Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta Isa asibitin na had'a su duka tayi ta masifa Banda hakuri Babu abinda suka ce mata, haka Umma ta kwana ba ta haihu ba sai uban wahalar da take Sha, har gari ya waye sai abin ya tashi ya sake kwanciya. Ganin har karfe 8 tayie bata Haihuwa ba Umma Tace su koma guda Ma'isha ta had'o musu breakfast ta kawo, a gidan Umma Haisam ya ajiye ta ya Koma gida yayi wanka ya dawo gidan Umman sai da ya karya Ma'isha ma tayi wanka suka koma asibitin. Abba na Abuja ji yake kamar ya dawo Amma ba hali kasantuwar washe gari yana da meeting da zasuyi, Daddy Kuma yana bauchi yaje yin wasu harkokin sa a Chan, anan asibiti sukayi sallar azahar, Haisam banda matsar kwalla ba abinda yake yi Mummy da Isha Kuma sai aikin rarrashin sa suke suna kwantar Masa da hankali Likita ce ta fiti fuskanta d'auke yake da Murmushi gunsu ta nufa Tace "Alhamdulillah Allah ya sauke ta lafiya, ta Samu Twins duka Mata" A tare su Umma suka Shiga hamdallah, Likita kuwa Tace "Amma ta zubar da jini sosai Gaskiya tana bukatar jini" Haisam a rud'e yace "To a d'i a nawa mana" Hannu ta d'aga Masa had'e da fad'in "Come with me." Yabi bayanta. Sai da aka gyara su tsaf da jariran ta Mummy da isha suka Shiga suka gansu Yara kyawa Masha Allah, wayar Ma'isha ce Fara ringing picking tayi ta dafa Kai "Tace am sorry wallahi yanzu haka ina specialist ne mom d'ina ce take labour, Amma gani Nan zauwa yanzu" Mikewa tayi Tace "Mummy zan tafi ni na manta ma yau afternoon nake karfe biyu ya kamata na karb'e ta gashi har quarter to 3 yanzu" "Yi maza kije Allah ya tsare" Ta amsa da "Ameen Mummy" sai da ta d'auki hoton jariran kana ta fice, napep ta Tara ta koma gidan Umma ta d'auko lab coat d'inta kana ta d'auki motar ta ta wuce asibiti, tana Isa wacce zata karb'e ta, ta tafi, wayar ta ta zaro ta turawa Daddy da Abba hotunan, Abba na gani ya kirata Yace "Dama ta haihu ne babu Wanda ya fad'a min" "Eh Abba d'azun Nan ta haihu" "Amma shine baku fad'a min ba tun d'azu hankali na a tashe yake" "Yi hakuri abba wallahi Mun shafa'a ne, Kuma ance tana bukatar Karin jini" "Subhannallahi an samu an Sa Mata?" " Ban sani ba wallahi nima yanzu ina bakin aikine" "okay bari na Kira su naji" Ya katse wayar Murmushi tayi Tace "Lalllai Abba bai ma damu da yaran ba matar sa kawai ya sani" Nan ta cigaba da aikin ta. Haisam kuwa jinin sa bai Dace da na Umma ba sai da suka saya sannan aka sa mata, bacci Tasha sosai har sai yamma lis ta farka, Murmushi kawai tayi ta yi, tana kallon 'ya'yan ta. Mummy kanta ne ya kulle ta rasa yadda zatayi , Ma'isha na gun aiki gashi suna bukatar abinci yau ga ranar Yar aiki, Kiran abba tayi ta rarrashi shi cikin ikon Allah ya amince dama akwai wacce take son Fara aikin a gidan mummy Amma ya Hana, Mummy ba tayi kasa a gwiwa ba ta kirata, ta fad'a mata Duk abinda zatayi tana zuwa Mai gadi ya bud'e mata gate ta shiga sabida mummy ta Riga ta fad'a Masa hakan yasa bai tsaya tambayar ta ba. Duk abubuwan da Mummy ta fad'awa Sadiya duk tayi su kasantuwar ita d'in Mai nutsuwa ce, Bayan ta gama ne ta Kira Hajiya ta Sanar mata akan ta gama, Mai gadi mummy ta Kira tasa ya kawo ta