Chapter 34
Chapter 34
zamuje mu nema Masa aure" Zumbur ta Mike Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Aure Kuma? Yayan aure zeyi?" Mummy cikin fad'a Tace "Ke Lafiyan ki kuwa me haka?" Jiki a sanyaye ta d'auki Jakarta ta haura sama da gudu tana kuka, Daddy yace "Meyasa Kika yi Haka?" "Alhaji me Kuma nayi?" "Baki San ma me kikayi ba?" "Umm to Alhaji maganar aure fa akayi, sai kace zancen mutuwa akayi, Kuma Alhaji ban ma San nayi hakan ba,Amma Alhaji nifa ina ganin yarinyar Nan tana son Haisam" "Kamarya Kenan fa?" "Baka lura da hakan ba yanzu fa maganar auren sa da kayi ne ya razanar da ita yanzu Nan tabbata kuka takeyi" Ajiyar zuciya daddy yayi yace "Maybe shakuwa ce kawai ba soyayya bace , Amma shekaru nawa sukayi suna tare a gidan Nan ai in da Soyayyar ce da mun sani ko? " "Hakane Kam, to Allah ya tabbatar da Alhairi" "ameen." Kamar yadda mummy Tace Isha kuka take tun da ta shiga d'akinta take aikin kuka Haisam kuwa Yana kwance hankalin sa kwance Yana waya sa masoyoyar sa, ya sanar da ita su daddy zasu zo gobe, tayi murna sosai harda Yar tsallen ta, Tace "Yanzu bari naje na fad'awa Mom ta sanarwa da Daddy" "Toh ki bari mu gama wayar Mana tukanna" "Aaa wallahi za dai muyi waya anjima zanje na fad'a mata" "Uhmn habibty zumud'i Kenan?" Cikin muryar Shagwab'a Tace "Toh habib ranar da nake jira Kenan fa kaga zumud'i dole, so kar kaga laifina" "A a Banga laifin ki ba ko kad'an ni kaina na kosa goben tayi, don a gaskiya ban so auren mu ya wuce Nan sa da 3 Months" Zaro Ido tayi kamar yana kallon ta tace "Har 3 Months Gaskiya yamin Nisa Habib" "A hakan yayi nisa? To ya ya kike so ayi?" "Nan da 2 months dai,kaga dama muna Shirin Exams ne zamu samu hutu Mai d'an tsayi kawai sai ayi" "To Shikenan hakan za'ayi zan Sanar wa su Daddy idan sun amince Shikenan" "Zama su amince,yanzu dai bye naji kamar daddy ya Shigo" "Bye" ta katsewayar, da kanta ta Sanar da dad halin da ake cike Murmushi yayi yace "Yaran zamani ba kunya wato ma zan yi baki Shikenan Allah ya Kai mu goben sai sun Zo" "To Daddy." Ma'isha kuwa sai da tayi kuka Mai isarta kana ta fito parlor mummy Tace "Dama yanzu zan Shiga na duba ki Lafiyan ki kuwa?" "Lafiya Lau Umma" "Ya naga idanun ki sun Kumbura?" "Bacci nayi Mummy,an gama abinci?" Ta fad'i hakanne don ta kawar da maganar ba don tana Jin yunwa ba. Mummy ta amsa da "Eh an gama,Yau anan Zaki Kwana ba gidan su Abba ba?" "Eh Mummy sai jibi zan koma chan d'in" "To Shikenan Allah ya kaimu,zo muje dining d'in." A tare suka zauna Ma'isha Tace "Mummy ina daddy?" "Ya fita yaje gidan Abban ku zasuyi maganar zuwa gidan su budurwar Yayan ki" Ma'isha ji tayi kamar zuciyar ta zata buga,ganin irin kallon da Mummy take Mata tana son gane wani abu tayi kirkirerren Murmushi Tace "Nifa na d'auka Yaya is not serious about her" "Dama kinsan tane?" "Eh na santa ita ma a school d'in mu take course d'insu d'aya da yaya" "Kina so kice min course mate d'insa ce" "Eh to kusan hakanne Amma fa ba aji d'aya suke ba,sune zasu Gama a shekarar Nan" "Oh Masha Allah, Yayan naki Kinga na manta kije ki kirashi yazo yaci abinci" Ta Mike Kenan ta hango shi Yana saukowa hannun sa a manne a kunnen sa yana waya Yana dariya,Zama tayi Tace "Gashi Nan ma" "Okay" Sai