Chapter 31
Chapter 31
kamar rarrashi yace "Umma please, Dan Allah ki duba lamarin nan" "Haisam Kenan, haryanzu baka fahimce ni ba Sam, bazan iya auran wani ba Bayan mahaifin ka zan cigaba da Zama haka har nima mutuwa ta riske Ni" "Umma ki dubi girman Allah ki sake tunani a Kai, kar ki manta fa Daddy shi ya taimaka mans muka fita daga cikin kuncin Rayuwa har muka dawo Mutane, kin San abubuwan da bazan iya lissafa su ba, yau yana neman abu a wurin Wanda zamu iya bashi Kuma mu hana shi, Idan mukayi hakan ba muyi Masa butulci ba kuwa?" A razane ta d'ago kanta ta kalli Haisam d'in kana ta sake kawar da kanta, ba Tace Masa komai ba magana yayi tayi Yana bata hakuri Amma bata tanka Masa ba har ya gaji yayi shiru mikewa yayi da niyar fita, har yasa Kai ya tsinkayo Murya Umma tana fad'in "Shikenan Na amince" Da d'an saurin sa ya dawo cikin d'akin ya d'an rungumeta ta kana ya sake ta yace "Yauwa Umma ta ai nasan Zaki amince" mikewa yayi Yana fad'in "zani na fad'awa Mummy" "Wa ya aike ka? Ka bari da kaina zan Sanar da ita dama yanzu zan Shiga part d'insu" Murmushi yayi yace "Shikenan Umma" Mikewa tayi ta d'auki mayafin ta, ta nufi part d'insu mummy ta tarar a parlor sun dad'e suna Hira sama sama kamun ta fad'a Mata cewar ta amince mummy murna yasa ta Kira daddy a waya ta Sanar mishi, yayi farin ciki sosai shima Nan take ya Sanar da Abba, Abba baiyi kasa a gwiwa ba yasa aka tura masa number ta Sannan mummy ta bata na Abba, Ba 'bata lokaci ya neman Soyayyar ta. Haisam kuwa d'akin Isha ya Shiga ya Sanar da ita labari Mai dad'i tayi murna sosai, Nan sukayi ta hirar su. *BAYAN WATA 5* Shirye shiryen biki su ke tayi duk da ba wani events zasuyi ba daga walima sai walima shima anan gidan su Ma'isha kawai za'ayi. Yayin da Haisam da Aysha wata soyayya ce Mai karfi ya Shiga tsakanin su kusan kullum suna tare, Ma'isha kuwa damuwa Sai abunda ya karu, Meerah kuwa kusan ko wani sati zata Zo ta duba lafiyar ta sannnan ta bata shawarwarin da ya Dace Amma Duk da hakan Isha ta kasa daina son Haisam. Alhamdulillah an d'aura Auren Umma da Abba sannan Amarya ta tare a gidan ta anan cikin garin gombe, Daddy ne yayi iya bakin kokarin sa ganin ya dawo da dukkanin aikin Abba a gombe. Ma'aruf kullum cikin Kiran Meerah yake Akan maganar Ma'isha, Amma Ma'isha Taki bada had'in Kai shi Kuma ya kasa hakura. Wannan Kenan "Isha please think about it Mana, Wallahi ma'aruf na sonki ke ko tausayin sa bakya ji? Ki duba kiga ni fa tun d'azu Yana waje Yana jiran ki Amma kin ki, ki saurare shi" "Nifa na Riga na fad'a muku bana son sa Kuma bazan tab'a son wani ba bayan Haisam meyasa Kika kasa fahimta na ne?" "To ai Banga amafanin hakan ba, tunda kin kasa fad'a Masa har yayi nisa da soyayyar wata hakan zai tabbatar miki da cewar kin rasa shi Kennan har abada" Hawaye na a idanun Ma'isha d'aya na bin d'aya, taji zafin maganar Meerah Amma Kuma tasan gaskiya ta fad'a mata sabida masu iya magana sukace shi Gaskiya d'aci gareta. "Na Sani Meerah, nasan kin damu dani kin damu da farin cikina gami da lafiya ta Amma Dan Allah kar kiyi kokarin sani Dole sai na Kula shi" Mikewa meerah tayi Tace "fine then Ni zan tafi dama shine ya ce na rako shi, ki sani