Chapter 36
Chapter 36
kike " "Aaaa haba Mummy nida Isha ai Mun Zama d'aya nima idan hakan ta same ni nasan zata min fiye da hakan,fatan mu shine Allah ya bata lafiya" "hakane Allah ya bar zumunci" "Ameen Mummy" "Please kiyi Mata magana ta fad'a miki abinda ke damin ta, Kuma taki cin abinci, rabonta da abinci tun jiya da dare" "Kar ki damu mummy zataci insha Allah" Mummy fita tayi ta barsu da ga ita sai Isha, plate da d'auka tasa abincin d'an dai dai ta ajiye Sannan ta zaunar da ita ta Shiga bata a baki ba musu ta karb'a. Cike da kulawa Tace "Haba Isha, Isha so kike ki kashe Kanki?wannan fa ba alkawarin da Kika d'aukan min ba Kennan, kin zabi ki mutu Kennan?" "uhmn zan mutu idan kwana na ya kare,kema kin San da hakan ko?" "Amma kuka ai gangancin kine zai saka ki rasa ran naki tun kwanakin ki bai kare ba, wallahi Isha na gaji da ganin ki a Haka, a gaskiya lokaci yayi da zan fad'a Masa da dasu mummy" "Meerah please ki tuna alkawarin, Duk Wanda ya karya alkawarin to ba Makawa alkawari zata cishi, kin fiso a rasa rayuka biyu ne?" "Ban gane a rasa Rayuwa biyu ba, wa Dawa Kenan?" " Ni da Ya Haisam, wallahi farin cikinsa matters allot to me, bazan juri ganin sa a cikin damuwa ba, moreover ba Sona yake ba" "Shima Kuma bazai tab'a jin dad'in abinda kike Shirin aikatawa ba, ko da ace baya sonki na tabbata zai so ki Nan gaba" Maganar Meerah a kunnen Haisam ya sauka, turo kofan yayi ya shigo gaisawa sukayi kana Meerah ta Mike Tace "Zan wuce asibiti dama nazo na duba jikin nakin ne, sai gobe zan dawo insha Allah, Allah ya baki Lafiya" Suka amsa da ameen tayi ficewar ta, tana fita ta nufi gun motar ta Muryar Haisam taji yana kiranta a hankali ta juya tana jiran sa. Karasowa yayi yace "Meerah wane ne Wanda Ma'isha take so?" In a serious tone yake tambayar ta, mamaki ma ya bata don ita ta manta ranar da ya Kira Ma'isha da sunan ta in bata manta ba tun suna school, ajiyar zuciya tayi Tace "like I said to you ban sani ba ni kaina taki ta fad'a min, sai anjima Kar na makara" ta shige motar ta har ta fice daga gidan Haisam na tsaye yana nazarin maganar ta a bayyane yace "Dole na sanarwa su Mummy sabida jinin ta sake Hawa yake Yi" Ya shige ciki ai kuwa Yana shiga har d'akin mummy yayi zama yayi ya Sanar mata da halin da Ma'isha Ke ciki tace "yanzu Isha dama akan na miji ne ta kamu da ciwon zuciya?" "Wallahi mummy Ni kaina abin mamaki yake bani" Daddy ne ya shigo Zama yayi Bayan sun gaisa ta Sanar mishi da halin da Isha take ciki Murmushi irin tasu ta manya yayi yace "Habae biri yayi kama da mutum, Dole mu nema Mata farin ciki ta samu abinda take so, koma wane ne zan Nemo shi sanan Nan da sati uku za a d'aura musu aure" "Haba alaji ko waye fa kace idan Kuma ba mutumin kirki bane fa?" "I trust my daughter baza ta tab'a son abinda bayi da kyau ba." Uhmnn kawai mummy Tace Haisam yace "am in full support Daddy Dole a nemo shi ko ina yake don wallahi idan bata Samu abinda take so ba zamu iya rasa ta" Daddy yace "Insha Allah, zan mata magana." Mummy ta ce "Amma ya kamata a bita a hankali gudun kar rashin Lafiyan nata ya kuma tashi ya kamata ace tana samun kulawa ne" "kar ki damu insha Allah zan San yanda zanyi ta fad'a min." Mikewa daddy yayi ya nufi d'akin ta babu yanda baiyi da ita ba ta fad'a masa Tace Masa "Babu wanda nake so Daddy." Matsa mata yayi Sosai daga bisani ta fashe da kuka daddy ransa a mugun 'bace ya bar d'akin. 