Chapter 13
Chapter 13
lot already dama driver yasan da fitan su yana hango su ya fito da motar a baya suka zauna, ya Danna wa motar key suka wuce saloon. Haisam da Ma'isha suna zaune a dinning tana cin abinci shi Kuma sai tad'i yake ta mata tana ci tana dariya har kamar zata kware,kwasam wayaey sa ta fara ringing hannu yasa a aljihun rigar sa ya zaro wayan ganin sabon number yasa bai d'auka ba, sai da aka sake Kira a karo na biyu yayi picking sallama yaji jin Muryar mace ya sa shi tunanin Wace ce wannan da zakin Muryar da bai tab'a jin irin ta ba, a ransa yake ayyana hakan, ta sake sallama a karo na biyu ya amsa bayan sun gaisa daga d'ayan 'bangaren Tace "Ka gane mai magana kuwa?" Yace "A'a " a takaice. Murmushi tayi Wanda Yana iya jinsa Tace "Nice na karb'i number ka d'azu a Cafeteria d'azu, ka tuna" Yace "Eh na tuna, ya kike? " Tace "Lafiya, idan baza ka damu ba Dan In na so muyi wata magana dakai idan baka komai?" " For now am busy gaskiya sai zuwa anjima when am less busy I'll call you" Tace "promise?" " Yeah Insha Allah" "Okay sai na jika" Kiit ya katse wayar, tunda ya fara wayan hankalin Ma'isha yake kansa Tace "Yaya who is that?" Yace "A friend" Tace "Okay" Yace "Yau ina Baki Labari........ " Nan suka cigaba da hirar su Saida ta cita koshi suka koma parlor suna kallon favorite series d'insu a zeeworld Mai sun I Do. ___________________________ Ina barar addu'ar ku fansa ina cikin wani yanayin da yake hanani komai hatta typing ma shiyasa kuka jini shiru. Please Comment Share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 17and 18 Haisam da Ma'isha kallo suke hankali kwance har Saida aka Fara kiraye kirayen sallar maghriba, mikewa yayi ya kashe TV turo baki tayi Tace "Yaya meyasa zaka kashe min Kallo na?" "Lokacin sallah yayi baki ji ana Kiran sallah ne?" "To ai Ni bana sal...... " Sai kuma tayi shiru ta kasa karasa maganar dariya yaso yi sai Kuma ya matse yace "karasa abinda zakice bakya me?" Mikewa tayi da sauri ta nufi d'akin ta tana dariya kasa kasa,dariya yayi ya kad'a Kai yasa Kai zai fita knn sai ga shigowar su Mummy, d'an Jaa da baya yayi ya basu wuri suka wuce Yana fad'in "Har kun dawo?" Umma Tace "harne? Bayan munfi 2hours" Yace "Naga kunyi sauri ne ai" Mummy Tace "Son ana Kiran sallah kana Nan kuna ta aikin surutu ko?" Murmushi yayi Yana Jin dad'in yanda mummy ke nuna kulawa a garesa tamkar ita ta haife shi yace "Yanzu Masallacin nayi" Tace "To a dawo lafiya" Ya amsa da "Ameen" Sai yayi ficewar sa. Ma'isha na shiga d'aki ta kwana abinta ta d'auki wayarta tana chatting da kawayen ta, Bata fito parlor ba har sai da ta ji shigowar Daddy, da gudu ta fito tana Masa sannu dazuwa. Daddy yace "Daughter baki san kin girma bako, ya kamata ki rage Shagwab'ar nan Haka" Haisam yace "Daddy ai saima abinda ya karu, Mijin ta zai Sha wahala sosai don na tabbata ko da bayan ta haihuwane Reno biyu zaiyi" A zuciyar Tace "Zaka Sha Reno dai, don kaine mijin nawa Insha Allah" a bayyane Kuma Tace "Uhmnn daddy kace Masa ya daina tsokana ta" har