baza ki sake gani na ba a gidan ku, sannan zan fad'awa Haisam halin da kike ciki" ta Kama hanya zata wuce Ma'isha ta Sha gaban rike hannayen ta tayi tana kuka "Please don't do this to me Meerah ke ce kad'ai kike saurarata ke ce kad'ai Kika San damuwa ta Akan me zakimin irin wannan hukuncin Kuma Kar ki manta kin min alkawarin baza ki tab'a fad'a wa kowa matsala ta ba" Fin cike hannun ta tayi da karfi Tace "Dallah malama gafara min na wuce idan ke baki da shi to ni Ina dashi, idan baza ki bawa ma'aruf dama ba ya maye miki gurbin Haisam ba to Dole ne ki samu Haisam" Har kasa ta durkusa ta rike kafafun ta tana Mata magiya Akan Kar ta fad'a Masa. Meerah Sam Bata Jin dad'in ganin kukan ta Amma Dole ce tasa tayi Mata hakan, Dole ta samarwa kawarta farin ciki gudun Kar ta kamu da ciwon zuciya. Cikin murya Kamar fad'a Tace "Wallahi tallahi sai na fad'a Masa in dai baza ki kula ma'aruf ba ai zab'i na Baki" mikewa Isha ta tayi ta share hawayen ta Tace "Shikenan na amince wallahi zan kula ma'aruf, Dan Allah kar ki fad'awa ya Haisam Dan Allah" Murmushin samun nasara Meerah tayi kana ta sa hannu tana share Mata sauran hawayen dake fuskar ta. Cike da kulawa Tace "Am sorry Isha, ki daina kuka Sam bana jin dad'in ganin ki a Haka ne shiyasa nabi ta wannan hanyan, yanzu ki d'auko mayafin ki muje Yana chan yana jiran mu Amma ki wanke fuskar ki tukkunna" Ba musu tayi yanda Tace mata suka fita suka tarar dashi a cikin motar sa, jiki na rawa ya fito suka gaisa, Mai gadi tasa ya kawo musu kujera ya ajiye musu a inuwa, suka zauna daga bisani Meerah ta koma d'akin Isha tana jiran su, sai da suka gama hiran ma'aruf ya kirata ya maida ta gida, tun daga wannan ranar Isha ta fara kula ma'aruf lokaci zuwa lokaci Kuma Yana zuwa gidan su tun bata sake Masa har ta Fara Duk da ba son shi take ba, ma'aruf mutum ne mai abin dariya yakan sa taji ta manta Duk wata damuwar da take dashi in dai suna tare. *AFTER 1 YEAR* Sosai Ma'isha ke mayar da hankalin ta Akan karatun ta, Sannan Duk weekend a gidan Umma take yi, Haisam kuwa tunda Umma tayi aure aka rufe part d'insu ya dawo part d'insu mummy Yana d'akin sa kusa da na Ma'isha , idan suna gida sukan zauna a parlor suyi Hira Duk sanda ya kawo maganar Aysha kuwa sai tayi yanda tayi ta kawar da maganar. Ma'isha ne zaune da Ma'aruf a garden suna hirar su, labari yake Bata dariya take Sha sosai yayin da shi Kuma sai aikin kallonta yake. Haisam kuwa dawowar sa Kenan daga gun Aysha tunda ya Shigo gidan yake kallon su, ji yayi ransa ya 'baci Amma bai San dalilin hakan ba, ya d'auki kusan mintuna biyar Yana kallon su su kuwa Basu ma ji shigowar sa ba, kasantuwar motan da tint yasa Basu ganshi ba, ajiyar zuciya yayi Sannan ya fice daga cikin motar har ya wuce Ma'isha Tace "Yaya ka dawo?" Kirkirerren Murmushi yayi Sannan ya dawo mikawa ma'aruf hannu yayi suka gaisa turo baki Isha tayi Tace "Dama Yaya wuce wa zakayi Kamar baka ganmu ba?" "Am sorry princess , kin San hankali shine gani ban lura bane" kallon Ma'aruf yayi Wanda shima kallon sa yake yi, da sauri ma'aruf d'auke Kan sa gani yayi ya Masa kwarjini, maganar su sukayi tayi kana ya shige
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76