Chapter 6
Chapter 6
Mai tsawo. Tunda suka Shiga cikin gidan Haisam Sai kallon gun yake baki a bud'e a haka har Daddy ya gama nuna masa, daga karshe ya kaisa wani d'aki Wanda makeken Italian bed Ne a ciki,da wall drop Shima kalan gadon sannan da sofa masu kyau guda uku,'daya three sitter sauran biyun Kuma 1 1 sitter ne. Yace "Haisam wannan ne d'akin ka" Haisam durkusawa yayi Yana kuka Mai sauti yanayiwa Daddy godiya,da kyar daddy yasa shi ya Mike ya umurce sa da yayi wanka ya huta Kan su Mummy su dawo yayi ficewar sa. Haisam ya dad'e Yana zaune Yana mamakin abubuwan da daddy yayi musu,Ashe dama akwai mutanen kirki a Duniya, da wannan tunanin ya Shiga wanka,bayan ya fito ne yayi sallar la'asar dake suna shagon sayan wayar akayi sallar la'asar,bayan ya idar da sallar ne ya hau Kan gado ya kwanta,tunanin sabowar rayuwar da ya shiga yake a haka har bacci Mai nauyi ya d'auke Shi. Daddy ma wankan yayi bayan Nan yayi sallah ya kwanta Shima ya hau baccin sa Mai dadi. 'bangaren su mummy kuwa San Hussain suka Shiga zannuwa masu tsada da dogayen riguna,mayuka,gyalalluka takalmomi da jakkakuna baza su irgu ba, ta loda wa Umma,Umma kuka ta Shiga yi. Matsowa mummy tayi daf da ita tace "Haba Hajiya Fatima kisani fa muna cikin mutane,Zaki sa ayi ta kallon mu" Ma'isha ta miko Mata handkacif had'e da fad'in " kiyi hakuri Umma ki daina kuka" Murmushi tayi Tace "Na daina Ma'isha" Bayan sun gama sayyayan duk abui da zasu Saya suka nufi saloon,Umma rabonta da zuwa saloon tun Abban Haisam na Raye,wani irin iska Mai dadi take ji Yana Shiga kanta duk da kusan kullum saita wanke,Amma wankewan Kai a saloon Daban yake da wanda zakayi a gida. Bayan sun gama da saloon suka nufi gida suna Shiga Ana Kiran sallar magrib,a dai dai Nan daddy ya fito da alwalar sa,ya hango motar su tana parking girgiza kai kawaii yayi ya tsaya kallon su. Ma'isha na fita daga motar taje ta Kira Haisam su Shiga masallaci,da saurin ta,ta nufi part d'in da Haisam yake hannun ta dauke fa ledodi,a parlor ta ajiye su ta nufi d'akin sa,dake da ita aka gyara d'akin shiyasa tasan d'akin sa. Tana sa hannu taji kofar a bud'e take,lekawar da zatayi ta hangosa a Kan katafaren gadon sa yana sharban baccin sa hankali kwance. _________________________ Please share and comments Milhaat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 9 and 10 Shiga d'akin tayi ta tsaya kallon sa, Haisam a baccin sa yake ji kamar akwai mutum a Kan sa, a hankali yake bud'e idanun sa har ya sauke su Akan ta, Murmushi yayi cikin muryar bacci yace "Ya dai malama? Kin wani sani a gaba kina ta kallo na am in safe?" Murmushi tayi Tace "Of course you are safe, Daddy ne yace na Kira ka ku tafi Masallaci" "Daddy ne yace na Kira ka ku tafi Masallaci" ya fad'in hakan ne Yana kwaikwayon muryar ta ya daura da fad'in "Kuma kika tsaya kallo na ko?" Cikin muryar shagwa'ba Tace "Yaya shine kake kwaikwayata ni dai ba haka muryata take ba." Mikewa yayi ya nufi hanyar ban d'aki ya waigo ya kalle ta kyaji dashi" ya shige ban d'aki a