Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 71

Chapter 71

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

_______________ Toh fans me kuke ganin Adnan me zai bukata daga gare ta? Ina jiran amsoshin ku. Please comment and share fisabilillah. Milhaat Ce Yar Terawa 75&76 '''Continuation.........''' sai da ya Kai bakin kofa yasa hannu ya bud'e kofan kana ya waigo ya kalle ta, Murmushi yayi yace "Zaki Koma gida a matsayin Mata ta, idan kin amince ki same ni a d'akina, and kir ki wani damu da batun waliyi, Zanyi handling na komai" ya fice kana ya rufe Mata kofar , duk da ya fita Amma baki a bud'e take kallon kofan, tana mamakin karfin Hali irin nasa. Zama yayi yana jiran ta Amma shiru har bacci yayi awun gaba dashi, alarm d'insa ne ya buga na karfe 5 ,jaan wayar yayi ya kashe kana ya Shiga ban d'aki ya d'auro alwala ya tada sallah , Bayan ya idarne ya Koma baccin Sa. Ayrah kuwa kasa bacci tayi tana ta kuncewa da tsakawa ta rasa abinda zatayi, sai da taga wuri ya fara haske ta shige ban daki tayi alwala, Bayan ta idar da sallah, zaune take Akan prayer mat d'in haryanzu dai maganar Adnan ke Mata yawo a kwakwalwar ta, Bayan ta gama tsakawa da warware a bayyane Tace "Zan amince na aure ka, Amma da zaran na fita anan dole ne ka sake ki, in Kuma kaki kotuce zata rabani da Kai" Kofar d'akin sa ta nufa, ta kwankwasa kofar had'e da kusa Kai ciki, duk zaman ta a gidan bata tab'a zuwa d'akinsa ba, daga d'akin da take sai kitchen, baccin Sa taga yana yi, ta koma da niyar fita Muryar da taji yace "Ina Zaki?" Cikin Muryar bacci ya mata tambayar Nan. "Na d'auka bacci kake" "Umm yanzu na farka Shigo Mana" Kujeran dake gaban Mirror ta ja ta zauna a kusa dashi kana Tace "Nazo muyi magana ne" Zama yayi yana d'an goge idanun sa da yatsunsa kana yace "Ina jinki" Shiru tayi kanta a kasa kana Tace "Na'amince zan aure ka, Amma Dan Allah Kar ka cutar Dani" hawaye fal a idanun ta, hannu yasa ya share mata kana yace "Insha Allah, I will never guv you the chance to regret, Is a promise" Murmushi tayi, shima ya maida mata mikewa yayi da d'an saurin sa ya shige ban d'aki karar ruwan da taji ne hakan yasa ta gane yana wanka ne, Zama tayi tana jiran sa, tana jin ya fito ta sunkuyar da kanta, ta cigaba da wasa bda yatsun ta, abun ma dariya ya bashi, me bata sani a Jikin sa ba? Sai da ya gama Shirin sa tsaf yace "Muje muyi breakfast ko?" Ta amsa da toh, had'e da mikewa tayi gaba yabi bayanta, yau tare sukayi girki, sunayi suna Hira abin birgewa kamar wasu amarya da ango, ko da yake sun kusa su fad'a lambun ma'aurata. Bayan sun gama karyawa ne, ya fita da niyar tsara komai na yanda za'a d'aure auren sa da Ayrah, hakan kuwa akayi bai dawo ba har sai da ya tabbatar an sa ka ranar d'auren su Nan da sati d'aya hakan kuwa akayi,dama ba wuya a wurin Allah muddin an sa Rana, a yau aka d'aura auren Adnan da Ayrah Akan sadaki dubu d'ari. (Oh Ni Milhat jikar Mutum hud'u, Adnan ya d'aura auren da masoyiyar sa ba tare da iyayen sa ko iyayen ta sun sani ba, yayi hayan iyaye ba tare da Wanda ya d'aure ya sani ba, Ko ya zasu wanye? Mu cigaba da zuwa). Adnan ya sa an yi Masa video don ya tabbatar wa da Ayrah cewar an d'aura musu aure ta Zama mallakin sa, Allah sarki Ayrah a duk