da bubbuga kafar ta kamar yarinya Yar shekara biyar daddy yace "Son ka daina tsokanar ta" Haisam dariya kawai yayi baice komai ba, mummy ce ta Shigo parlor taci kwalliya sai zuba kamshi take Tace "Daga dawowar sa kun sashi a gaba da shirmen ku babu Wanda yayi tunanin karb'ae jakar sa" Ma'isha saurin karb'an jakar hannun da tayi tace "Laa sorry daddy wallahi farin cikin ganin sa ne yasa na manta" Haisam yace "Hakane mummy 2 weeks fa dad baya Nan Dole muyi kewar sa" "Naji yanzu dai ku bari idan yaci abinci ya samu ya huta sai kuyi hirar taku" A tare sukace toh. Karb'an jakar hannun Ma'isha tayi, Ma'isha Tace "Mummy ki bari Mana na kai Masa d'akin sa" "Anki d'in mijinkine ko mijina?" Ma'isha hannu tasa ta rufe bakin ta Tace "mummy abin harda gorine Kuma?" Hararar ta mummy tayi ta bi bayan Daddy da tun d'azu ta wuce d'akin sa. Zama Ma'isha tayi a Kan couch d'in dake gefen na Haisam bakin sa ya kawo dai dai kunnen ta yace "kinji abinda mummy Tace ko dama maza ki Nemo miji in yi miki aure idan bakya son Gori" Dariya tayi Tace "Na baka huka da nama yaya ka Nemo min mijin aure na maka alkawarin ko wane ne ka kawo zan aure shi" "kamar dagaske, confidence d'inki dariya yake bani wallahi kina nufin ko Mai gadi na kawo miki zaki aura? " "Da gudu ma, ai Mai gadi mutum ne kamar kowa ko?" "Shikenan tunda kince haka Zaki Sha mamaki." Dariya kawai tayi suka cigaba da kallo. Umma ce ta Shigo parlor Tace "Kun samu sana'a ku Kam, a haka za'a samu likitocin?" Haisam yace "Ai gobe ba school ne Umma Sunday ne fa ranar hutun d'an boko" " Gafara Chan ka zauna kana kallon zeeworld kamar wata mace" "Wallahi umma ba laifina bane, laifin Yar kice itace ta koya min Kallo" "nasan abinda zakace Kenan ai" wuri ta Samu ta zauna suna kallon tare. Daddy ne da mummy suka fito baka Jin abinda suke cewa Sai dariyar su kawai, Haisam kasa kasa yace "Kin gani ko princess kiyi aure ki Rika samun farin ciki abunki" "sai na fadawa Daddy abinda kace yanzu" "a a yi hakuri nayi shiru" Dinning suka nufa, Umma, Ma'isha da Haisam Suma suka wuce dinning d'in Tuwon shinkafa da miyar kuka mummy tayi yaji daddawa da citta sai nama da kifi da suke ta shawagi a ciki, suna ci suna Hira har suka gama suna gamawa Haisam ya Mike yace "Yau bacci nake ji sosai zan kwanta" Ma'isha a take ta 'bata Rai Tace "Yaya but kace min zamuyi Kallo tare fa" "Am sorry Kanwata wallahi a gajiye nake akwai gobe wuni zamuyi muna Hira kinji?" Bata so hakan ba Dole ce tasa ta hakura yayiwa su mummy sai da safe ya wuce part d'insu Yana tafiya Ma'isha itama tashi ta shige d'akin ta. Haisam na shiga d'aki ya ban d'aki ya fad'a yayi wanka ya sanya vest da d'an gajeren wandon sa ya d'ale Kan gado ya bud'e datar sa ya Fara chatting, emoji da stickers na kuka ya Fara cin karo dasu Ma'isha ta jero Masa dama yasan za'a Rina Nan ya shiga rarrashin ta suna cikin chat d'in ne bakuwar number ta kirasa. Yana picking Tace "Haba yallab'ai kasa ina ta jiran ka, nan ne ma ya tuna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76