Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 37

Chapter 37

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wa jama'a?" "Amma Yaya Ana uzuri ko?" "Eh Ana uzuri, Amma baza a d'aga bikin Nan ba, ranar jumma'ar Nan za'a d'aura auren. Abba ganin Daddy dagaske yake hakan yasa ya bar maganar suka Fara maganar kasuwancin su, Haisam kuwa Zama yayi dasu mummy Yana Basu hakuri had'e da wasa da kannen sa, sun girma sai wayo idan sukayi wata maganar zakace fad'a musu akayi, dab da sallar magrib Abba ya Shigo akan su koma gida. Umma ta kekashe Tace babu inda zata je anan zata kwana sabida ta kula da Ma'isha, Dole daddy ya hakura, Daddy ne yace "To kaji, kaima sai ka kwana anan, tunda gidan babu kowa baza ma kaji dad'in gidan ba." Murmushi yayi irin nasu na manya yace "To ya na iya da garen da ba wuya? Dole nima na kwana" Daddy ne ya maida kallon sa ga Haisam yace "Toh masu kanne taso muje Masallaci" suka wuce. Sosa keya Haisam yayi ya bi Bayan su. Ma'isha sai da gari ya Waye kana ta farka, mikewa tayi ta Shiga ban d'aki ta wasa ruwa kana ta d'auro alwala Sannan ta Shiga jero sallolin da ake binta, Bayan ta idar ne ta sauko parlor Jin muryar su Mummy a dinning room ne ya sa ta nufi gun, da sallama ta karasa inda suke ta jaa kujera ta zauna dukkanin su kallon ta suka Shiga yi cike da mamaki Umma tace "d'azun Nan fa na leke ta tana bacci, Amma gashi ta fito." Abba ne cike da kulawa yace "Daughter ya jikin naki?" Ta amsa da "Sauki Alhamdulillah" Daddy yace "Sannu daughter" Ta amsa da "Yauwa nagode Daddy." Mummy mikewa tayi ta shafa kanta had'e da tab'a wuyan ta Tace "Jikin naki da d'an zafi har yanzu" "Uhmn da sauki mummy" Haisam kuwa gyaran murya yayi yace "Princess ya jikin naki? Da fatan bakya jin komai yanzu?" Kirkirerren Murmushi tayi kana tace "Eh bana jin komai , sai Kaine da yake d'an sarawa kad'an kad'an" "Allah ya sauwaka, shima zai daina a hankali." Duk suka amsa da "Allah yasa" Kallon Mummy Ma'isha tayi Tace "Mummy nima a Samin abincin" Jika na rawa ta sa mata abinci, kallon ta suka tsaya yi Murmushi tayi Tace "Dan Allah ku daina kallo na haka sai ku sa na kware." Haisam yace "Ai Dole ne mukalle ki, Duk da Yan kwanaki kikayi bakya cikin mu, ji muke Kamar shekara kikayi" ya maida kallon sa ga su Umma ya d'aura da fad'in "Ko ba Haka ba" Umma ta amsa da hakane, dariya sukayi suna ta hirar su, dukkanin su sunji dad'in ganin Ma'isha a haka. Sai da aka Fara kiraye kirayen sallar azahar ,Duk mazan Suku fice zuwa Masallaci, Bayan sun idar da sallar kuwa asibiti suka nufa, Haisam office d'insa ya bud'e musu suka zauna kana ya fita, bai wani dad'ewa ba suka ya Shigo Meerah kuwa na biye da shi. Har kasa ta durkusa ta gaida daddy ne yace "Tashi ki zauna" Yana nuna mata kujerar dake fuskantar su, Bayan ta zauna ne ya Fara magana yace "Meerah nasan Daughters bata da kawar da ta wuce ki, sannan nasan kin San sirrukanta Dan Allah ina so ki fad'a min abinda Kika sani game da Wanda take so" Kai ta d'aga ta kalle shi kana ta maida kanta kasa Tace "Daddy ban sani ba, ban San Wanda take so ba" Abba yace "Please ki fad'a Mana gaskiya nasan Dole Akwai abinda Kika sani akai" Meerah har cikin ranta take so ta Sanar dasu gaskiya Amma idan ta tuna alkawarin da tayi wa Ma'isha sai ta fasa Tace "Abba