Chapter 67
Chapter 67
matar da take Kawo Mana abinci a 'boye ba tare da Mijinta ya sani ba, sannan itace matar da take kullar miki dani a lokacin da babu Wanda yake tare da ke, ta d'auki risk da dama akaina, shin Umma laifin wani na shafan wani dama?" Ya karasa maganar cikin sanyin Murya. Shiru Umma tayi , Jikin ta ne yayi sanyi tabbasa mamy mutunce ta taimaka musu da ita da 'danta a lokacin da basu da kowa basu da komai, kosan da ta sayar a baya ma Itace ta bata jarin, tana cikin wannan tunaniin ne ta ji an Kama Mata kafa da sauri ta kalli a kasa, ganin Mamy tayi ta zube a gaban ta, tana kuka Tace "Dan Allah maman Yara kiyi Hakuri nasan an cutar dake, nasan Hakurin da zan baki bazai Canza komai ba, but please find a place in your heart to forgive and believe me, Wallahi I know nothing about this, hatta ita Ayrah ma bata San komai ba, you know how Hassan is he a very manipulative human being, yayi manipulating d'inta ne Wallahi bata San komai ba Yanzu haka maganar da nake miki ayrah ta 'bata kusan watanni hud'u kenan bamu San inda take ba ko ta mutu ko tana raye bamu sani ba, babban tashin hankali na ace ta mutu bamu gana ba sabida nayi fushi da ita tsawon shekarun Nan da muka rasa Haisam, Akan sai ya farka na yafe mata gashi ya farka and she is nowhere to be found" ta karasa maganar cikin kuka. "Tabbas ni shaida ce, Mamy bata kula Ayrah, Wanda hakan ba karamin tada Mata hankali ba" duk suka kalleta, sai Kuma tayi shiru kamar ba ita tayi maganar ba, Haisam kallo d'aya ya mata ya gane ta, ya dad'e Yana kallon ta kamar Mai son gano wani abu, sai Kuma ya kawar da kansa. Umma hannu tasa ta d'ago Mamy suka rungume juna, Umma na fad'in "Kiyi Hakuri Maman Yara, da na kasa fahimtar ki na manta duk abubuwan da suka faru a baya, na rasa madafa, Ina cikin tashin hankali" " Ko kad'an Banga laifin ki ba, Amma Dan Allah ki yafe min" "Allah ya yafe Mana duka" Duk suka Masa da amin Amma fa Banda Mardiya da take ta taunan chewn gum tana latsar wayarta. Duk wuri suka samu suka zauna, kasantuwar d'akin babba ne ya d'auke su, Hira suka Fara yi harda Mummy, cikin hiran ne suka yanke shawarar zuwa ganin Jikin malam hassan, Mummy, Umma da Mamy suka fita,suna fita Haisam ya Koma Kan gadon sa ya kwanta suna Hira da Isha,daga bisani sukayi shiru baka jin komai sai karar chewn gum d'in da Mardiya ke tauna. Suna cikin wannan yanayin ne faruk da Meerah suka shigo, Isha na ganin Meerah da d'an saurin ta Mike ta rungume Meerah, Meerah d'an ture ta tayi tana fad'in "Kaaai mai ciki zungurina fa kike da tumbin ki" sai a sannan mardiya ta d'ago kai ta sauke Akan tumbin Isha, zaro Ido tayi tana kallon Isha, Meerah da ta lura da kallon da take mata Tace "Allah ya sauke ki lafiya mu samu Ma'aruf junior" Mikewa tayi tana kallon Isha cikin Muryar kuka Tace "Ciki? Ciki kike dashi Isha? Cikin Yayana?" Duk lokaci Guda ta jero mata tambayoyin Nan, Murmushi Isha tayi kana Tace "Uhmnn eh" mardiya Rungume Isha tayi ta fashe da kukan farin ciki. _________________________ Please comment and share Milhaat ce Yar Terawa [8/15, 8:02 PM] Miilhaat Writer✍🏻: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM* Page 71&72 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ ```Continuation.......``` Isha Murmushi kawai take ta kasa bata amsar tambayoyin ta, mardiya sakin Isha tayi hawayen fal a kwarmin idanun ta, Tace "Allah ya sauke ki lafiya" Duk suka amsa da Amin, Farukh ne ya zauna kusa da Haisam musabaha sukayi, sannan ya tambaye shi ya Jiki, hiran su suke hankali kwance, yayin da Meerah da Isha ma tasu hirar suke, Mardiya kuwa ta yi saye tana kallon su kamar gunki, kallon ta Farukh yayi yace "Hajiya ki zauna Mana" kamar dama jira take ta koma mazaunin ta Jiki a Sanyaye. Farukh yace "Baby ya Kamata mu tafi fa, kin San akwai wuraren da bamu je ba tukunna" Mike wa Meerah tayi fuskar ta d'auke yake da Murmushi, kallon ina zakuje Isha take Mata, hannu tasa a jakar ta ta cire IV (invitation card) ta zaro su dayawa bata San Guda nawa bane ma ta Mika wa Isha had'e da "fad'in tare ya Kamata mu raba, amma Kuma kina tare da patient, ga wa'annan ki bawa Wanda ta dace" Kallon kati Isha tayi tana Murmushi Tace "Kai Masha Allah, katin yayi kyau, ikon Allah baikin saura 1 months" ta karisi maganar tana kallon Meerah, Murmushi tayi Tace "Eh." Gyaran Murya Haisam yayi kana yace "Amarya to ni ina katin nawa ko baza a gayyace Ni bane?" Yar karamar dariya tayi kana Tace "Ai sai dai kayi gayya ba dai a gayyace ka ba" Faruk yace "You're right kaifa babban abokin angone" " Isha Kuma babbar kawar Amarya ba, an bata Amma Ni ba'a bani ba" a Shagwab'ance Haisam yayi maganar kamar karamin yaro. Isha dariya ma ya bata ta Mike ta Mika Masa Tace "Gasu Nan Yaya" Meerah Tace "Bakwa gajiya da drama, to ai Ishan ba nata bane na bata ne don tayi gayyar ta itama" " To Nima a bani tawa" ai kuwa da sauri Meerah ta Sanya hannu a jaka ta miko Masa masu yawa, dariya ya shigayi had'e da fad'in "Ni Wallahi zolayar ki nake, Allah ya nuna Mana ranar" Suka amsa da Amin. Mardiya kuwa ji take kamar ta Burma musu huka, ta tsani taga Meerah na cikin farin ciki duk da ta kasance kawarta ce tun na yaranta, mardiya irin mutanen ne masu bakin hassada da Kuma kyashi. Meerah da Farukh suka nufi hanyan fita, sai Meerah ta juyo kamar tayi mantuwa, inda Mardiya take ta nufa,ta zaro kati d'aya ta Mika mata had'e da fad'in "Be my guest" kallon katin ta tsaya yi kamar Mai tunani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76