sanda aka d'aura wa yarinya aure tana samun kula ta musamman a gun dangin ta, za a rako ta har d'akin ta ana nuna mata so da Kauna sannan su rabu cikin kuka da kewar juna, Amma kashhh ita ta samu aka sin hakan, video d'in da yayi shine shaidar auren su, tayi kuka sosai Adnan tun yana rarrashin ta har ya daina ya fita ya bar mata d'akin ma gaba ki d'aya. Tun daga wannan ranan Ayrah kullum cikin kuka take,shi Kuma Adnan baya gajiya da bata hakuri a haka har ta sake Jiki dashi ta bashi dama Yana nuna mata irin soyayyar da yake mata,yana Kuma saka ta tana Kara son shi,duk da cewar tana kokarin taga ta 'boye,Amma masu iya magana sunce shi so baya 'buya. Haisam ta samu sauki sosai har ya Fara fita gun aiki,farin ciki da kwanciyar hankali Kuma sai dai ace Alhamdulillah,Isha na samun kula sosai musamman ma gun Umma da ta hana ta fita ko ina,idan ta fito to tare da Haisam suka fita Nan ma idan suka dad'e Umma tayi ta Kira Kenan Kira Kan Kira. Shirye shiryen Biki Meerah ake yau saura kwanaki Uku, events Kam sun Sha shi,sunyi friends day,bridal shower da dai sauran isha ba a barta a baya ba duk da ba wani Abu take ba sai dai ta zauna tana kallon su. *Ranar Biki* Farukh ne zaune da Haisam da sauran abokan sa suna shiri zuwa gun d'aurin aure sai tsokanan sa suke musamman ma haisam da dama sarkin tsokana ne,wayar Farukh ce tayi kara har da bazai d'auka ba sai Kuma ya zaro wayar a chaji ,sakon da ya shigo wayar sane yasa shi tsuman tsaye,Nan da Nan hawaye suka cika idanun sa,Kallo d'aya Haisam ya Masa ya Gane ba lafiya,hakan yasa ya mike ya nufi inda yake kafad'ar da ya dafa had'e da fad'in "Ya dai ango Lafiya kuwa ga na ganka Haka?" Farukh Mika Masa wayan yayi ba tare da ya Ce Masa kala ba, Haisam da d'an saurin sa ya sa hannu ya karb'a. Yana ganin abinda faruk d'in ya kalla zaro ido yayi dq d'an karfi yace "whaaaaatttt!!!! Hakan yasa dukkanin abokan su hankalin su yayi ta Dawo kansu,d'akin shiru yayi baka jin motsin komai sai Karan AC da kumma TV dake aiki. _________________ Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 77&78 Continuation.......''' 'daya daga cikin abokan sune yace "Ya dai Guys? Lafiya kuwa?" Murmushi Haisam yayi had'e da fad'in "Good" beyi aune ba sai jin karar an rufo kofa, farukh ne ya fita Yana mugun sauru. Haisam ne yace "Ku cigaba da shiri bari muzo" Bin bayansa sa yayi, har ya bud'e marfin motar yaji Muryar Haisam "Farukh ina zaka?" Cike da tashin hankali Farukh yace "zanje ne na dakatar da auren Nan, I can't marry Meerah, Ashe dama haka Meerah take? Duk irin soyayyar da nake mata Amma ace da abinda zata saka min Kenan" ya karasa maganar Yana kuka, Haisam kwace key d'in motar yayi ya zaga ya Shiga gun zaman driver, farukh kuwa kallon sa ya tsaya yi ya kasa motsi, Haisam lekowa yayi yace "bamu da Lokaci Shiga muje" "Ina zamu?" "Idan munje zaka gani" Tada motar yayi Mai gadi ya wangale musu gate suka fice daga gidan, gudu sosai haisam keyi sai da ya Isa inda yake son zuwa kana ya tsagaita gudun, a bakin gate d'in ya tsaya ba tare da ya Shiga ciki ba, wayar sa ya d'auka ya Shiga yayi dialling number, duka biyu ta d'aga da sallama, kai tsaye yace "Ki fito ki same ni ina waje,

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});