Chapter 47
Chapter 47
dalilin ki ba Haka baza mu iya yafe miki ba" riko hannun Isha tayi da niyar barin d'akin har sun Isa kofar fita, Ma'aruf yace "Isha please " a hankali suka juyo suna kallon sa, ya karasa inda suke yana matsar kwalla yace "Nasan an zalin ce ku, har abada abinda kuka rasa baza su Dawo ba, Dan Allah ina rokon ku, ku yafe mata on my behalf, and please Isha Kar abinda Kanwata ta aikata a gare ki ya sa ki janye maganar aurena dake" Murmushin gefen baki tayi kana Tace "It can never happened" Cikin rashin fahimta a d'an kid'ime yace "What? Isha please Kar kice baza ki aure ni ba Dan Allah" Girgiza Kai kawai tayi ta fice Meerah na ta bi Bayan ta yana Kiran sunan su basu juyo ba bare su saurare shi ya dad'e a tsaye a gun ya rasa abinda ke Masa dad'i d'akin shiru yayi Banda sautin kukan Mardiya babu abinda kake iya ji a parlorn, cike da takaici ya kalle ta Kiran sunan ta yayi da d'an karfi "Mardiya!!! A d'an razane ta d'ago kanta had'e da mikewa jikin ta na kyarma cikin rawar murya Tace "Na...naaa..... Na'am Yaya" Cike da takaici ciza leb'en sa yayi yace "Are you happy now? Kinji dad'i ko? A dalilin ki na rasa masoyiyata" "Wallahi yaya ban sani ba, ban San itace wacce kake so ka aure ba da ban....... " A tsawce ya katse yace "Da bakiyi me ba? Oh sai kin San cewar zan aure ta ne tukkunna kisan abinda ya kamata? Who gave you the right to mingle in someone's life? Me suka miki? Nace me suka Miki?" Ya karasa maganar cikin tsawa har Saida ta razana ta jaa da baya a tsorace cikin Muryar kuka Tace "Yaya please" daka mata tsawa yayi ya nuna ta da 'dan yasa yace "This will be the last day da zaki sake kirana da wannan sunan Ni ba Yayan ki bane, daga yanzu na yanke ki daga jikina" ya Kama hanyar fita da gudu ta karasa inda yake ta rike kafafun sa tana kuka had'e da bashi hakuri, hankad'e ta yayi da kafar sa ta buge bakin ta a Kan tiles d'in dake gun Nan da nan bakinta ya Kumbura ganin ya fice ta bi Bayan sa cikin sauri. Wurin motar sa ya nufa ya shige ganin tasa hannu ta bud'e motar zata Shiga a tsawace yace "Kul Kar ki soma Wallahi Kika kuskura Kika Shiga min mota sai na karya ki kinji na gaya miki" marfin motar ta rike ta sandare tana kallon sa tsaki yayi ya sa hannu ya ja marfin motar sa da karfin gaske ya rufe ya had'a da yatsanta , wani Kara ta saka har da ya tsorata, da sauri ya fice daga motan, hannun ta ya cire ya na mata sannu had'e da hura mata hannun (Nace Allah sarki jini kennan duk da yana fushi da ita amma ya damu da lafiyar ta) yana tuna abinda tayi ya ture ta had'e da rufe marfin motar sa ya zaga ya shige ya sa wa motar key Mai gadi ya wangale Masa gate,Mai gadi yana masa sannu da fitowa Amma bai kalle sa ba bare ya amsa,ficewar sa kawai yayi. Mai gadi girgiza kai yayi had'e da fad'in "Anya Lafiya kuwa?" Sai ya hango Mardiya a tsaye tana kuka ta rike hannu ta tana kallon raunin da Yayan ta ya ji mata, da sauri ya karasa inda take yana mata sannu ganin jinin da yake zuba a hannun ta, yana mata magana bata kulashi, hanyar fita tayi Yana kallon ta har ta fice, tab'e baki yayi had'e da fad'in "Tooooh Allah shi kyauta." Da