da ya gama wayar yazo ya ja kujera had'e da fad'in "Barka da Dare Mummy" "Yauwa Barka son,yanzu nake ce mata ta Kira ka sai ga kanan,waya ake tayi haka da surkuwa ta?" Murmushi yayi kawai baice mata komai ba, Ma'isha tace "Yaya ina wuni" "Lafiya Lau princess, pharmacists of the house ya na ganki haka? Baki da lafiya ne?" "Bacci na wuni yi Yaya" Mummy Tace "Wai wuni naga Bayan la'asar Kika dawo" Uhmn kawai Tace ta cigaba da cin abincin,ci kawai take Amma bata jin dad'in abincin Sam kasantuwar bakin ta Duk d'aci,mikewa tayi ta ajiye plate d'in a kitchen kana ta wuce d'akin ta ba tare da tace musu komai ba. Haisam yace "Mummy Amma baki lura kamar princess na cikin damuwa ba?" "Gata Nan dai nima na lura da hakan Amma na tambaye ta Tace min bakomai" Mikewa yayi yace "Bari naje naji ko mene ne." Bai jira yaji amsar ta ba ya haura sama da sauri, tun daga kofar d'akin yaji tana ta dariya, a hankali ya tura yaga tana waya Zama yayi tana kallon sa Amma Bata kashe wayar ba,ta d'auki kusan 5 minutes Kan ta katsewayar da fad'in "Sorry Love zan Kira ka yanzu" Haisam ji yayi wani abu ya tokaresa a wuya Ma'isha Tace "Am sorry yaya wallahi Ma'aruf ne yake ta bani dariya" Cikin rashin Jin dad'in maganar nata yace "Waye ma'aruf?" "Saurayina man Yaya Wanda yake zuwa gidan Nan" "Oh that guy? Ni ban San sunan sa ba" "Ma'aruf sunan sa" "Ban San me Kika gani a jikin sa ba Ni Sam bai min ba" "Yaya saurayin nawa ne bai maka ba? Aiko shi nake so Kuma zan aura" "Hmm lallai gani nake Sam baku dace ba" Ma'isha wayanta ta bud'e ta Shiga gallery ta Mika Masa wayan had'e da fad'in "have a look" Karb'a yayi ganin hotunan da suka d'auka tare sauran selfies ne sauran Kuma d'aukan su akayi suna dariya a wurare da dama,sauran gun wurin cin abinci ne da ice cream Rai a 'bace ya Mika mata wayan yace "ba laifi maybe ranar kallon tsoro na Masa,Kuma yana sonki?" "Eh Mana sosai ma yana sona ga alamu Nan, hotunan Nan da ka gani ai sun Isa ka gane hakan" "Hakan.......yanzu auren sa zakiyi?" "Eh insha Allah,daddy ma yace na fad'a Masa ya turo don Yana so a had'a ayi rana d'aya" "Me za'a had'an" "My wedding and yours" Mikewa yayi yace "Yayi kyau" Ya fice Isha kuwa d'aga kafad'a tayi irin halin ko in kula d'in Nan ta Kira Ma'aruf ya katse kana ya kirata suka cigaba da wayar su. Haisam kuwa Yana Shiga d'akin sa ya kasa tsaye ya kasa zaune ya rasa dalilin da yasa yaji duk ya damu baya son Ma'isha ta auri gayen Nan, dafe kansa yayi yace "Maybe ko don gayen baya burgeni ne?" Ya kuma bawa kansa amsa da "Hakanne ma?" Wayar sa ya d'auka kamar zai Kira Aysha sai kuma ya fasa ya kashe wayar gaba ki d'aya ya kwanta dakyar da makyar kyasa bacci ya sace shi. *Washe Gari* Karfe hud'u na yamma,Daddy da Abba suka shirya don zuwa gidan su Aysha , Haisam ke Jan motar yayin da Abba ke gefen sa daddy Kuma yana baya suna tafiya suna Hira har suka Isa. Kasantuwar an san da zuwan su aka musu iso cikin gidan,Amma Haisam a mota ya zauna ya kira ta a waya suna ta Hira daddy da Abba suka gabatar da Kan su,shima Dad d'in Aysha da kannen sa maza biyu suka gabatar da kan sun,sun fahimci juna sosai kasantuwar Daddy sa nannen mutum ne, sannan basu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76