asibitin ta kawo musu abinci da duk da duk wani abun da zasu bukata. Kwanakin su uku a asibitin aka sallame su, a ranar Kuma Abba ya dawo, bakin Nan a wage an kasa rufe shi, Mummy Kam gaba ki d'aya ta dawo gidan Umma tana kula da ita, bayan Nan mummy tasa Dole sai da aka samawa Umma ita ma Yar aiki, sai Bayan suna Mummy ta koma gida kasantuwar Daddy zai dawo, Twins kuwa Ana Kiran su da Aaima da Aymana. Sosai suke samun kulawa a gun familyn gaba ki d'aya kun San Twins da Shiga Rai musamman ma ace identical Twins ne. Kwan a tashi ba wuya a wurin Allah, Haisam ya samu ya gama makarantar sa sabida good Results d'insa ma Asibitoci da dama suna son su d'auke shi aiki, Amma Isha ta kafa ta tsare Dole ya karb'a a inda itama take aiki, acikin shakara d'aya komai ya canza, Haisam kuwa dama a kage yake ya gama don ya samu damar mallakar Aysha, Ma'aruf kuwa Ma'isha ta kaishi sun gaisa da su Daddy an San da zaman shi, komai tafiya normal yake sai godiyar Allah. Haisam ne zaune shi daddy suna Kallo a parlor sai yayi Kamar zaiyi magana sai Kuma ya kasa, mummy Ce ta fito hannun ta rike take da Plate fruits ne a ciki ta ajiye a gaban Daddy, Kallon Haisam tayi Wanda ya Shiga duniyar tunani, Kiran sunan sa da tayi "Son!!! Ne ya dawo da shi daga tunanin da ya Lula ya amsa da "Na'am Mummy" "Lafiyan ka kuwa?" "Lafiya Lau Mummy" Murmushi daddy yayi yace "Tun d'azu na lura dashi Akwai abinda yake damun sa amma yayi shiru, ka fad'a Mana Son me ke faruwane? Ko dai matsalar daga gun aikine?" "A a daddy dama.... " Sai Kuna yayi shiru yana Sosa keya daddy yace "Feel free man, ka Fad'i Duk abinda kake so ni Kuma na maka alkawari zan maka shi in bai fi karfina ba" "Umm dama... Dama Akwai wacce Muke soyyaya da itane , to ina so a nema min auren tane" Murmushi mummy tayi Haka shima daddyn yace "Wace ce Kuma Yar gidan wace ce?" "Sunanta Aysha,Amma Gaskiya daddy tun da muke ban samu damar ganin mahaifin ta ba, Amma na San gidan su" "Toh Shikenan ba matsala, sai ka Sanar da ita su sa mana Rana" "Daddy Kuna iya zuwa gobe ma don munyi magana da ita" "To Shikenan dama Abban Kuma yana gari kaga sai muje goben kawai" "To Shikenan Allah ya kaimu." Mummy tunda Haisam ya ambaci sunan wata ba sunan Ma'isha ba sai taji ba dad'i Haisam mikewa yayi ta Shige d'akin sa, mummy cikin damuwa Tace "Alhaji wallahi na d'auka yaran Nan soyayya suke" Cikin rashin fahimta yace "Wasu yaran Kenan?" "Ma'isha da Haisam Mana Gaskiya na dad'e ina burin naga an had'a su aure" "hmm bake kadai ba har Ni kaina na yaba da halin yaron Nan, Amma tunda ya ce ga wacce yake so ai baza mu Masa Dole ba ita Ma'ishan sai ta fad'awa wannan yaron da yake zuwa gun ta ya turo Iyayen sa sai a had'a ayi rana d'aya." Ma'isha ce ta Shigo cikin parlor bakin ta d'auke da sallama da kayan aiki ajikin ta da alama daga asibiti take Zama tayi a Kan kujerar da yake fuskantar su Daddy a kasalan ce ta gaida su suka amsa daddy yace "Yauwa daughter kin dawo a dai dai, ki fad'awa wannan yaron da yake zuwa wurin ki ya turo magabatan sa in har da gaske yake sai a had'a Rana d'aya da na Yayan ki shima gobe

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});