Zan wuce gida" Itama Isha mikewa tayi ta amsa da "muje na taka miki" Ma'aruf da tun d'azu ya shigo Yana tsaye a bakin kofa yana Jin maganar da suke musamman ma maganar sa yasa shi ya kasa Shiga d'akin yana jin suna kokarin fita yayi saurin komawa parlor ya zauna, Yana danna wayar sa. ________________________ Please comment and share Mihaat Ce Yar Terawa 61&62 '''Continuation.......''' cike da mamaki suke kallon sa, murya chan ciko Isha Tace "Yaushe ka Dawo?" 'dago kansa yayi ya Kuma maida kansa Kan wayar sa kana yace "Yanzun Nan shigowa na" Meerah cikin tsigar tsokana Tace "Ango Ango kasha kamshi" Yar karamar dariya yayi yace "Meerah manyan gari ashe kina Nan gaba ki d'aya kin kimu" "Aaaaahhh wane ni kawai dai na baku lokacine kuci amarcin ku da kyau, Amma har sai kun gaji dani" " Baza mu gaji ba gaskiya, so ya aikin dai?" "Alhamdulillah, Amma ba Dad'i Wallahi aminiyata bata Nan so wurin ya Zama min so boring,ya Kamata ka bar min ita haka ta Dawo bakin aiki" Murmushi yayi yace "Zata Dawo ai da zaharan hutun ta ya kare" "To Shikenan, Allah ya nuna Mana" Ya amsa da amiin, Tace "Sai anjima" Ya amsa da "A gaida gida" " Gida zaiji" Tayi gaba Isha Tace "Bari na rakata" Yace "Alright" Har wurin mota ta rakata, sai da taga fitar ta kana ta Shigo cikin gida, ta iske

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});