Chapter 21
Chapter 21
na amsa da ameen. Da guda na koma gidan su Haisam don ganin Wace wainar ake Toyawa. Bayan Umma da Ma'isha sun gama girki suka zauna zaman ci, Umma da kanta taje ta Masa magana Akan yazo suci abinci yace Mata ya koshi, ta dawo abinta Ma'isha kuwa duk yanda take son Tuwo ta kasa ci , gashi Nan tuwon shinkafa sukayi da Miyar alaiyahu yaji gyad'a sai zuba kamshi yake. Har karfe 9 Haisam yaki fitowa hakan yasa tayi wa Umma sai da safe ta koma part d'insu. Mummy da Daddy ta tarar a parlor ta musu sannu ta Shige d'akin ta Bata zauna sukayi Hira ba kamar yadda suka saba, gyara Zama daddy yayi yace "Hajiya baki lura ba kamar yarinyar Nan akwai abinda ke damin ta" "Na lura da hakan ya wuce ita da Yayan nata?" "hmm Haisam da Ma'isha Kenan wannan karon Kuma me ya Faru" Nan mummy ta Sanar dashi abinda tayi, tsaki yayi yace "Ni kaina ta 'bata min Rai banji dad'i ba bare shi da akayi wa, ko da yake zasu shirya kansu" Mummy Tace "Sanin hakan ne yasa ban Shiga cikin maganar tasu ba, sun fi kusa" Nan suka cigaba da kallon su suna Hira, daga bisani suka kashe TV suka koma d'akin su. "Allah kawata kice kin kuntata mata yau?" "Trust me mana, nice fa Kuma kin San me abun burgewar?" "A a sai kin fad'a" "A lokacin da na kashe wayar naga kiranta ya fara shigowa na kashe , bayan Nan kusan thirty minutes sai na hango ta tsaya tana kallon mu sai ta juya ta tafi" Wata irin shu'umin dariya Mardiya Tace "That's my girl idan kina haka Zaki Shiga tsakanin su a saukake ba tare da sun gane ba" "Hmm ke dai bari zan so da Kinga fuskar ta d'azu Amma Anya Qawata yarinyar Nan ba son shi take ba kuwa?" "Haba ke kuwa ya za'ayi ta so shi bayan d'an uwan tane?" "Ina ta tunanin hakan Amma zan Kara tambayar sa nayi don ina tunanin na uwa d'aya uba d'aya suke ba, babu yanda za'ayi suna uwa d'aya uba d'aya su shaku har haka" "Da wannan ma to ki kirashi Mana tunda kuka rabu kunyi waya kuwa?" "A a 'bata min Rai yayi Kinga wani saurin da yake ya barni a gun kamar wata wawayi yasa aka tsaya kallona" "Fushi fa ba naki bane ki kirashi kawai, don na tabbata tana fushi dashi Kinga kin samu damar waya dashi ko ba komai zaiji dad'i" "Wannan hakane, bari na kirashi" Sai da safe sukayi wa junan su, Aysha wanka ta Shiga abinta Akan in ta fito tazo kwanciya sai ta kirashi. Haisam har karfe goma ya kasa bacci sai juyi yake , Yana ta jiran Kiran Ma'isha Amma Bata kirasa ba a bayyane yace "wato ma baza ta iya Kirana ba ta bani hakuri bayan tasan tamin laifi" Yar karamar tsaki yayi ya d'auki wayar sa ya Shiga kiran Aysha, fitowar ta Kenan daga wanka jikinta sanye yake da bath robe, Murmushi tayi Tace "Alhamdulillah" Picking tayi cikin sanyin Murya ta Masa sallama ajiyar zuciya yayi ya amsa kana ya Shiga Bata hakuri Akan tafiyar da yayi ba tare da yayi Mata sallama ba, ta nuna Masa ba damuwa. Nan tayi ta jaan shi da Hira har ya manta da Yana cikin 'bacin rai, suna cikin wayar ne yaji shigowar wani Kiran dubawa