Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kasa. Dafe kafad'ar tayi Tace "Isha!!" 'dago kai tayi a hankali ta na kallon ta, Tace "I know how you feel son Wanda baya sonka babbar matsala ce but you can't force him to love you" Cikin Murya kuka Tace "Kin fad'i gaskiya, Dole na rarrashi zuciya ta" sai Kuma tayi Murmushi bayan hannun ta tasa ta share hawayen dage gangaro wa a fuskar ta d'aya nabin d'aya kana ta d'aura da fad'in "Insha Allah zan cire Ya Haisam a raina please ki taya ni da addu'a" "Insha Allah dear" Ma'isha Tace "Kwana biyu ba mu had'u ba ba wani gulma ne?" "Hahaha Allah ya shirye ki Isha kina cikin damuwar ma baza ki Canza Hali ba?" "Ahhh ya zanyi to? Kefa Kika ce min na cire shi a raina to it starts from now" Dariyar ta Kuma yi Tace "Akwai su dayawa har sai kin gaji da fatan wuni zakiyi?" "Eh sai 5 zan koma" "Kai Amma naji dad'i wallahi" Murmushi kawai Ma'isha tayi bata ce komai ba. Ameerah Tace "Yauwa mutumin ki kullum sai ya tambayeni ke" Cike da rashin fahimta Tace "Wa Kenan?" "Ma'aruf Mana" "Mtswww wai dama yana Nan? Ni wallahi na ma manta da wani ma'aruf" "Hmm to na tuna miki, please give him a chance" " I can't dallah,Ni yunwa nake ji ma me Akwai?" Girgiza kai Ameerah tayi ta fahimce ta so take ta kawar da maganar sabida tun shigowar ta Tace zata kawo mata abinci tace a koshe take, riko hannun Ma'isha Ameerah tayi had'e da fad'in "Zo muje kitchen mu duba me suka girka don dama Nima tun breakfast ban ci komai ba" Nan suka nufi hanyar kitchen, a hanyar su ta Shiga kitchen suka ci karo da mahaifiyar Ameerah har cikin girmawa wa ta gaida ta ,ta amsa ba yabo ba fallasa, suka shige cikin kitchen. Haisam kuwa Yana fita gidan su Farukh ya nufa, a d'akin Farukh na hango sa yana zaune hannu a goshin sa yana murzawa Wanda hakan ya zame Masa jiki da zaran ransa a 'bace yasa hannu yayi ta murza goshinsa a Haka har ya huce. Farukh yace "Look nifa banga laifin yarinyar Nan ba, Bayan Kaine ka mata ba dai dai ba Kuma ta baka hakuri sannan ka nuna Mata Kai d'an iskane" Gyara zaman sa yayi kana yace "Jiman ya za'ayi na fad'a maka matsala ta Kuma na tsaya kana goyon Bayan ta?" "Ba goyon Bayan ta nake ba,Ina dai fad'a maka gaskiya ne, yarinyar Nan fa son ka take Amma ka kasa gane hakan" A zabure ya Mike yace "so bangane tana Sona ba" Shima farukh mikewa yayi ya ce "Eh Mana baka lura da hakan ba,kishine yake cin Ma'isha" Yar karamar dariya yayi yace "No No it can't be ba so na take ba nifa Yayan tane" ya koma ya zauna. "Eh kai Cousin Brother d'inta ne like you told me and Akwai aure a tsakanin ku,Kuma kaima kana sonta baka gane hakan bane haryanzu" "Yes she is my cousin but,bazan tab'a son Ma'isha ba, a matsayin Kanwata na d'auke ta wallahi Bayan hakan babu komai a raina,And wani abunda baka sani ba,ina ji na Fara son Aysha" Zama farukh yayi yace "nasan za'a Zo Nan, Amma Ni Kam am not in support gaskiya Wai Aysha mtsww" "Me Ayshar tayi bata had'u bane? Ko tana da wani mugun Hali Wanda Ni ban sani ba?" " NO NO ko kad'an kyakkyawa ce Kuma na lura kanta na d'an rawa ba kamar Ma'isha ba,Gata