Chapter 29
Chapter 29
"Shut up!!! Amma me? Nace amme? Akan me Zaki zauna kisa yaran Nan a gaba kina fad'a musu abinda bai shafe su ba iyee? Answer me?" Mummy kasa magana tai ta sunkuyar da kanta a kasa tana kuka Mai cin Rai Duk yanda taso ta Hana kukan ta ta kasa sabida yanda daddy ya ke mata tsawa da fad'a a gaban yara, da su ya sune abun Sam bazai Dame ta ba. Ma'isha Murya na rawa Tace "Daddy please Daddy kayi hakuri wallahi ba laifin mummy bane mune muka sata a gaba Dole tasa ta fad'a Mana, Kuma....... " "Ma'isha!!! Ya Kira sunan ta a wani irin Murya Wanda hakan yasa ta rike bakin ta da hannun ba tare da tasan tayi hakan ba, ba tare da ya kalleta ba yace "Idan na Kuma Jin bakin ki a wurin Nan sai na 'ballaki" Ya cigaba da fad'in "Taya za'a yi ni da gida in kafa doka Amma ki take shi? Yaushe Kika Zama Haka Maryam?" Haisam cikin girmawa yace " Daddy please kayi hakuri Dan Allah Ni a gani na wannan abun ba abin tada hankali bane ba, yes kamar yadda princess Tace mune muka Masa wa Mummy Akan ta fad'a maana abinda ya faru sabida d'azu a gabana naga kana Mata fad'a, abinda ban tab'a gani ba Kennan tunda na dawo gidan, ta fad'a min ne sabida tasan Idan nayi wa Umma magana zata amince, sannan Abba nasan Idan hakan ta kasance zaka fi kowa farin ciki, Amma Dan Allah kayi hakuri" Shiru Daddy Yana sauraron sa jikin sa Duk yayi sanyi, tabbas maganar Haisam hakane zaifi kowa farin ciki sannan idan Haisam yayi wa Umma magana babu Makawa zata amince, shiru d'akin yayi na d'an wasu lokuta Banda kukan mummy da na Ma'isha babu abinda ke tashi a d'akin jiki a sanyaye Daddy ya nufi inda Mummy me tsaye tana matsar kwalla, bai tsaya 'bata lokaci ba ku Jin kunyar su Haisam ba ya rungume ta Sam a jikin sa Yana d'an bubbuga Bayan ta a hankali, yace "Am sorry Maryam, am sorry please wallahi raina ne ya 'baci jin kalaman Zainab a Jan d'an uwana Sai na kasa jurewa yanda na ga ta ki Abdallah karara naji zafi sosai da kalaman ta, Amma bani da ikon da ita bazan iya tirsasata ba, na d'au lokaci Mai tsawo na ganin irin wannan ranar da Abdallah zai kawo min maganar aure, nayi matukar murna sosai Allah Allah nake na dawo gida don Jin labari Mai dad'i sai Kuma najie akasin hakan, ke Kuma da na hanaki magana akai sai Kuma Kika ki jin magana Amma maganar da Son yayi sai na gane kuskure na" d'an d'ago Kan Mummy yayi yasa hannu Yana goge mata hawaye yana fad'in "am sorry am sorry" Haisam d'an Buge kafar Isha yayi da kafar sa ta juyo ta kalle sa murya kasa kasa yace "Kinga ko mijin ta ya rarrashe ta,Yana share Mata hawaye ta daina kukan, gwamma kiyi shiru don ba Mai rarrashin ki anan" 'dan Buge shi tayi da kafan ta yana gumse dariyar da ke kokarin kwace Masa. Mummy zare jikin ta tayi a hankali daga jikin daddy tasa Bayan hannun ta, ta share hawayen ta kana ta gyara murya Tace "Son kaci gidan ku" Kama baki yayi yace "Laaaa Ashe ta ji" da gudu ya fita isha ta Mara Masa baya, Tace "Ja'irai kawai" suka bar daddy dashi da Matar Nan, suka Shiga soyewa abinsu. Haisam da Ma'isha kuwa a parlor suka zauna Banda dariya babu abinda suke yi, su Haisam harda rike ciki itama Isha dariya take sosai ba