yayi Yana ganin sunan *Princess* yayi Yar karamar tsaki. Aysha Tace "Lafiya kuwa ya da tsaki?" Yace "Wani ne yake ta damina da call" "To ka d'aga Mana" "Kar ki da mu it's not important, Uhmn kina bani labari" Yar karamar dariya tayi Tace "Yauwa bayan na gama......" Nan ta cigaba da bashi labarin shimen ta shi Kuma ya biye mata, har wayar ya Kai awa d'aya yanke ya Kuma kiranta suka cigaba da hirar su, Ma'isha Kuma ta Kira yafi sau ashrin idan taji yana waya sai ta katse, har karfe Sha biyu na dare suke waya jin ta Fara hamma ya mata sai da safe ya katse wayar missed call 57 na Ma'isha ya gani da message guda d'aya _"Yaya Dan Allah kayi hakuri, na yi ta jiran ka baka Zo ba Kuma wayar ka akashe bayan naje neman ka Kuma naga Kuna Tutorial da Aysha shiysa na dawo gida don kar na katse ku am sorry please"_ Bayan ya gama karantawa tsaki yayi ya ma kashe wayar Baki d'aya ya yi baccin sa, Ma'isha ta sake Kira taji switch off kukane Mai karfi ya kwace mata tana fad'in "Shikenan Shikenan dama na San Yaya ba so na yake ba ni kad'ai ce nake hauka na, insha Allah daga yanzu na cirewa kaina soyayyar ka" Kasa bacci tayi yanda taga rana haka taga dare, idan tayi kukan ta gajie sai tayi shiru tana tuna abinda ya mata Kuma sai ta fashe da kuka a Haka har gari ya Waye, tana Jin an Kira sallar asuba ta Mike tayi wanka sannan tayi alwala, bayan ta idar da sallah ta nufi kitchen breakfast ta d'aura bayan ta Gama ta dawo d'akin ta ta Fara Shirin school. Bayan ta gama ta d'auki Jakarta ta fice daga d'akin, dinning ta nufa ta tarar da su Mummy da Daddy na karyawa cikin girmamawa ta gaishe su suka amsa. Ta sa wa kanta abincin ta hau ci bayan ta gama ci ta musu sai ta dawo, tayi ficewar ta Mummy da Daddy kallon junan su sukayi yace "Haryanzu fa Basu shirya ba" Mummy Tace "zasu shirya don na tabbata yana waje yana jiranta" Haka kuwa akayi tana fita ta hangosa a mota Yana jiran ta, Kuma waya yake hankalinsa kwance da kamar baza ta Shiga ba sai Kuma ta fasa ta bud'e gaban motar ta Shiga Kallo d'aya ya Mata ya cigaba da wayar sa. Ya d'auki tsawon minti uku Yana waya kamun Nan yace "karfe nawa Zaki Shigo?" Daga d'ayan 'bangaren ta ce "Karfe 4,kaifa?" "Ni bani ma da Lectures yau" Cikin wani irin murya Tace "Yau bazan ganka ba Kenan?" " Me zai hana idan kina son gani na zaki ganni, Kuma kinsan Dole na Kai princess makaranta" "Albarkacin ta zanci Kenan" "Umm umm ko don ke zan Shigo ai idan kin bukaci hakan" Murmushi tayi Tace "Nagode Amma yallab'ai uwa d'aya uba d'aya kuke da ita ko naga Kuna Kama?" "A a Yar Baffana ne" "oh Masha Allah ka gaida min ita sai na Shigo d'in" " Okay bye" Ma'isha tana Jin su kamar zuciyar ta zata fashe Amma tayi kokoran saita kanta, ganin ya tada motar Tace "Ina kwana?" Ya amsa da "lafiya" kawai yace mata a takaice, yasa wa motar key suka wuce makaranta. _______________________ Please comment and share Milhat ce Yar tarewa _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76