sallam ya shigo parlor kallon da take Masa ne yace "Mama Lafiya kuwa kike min irin wannan kallon?" Ma'aruf keyiwa mahaifiyar sa Wannan tambayar. "Ina fa Lafiya ina ka baro min yarinya, Kun fita tare Kuma ka Dawo kai kadai" Shiru yayi a zuciyar Kuma yace "Kash Ma'aruf ka kwafsa kasan Dole sai an tambaye ka inda take" a karo na biyi ta Kuma cewa "Ina magana kayi Shiru Ina take?" "Umm... Ummm" Muryar ta ya jiyo a ta Bayan sa tana fad'in "Gani Nan Mama" "mtsww dama kuna tare Kuma shine ina tambayar ka kayir Min shiru" Shiru yayi baice mata komai ba, mardiya inda Mama take ta nufa ta zauna a gefen ta, idon Mama ne ya sauka a hannun ta da yayi jajir jini yana d'an sauka a hankali cikin tashin hankali Tace "Subhannallah Auta me ya same ki?" "Mama na....." Charafff ma'aruf ya kase ta da fad'in "Wurin rashin hankalin ta man, ta datse hannun ta a marfin mota" Hannun ta rike tana mata sannu Tace "Amma shine Kuka Dawo gida baka kaita asibiti ba? Haryanzu fa jini yana zuba" Yace "itace fa, Babu yanda banyi da ita ba muje Taki wai in muka dawo gida zata sha magani shiyasa na kyale ta" Mardiya kallon sa tayi cike da mamakin karyar da yake,ganin tana kallon sane hakan yasa ya mata wani irin muguwar Kallo,da sauri ta kawar da kanta. "idan ita bata da hankali kaima baka dashi Kenan? Maza ka d'auke ta kuje asibiti" Ba don yaso ba ta fita tabi Bayan sa, ta tarar ya Shiga mota har ya tada ta, ta bud'e gidan baya zata zauna a tsawace yace "Ni d'in driver kine da Zaki zauna a baya don gidan ku?" Jiki na rawa ta Dawo gaba, tana zama Bai jira ta rufe kofar ba ya fizgi motar, Mai gadin gidan nasu ya bud'e musu gate suka fice, babu Wanda yayi wa d'an uwan sa magana har suka Isa wani clinic tare suka Shiga yasa aka wanke mata had'e da sa bandage, ya biya sa hakkin sa kana suka fice. "a gaskiya Isha wannan shawarar da Kika yanke bata yi min ba Sam" Meerah kewa Isha Wannan maganar. Isha kallon ta tayi da kamar baza ta tanka mata ba sai Kuma tace "Koh?" Meerah ta amsa da "Kwaraai ma kuwa" "To ni yamin" "Uhmn Isha Kenan, ya kamata ki gane wani abu Mardiya daban haka ma Ma'aruf daban, so please kar laifin wani ya shafi wani please" "Dole ya shafe shi sabida kanwarsa ce, Akan me zan zauna da irin Wannan mutanen sai su kashe ni ai" "Babu Wanda zai kashe ki Isha, sanin Kanki ne Ma'aruf mutumin kirkii ne, shikan sa baiji dad'in abinda tayi ba please ki bar maganar nan iya mu Dan Allah" Kallon ta tayi kana ta girgiza Kai tace "Da ce miki nayi zan kai maganar wani gun?" "To what's the difference Tunda Kince kin fasa auren sa, idan Kika fad'awa daddy dole sai kin Sanar Masa da dalili Kinga Kenan bak tsaya a iya Nan ba" "Uhmn Wai yaushe nace miki bazan aure shi ba? Kawai dai naji kamar na fasa ne" "To Dan Allah Kar ki ji kin fasa,Wallahi mutumin kirkine Kuma yana sonki" "To naji,ke dama ai bakya son laifin sa" "A'a gaskiya dai na ke fad'a idan yayi laifi Kam Dole a hukunta shi" "Meerah sarauniyar dad'in baki" "No kema kin san ni ai gaskiya nake fad'a miki" "To naji mubar zancen please kaina har wani sarawa yake" " Dole ai ni
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76