kakkautawa tana cikin dariyar ne kwasam ta Mike a zabure ta wuce d'akin ta da gudu, Haisam kuwa baki ya sake Yana kallon ta har ta haura d'akin ta sai da yaga ya daina kallonta kana ya kawar da kansa Yana mamakin Shagwab'a irinta Ma'isha , a bayyane yace "Mutum bata da aiki sai kuka" Ma'isha kuwa tana Shiga d'akin ta ta had'a kai da gwiwa ta fara rera kuka son ranta, tunawa tayi da Haisam na son wata ita ba, yanzu duk dakon soyayyar sa da ta dad'e tana yi ya tashi a banza Kenan? Karar shigowar Kira taji ya shigo wayar ta mikewa tayi ta duba fuskar wayar ta ganin sunan Meerah yasa ta daina kukan ta yi picking ba tare da Tace komai ba, Meerah Tace "Hy Isha kin koma gida kalau, da fatan kinsha maganin da muka saya d'azu?" "Nikam Na manta da wani magani" a ranta ta ayyana hakan Amma a bayyane Kuma Tace "Uhmmn Nasha" "Subhannallah Isha kuka kikayi yana ji muryar ki haka Lafiyan ki kuwa?" "Uhmn Lafiya na Lau daga bacci na tashi" "oh sorry na tashe dama so nake na ji ko kinsha maganin nakin gudun kar jinin naki ya sake Hawa" "Kar ki damu Nasha" "Tohm Shikenan zan Zo gobe Insha Allah na gwada BP naki ko ya sauka, da fatan baki da Lectures gobe?" "Akwai But da safe ne zuwa la'asar zan dawo" "alright sai mun had'u goben please take care" " Insha Allah thank you" a tare suka katse wayar d'ago kanta da tayi ta sauke kanta a Kan haisma da tun da ta Fara wayar Yana tsaye Yana kallon ta, Murmushi tayi Tace "Yaya ka Shigo Mana" Girgiza Kai yayi yace "Ba Zama ya kawo ni Nan ba, Princess meyasa ki kuka? Kuma ke da wa kike waya naji kina maganar kinsha? Me ke damin ki baki da lafiyane?" Yar karamar dariya tayi Tace "Yaya irin wannan tambaya haka wanne zan amsa a ciki?" "Dukka" ganin ba wasa a fuskar sa Tace "Uhmn dama kaina ne yake ciwo" "Uhmn sai akayi Yaya? Da wa kike waya?" "Ameerah ce dama da naje gidan su ne, saai.... Umm kaina ya Fara ciwo shine ta bani magani Nasha Akan in na dawo na Sha, shine ta Kira taji ko Nasha" "Toh naji shi Kuma kukan na mene ne?" "umm... Ummm..... Kai na.... Kaina ne yake ciwo" "Ciwon Kan ne ya saki kuka?" Kai a kasa ta amsa da "Eh shine" ganin ya kure Idanun sa yana kallon ta Yana kokarin gaskata maganar da. "Ya ciwon Kan, kin Sha maganin?" "Eh Nasha" " Alright, sai ki samu ki kwanta kar na Dame ki, good night" ya jaa kofar ya rufe Mata bai tsaya Jin abinda zata ce ba. Ajiyar zuciya tayi Tace "That was closed I thought yaji" girgiza Kai tayi ,ta Shiga ban d'aki ta yi wanka tana fitowa ta Sanya sleeping dress d'inta ta kwanta sannan ta kunna datarta, ta Shiga WhatsApp, ganin Haisam a online yasa ta Masa "Hy Yaya ba kayi bacci ba?" Sai da ya d'auki kusan 5 minutes kana ya mata reply da "Eh banyi ba me ya hanaki bacci?" Emoji na kuka ta jero masa had'e da tura masa "Sai yanzu Zaka kulani?" "am sorry Video call muke da auntyn ki" Tana bud'e wa ta kashe datar ba tare da ta Masa reply ba, ta gyara kwanciyar ta tana ta tuna abubuwa dayawa daga bisani bacci yayi awon gaba da ita. ```Washe Gari``` Haisam ne ya Shigo ya tarar da mummy da Daddy a parlor suna karyawa gaishe su yayi suka amsa kana ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76