gaggauce yayi alwala ya fito ganin Ma'isha na tsaye a inda ya barta ya sashi Kama Baki, kallon ta yayi cike da mamaki yace "Wai ke dama baki tafi ba? Ko so kike sai kin sani a gaba tukkunna?" Kai ta d'aga Masa alamun eh, girgiza kai yayi yace to muje Yana gaba tana biye dashi. Daddy na hango su yace "kaji yaran Nan har na ma manta na aiketa" Suna karasowa inda yake yace "Daughter ke kuwa daga aika ai ki zauna Sai kace an aiki baiwa gidan su?" Yar karamar dariya tayi Tace "Daddy ai Yaya ne, yake ta bacci dakyar na tashe shi" Haisam yace "Ji Dan Allah ko kunyar karya ma ba kyaji bayan...... " Daddy ne ya yanke Masa zancen yace "Ya Isa ya Isa, yanzu sai ka wuce muje Masallaci idan muka dawo sai ku cigaba da musun naku, kema ki wuce kije kiyi sallah" Ta amsa da "To daddy sai Kun dawo a Mana addu'a" Ya amsa da to ba tare da ya waigo ba,cikin gida ta wuce su Kuma suka wuce Massallaci" A parlor ta tarar da Mummy da Umma, mummy na ganin ta tace "daga zuwa aika Ma'isha sai ki zauna abunki?" "mummy ya Haisam ne da surutun sa" "Da surutun ku dai, ina sauran kayan Nan kike ajiye su?" " Yana part d'in su Umma, na d'auko ne?" "A a bar su kawaii d'auki wannan d'in ki Kai su Chan" Ta amsa da to had'e da d'aukan sauran kayan ta wuce dasu part d'in su Haisam, Umma ta rufa Mata baya. A chan Ma'isha tayi sallar maghrib da Isha, Haisam da daddy tunda suka fita basu dawo ba har Sai da aka yi Isha suka dawo gida. Mummy na ganin su Tace "Alhamdulillah to ba komai nasan yanzu bani kad'ai bace a gidan" Murmushi daddy yayi ya ce "Toh me Kuma ya Faru rankishidad'e?" "Duk fita kuka yi kuka barni Mana ni kad'ai kamar mayya" "Ahh ina su Ma'ishan suke?" "Tunda nace ta Kai Mata Kaya shiru kake ji ba ta dawo ba" Yar karamar dariya yayi yace "Ai Ma'isha ta iya zuwa aika, Haisam je ka kirawo min ita" Ya Mike Kenan ya hango shigowar su yace "Daddy ai ga sunan ma sun shigo" ya koma ya zauna. Girgiza Kai yayi yace "Wato shine kuka bar min Mata ita kadai ko?" Murmushi Ma'isha tayi Tace "Daddy wallahi Hira muke tayi muna kallon zee world bamu San lokaci ya tafi har Haka ba" "To kun kyauta, Hajiya yunwa fa nake ji" Mummy mikewa tayi Tace "Muje Dining dama dazu na kirb'a sakwara na sa a food flask" " Yauwa Yar Albarka na" ya Maida kallon sa ga Haisam yace "Son muje ko?" Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya bi bayan sa, Ma'isha hannun Umma ta rike tace "Umma muje" Mummy Tace "Shikenan nikuma an yaye ni ko?" Dariya kawai sukayi suka nufi dinning suna cin abinci suna hira har suka gama, bayan sun gama ci Haisam yayi musu Sai da safe ya koma part d'in su, Umma da Mummy da Ma'isha a parlor suka zauna suna Hira a yayin da daddy ya shiga bed room dinsa, sun dad'e suna Hira har karfe 10 ta wuce Umma sai hamma take cikin muryar bacci Tace "Ni ina gani zan wuce bacci nake ji sosai ga gajiyar da muka kwaasa d'azu" Yar karamar dariya mummy tayi tace "Ni kaina baccin Nan nake ji muje na d'an taka Miki" "To Shikenan"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76