da na sani wallahi zan fad'a Muku" Haisam ransa ya yi mugun 'baci cikin 'bacin Rai yace "Wallahi karya take Daddy, da kunne na fa naji lokacin da suke maganar Amma yanzu Kuma don ta Raina Mana hankali tace bata sani ba" Daddy yace "Son calm down" Abba yace "Kinji ko Ameerah, Dan Allah ki fad'a mana wane ne, kece kad'ai zaki taimaka Mana wajen sama wa zuciyar ta abinda take muradi" Shiru tayi tana matsar kwalla, a tsawace haisam yace "Shegen taurin Kan tsiyane da ita, ranar babu yadda banyi da ita ba Akan ta fad'a Min Amma taki, na rantse da Allah idan wani abu ya sami princess...... " Daddy ne ya d'aga Masa hannu yace "Ya Isa , ya Isa " mikewa yayi ya kalli Abba yace "Mu tafi ko?" Abba Rai ba dad'i ya mike yana girgiza Kai, Sai da suka Isa kofar fita, Abba ne ya juyo ya kalle ta yace "ki yiwa girman Allah ki ceci rayuwar Isha wallahi tana cikin wani matsanancin hali dan Allah ki fad'a mana gaskiya wane wannan wanda Isha take so a ina yake kuma d'an waye?" Cikin Muryar kuka Tace "Wallahi ban sani ba,da na sani da na fad'a Muku" Girgiza Kai Daddy yayi yace "Allah shi kyauta" suka fice Haisam Rai a 'bace yace "Tirrr da qawa irin ki, Wallahi ko kaffara bazan yi ba kin San komai" "Ya Haisam ban....... " A tsawace yace "Get out of my office" a tsorace tayi hanyar fita sai da ta kusa fita yace "Kuma ki sani idan wani abu ya same ta kece sila" cikin kuka ta fice. Tana fita shima ya fita, rufe kofar office d'in yayi ya nufi gun su Daddy dake tsaye a jikin motar sa suna jiran sa , hakuri ya basu Duk suka shige motar suka koma gida, Bayan ya ajiye sune ya koma office don cigaba da aikin sa. Daddy da Abba ganin Isha na walwala hakan yasa suka d'an ji dad'i, ta wuni cikin farin ciki sai fara'a take,Nan suka Cigiba da shirye shiryen biki, Isha kuwa Duk lokacin da ta Shiga tashin hankali sai ta Rika ambaton '''la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu Minal zalimin''' hakanne yasa ta ji sauki abun Sosai. Rana bata karya sai dai uwar d'iya taji kunya, yaune ranar da Haisam da Aysha suke jira, shine ranar da yafi shekaru har hud'u yana jiran wannan ranar, Bayan sallar jumma'a za a d'aura auren amma a kofar gidan su Aysha za a d'aura dalili kuwa shine mahaifin Aysha ne ya bukaci hakan. Bayan sallar jumma'a jama'a sun taru, ga Nan waliyin Ango Amma babu waliyin amarya, Abba ne ya bukaci da a d'an jira su, wurin shiru yayi kwasam suka jiyo horn d'in mota da gudu motar ta karasa rumfar da Mutane suke zaune, Kura motar ta tada mutanen daga masu Allah ya wadai sai masu zagi, sai wa'anda Kuma suke kokarin toshe hancin su. Kowa hankalin sa a Kan motar take kowa son ganin Wanda ke cikin motar suke son gani, ai kuwa Mahaifin Aysha suka gani da Kanin sa, inda su daddy suke suka zauna, Haisam kuwa fararen jamfa da garen sa Sannan kansa bakar hulace Kamar yadda takalmin sa yake Baki,sai baza kamshi yake, Murmushi yake abokanan sa na tsokanar sa babu ma Kamar Farukh, Malamin da zai d'aura auren ne yayi hamdallah zaiyi magana mahaifin Aysha ya dakatar dashi malam yace "Lafiya dai ko?" Ya amsa da "Uhmn lafiyar Kenan Akwai Wanda ya kamata ku gani kamun a d'aura auren na" Abba yace "Wane ne? Kuma yana ina?" Hannu ya d'aga ya nuna Masa jikin motar,

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});