kyakkyawa,ga sanin ya kamata sannan Bata da rawan Kai" "Nifa Kuma a hakan nake son kayana,idan Kuma kana son Ma'isha ne zan maka jagorawa har wurin daddy" "Ai da kuwa na Rika sa maka Albarka har karshen rayuwata in dai na mallaki Ma'isha a dalilin ka,Amma bazan iya son maso wani ba so count me out" "Shirme kayi rawa kayi kid'a duk Kai kad'ai" mikewa yayi yace "Tashi muje Masallaci daga chan zan wuce gun habibaty" Dariya Farukh yayi yace "Wata sabuwa inji yan cha-cha wai har an Canza ma Aysha suna?" "sa wasa" yayi maganar yana shafa kirjin sa,Yana jin kansa a sama. Tab'e baki Farukh yayi yace "Nawa Ido Allah sa kar kazo daga baya kana da na sani,Ni dai bata min" " Ni Kuma tamin" Yana kai Nan yayi hanyar fita har ya bud'e kofar ya waigo yace "gwamma ka fara sonta sabida she is my wife to be idan ka gama Kallo na ka same Ni a waje." Yayi ficewar sa da d'an gudu Farukh yabi bayan sa. Bayan sun idar da sallar la'asar ya Kira Aysha ya Sanar da ita yana hanyar gidan su, da kwatancen ta ya kai kansa gidan su, abinka da unguwar manya bai Sha wahala ba ya Isa kofar gidan su a GRA. Har cikin gidan ya Shiga yayi parking motar sa,kujera tasa a ka fito musu dashi suka zauna ta sa aka jera Masa kayan shashaye da fruits ruwa kawai yasha Nan ya fara kwararo mata da abinda ke zuciyar sa, Aysha ba 'bata lokaci ta karb'i bukatar sa,Hira suka Sha sosai sai har Saida ya ji an fara Kiran sallar maghrib ya Mike ya yi Mata sallama,har wurin motar sa ta raka shi Yana fita ta koma cikin gida zuciyar ta fal farin ciki. Ma'isha hira suka Sha sosai karfe 5 saiga mallam kabiru ji sukayi kamar kar su rabu, har jikin mota ta raka ta, da tabbacin Sunday Mai zuwa Ameerah zata Zo gidan su, Nan ya tada motar suka wuce gida. Isowarsu yayi dai dai da Shigowar Haisam gidan, Zama yayi a motar Yana kallon ta, ta ganshi Sarai su Amma tayi kamar bata gansa ba ta shige cikin gida, kitchen ta Shiga ta tarar da Mummy da masu aiki suna girki tana supervising ta baya ta rungumeta had'e da fad'in "Mummy na, na dawo" Mummy dariya tayi Tace "Daughter so kike ki karyani ko?" Sake ta tayi had'e da fad'in "A'a mummy na Isa, idan na karyaki ina zan sa kaina?" "Ina fa zaki zauna da Umman ki da Yaya ki da Daddyn ki" Rufe Mata baki tayi da hannun ta Tace "Yi shiru mummy bana son kina fad'in hakan" "Nima zolayar ki nake Ma'isha" "Yauwa, Mummy naga kuna ta aiki daddy zai dawo ne?" "Eh Kuma zaiyi baki shiyasa" "Gaskiya daddy Kwanan nan baya Zama baya yin sati a gida fa" "Aikin Kenan sai dai mu bishi da addu'a" "Allah ya taimaka Masa, ya dafa Masa" "Ameen daughter je ki Samu kiyi sallah ki Zo ki tayani" Ta amsa da to ta nufi d'akin ta Tora kofar tayi a hankali, wurin ajiye takalmi ta nufa ta cire takalmin ta sannan ta rataya jakar ta juyowan da zatayi ta hango mutum a kwance a Kan gadon ta, dafe kirji tayi tana ambatan "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" _______________________ Please comment and share Na kusa na Fara removing marasa comment, and please idan na cire ki kar kiji haushina Milhaat ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});