'Dakin mummy ya nufa ya tarar haryanzu Mummy da Haisam maganar suke,hushi yake Yana fad'in "Taki ta fad'a min,ban san wani irin taurin kai Isha take da shi ba,tana chan tana kuka don kawai na bukaci ta fad'a Mana gaskiya" Mummy mikewa tayi Tace "Ka gani ko Alhaji,sai da fad'a maka mubi ta a hankali" tana kai Nan ta fice da sauri tayo d'akin Isha. Haisam shima mikewa yayi yace "Daddy kawarta fa tasan komai" Kallon sa yayi kana yace "Wacce kawarta Kenan?" "Daddy ai kawarta d'aya ce Ameerah,I over heard them suna maganar sa but na bita ta fad'a min Taki ta Sanar dani" "Ta kwana gidan sauki,Ni zan same ta da kaina kasan inda zamu same ta?" "Eh har gidan su na sani,Kuma Nurse d'in mu ce" "Shikenan idan Allah ya kai mu gobe sai muji" "Allah ya Kaiimu" sai ya fice. Mummy na Shiga d'akin Isha ta tarar da ita kuka take Sosai rungume ta tayi tana rarrashin ta amma Taki yin shiru, ganin Kamar numfashin ta na kokarin tsayawa ta shiga kwalla wa Haisam Kira, Haisam kuwa dama yazo fita ne yaji irin kiran za take masa, da gudu ya dawo ya Shiga d'akin, Daddy da sadiya suka shigo a tare. Duk kanta suka nufa Haisam kuwa Bayan ya duba ta d'akin sa ya Koma ta d'auko first aid box ya fara duba, Duk abubuwan da yakamata yayi Mata kana ya mata alluran bacci, mummy kuwa kuka take Sosai daddy na rarrashin ta, sadiya kuwa tausayin Ishan ce ya kamata sai matsar kwalla take, sabida Isha ta kasance tana kyautata Mata. Haisam ne yace "Mummy!! daddy!! Ya kamata mu bar ta ita kad'ai ta samu damar bacci, mummy Dan Allah ki daina kukan hakan Nan, Kar kema ki jaa wa kanki wata matsalar please." Hannun ta daddy ya rike suka fice daga d'akin,sadiya tafita, Haisam kuwa kallon ta ya tsayayi na d'an wasu lokuta kana ya fice daga d'akin. A hanyar sa ta fita ya jiyo Muryar Umma da Abba a parlor da sauri ya karasa Bayan ya gaida su ya Mika hannu ya d'auki kannen sa wata Aaima da Aymana, mummy dai haryanzu kukan take Umma hankalin ta tashi yayi ganin mummy a Haka, cikin Muryar kuka Tace "Dama jikin Daughter yayi tsanani har hakane? Nifa tun a asibiti da na ga har munyi Hira na d'auka taji sauki Sosai." Ajiyar zuciya daddy yayi ya Sanar Mata abinda yake damin ta dama sun 'boye Mata Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ciwon zuciya a d'an karamin shekarun Nan nata? Kuma akan na miji? Dan Allah wane ne shi? Ni zanje na durkusa har gaban sa ya aure ta" ta fashe da kuka, cikin Muryar kuka Mummy Tace "Bamu San shi ba, Taki fad'a mana Wanda take so" Daddy yace "Yanzu kukan da kuke me zai amfane mu dashi? Dan Allah da wanne zamuji?" Tsaki yayi ya fice daga gidan, Abba ma yabi Bayan sa, a garden suka zauna suna ta tattaunawa har Abba ya bukaci da a d'aga auren daddy yace "A a Abdul baza a d'aga auren Nan ba" "Amma Yaya ka duba halin da isha ke ciki, shi Karan kansa baya cikin hayyacin sa" "Uhmn bikin Nan fa saura 4 days, 4 days kawai me zamuce
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76