Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 73

Chapter 73

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta tare a gidan angonta.Allah ya bada zaman lafiya amiin. *After 4 months* Malam Hassan duk wasu raunuka na jikinsa sun warke Amma sabida tashin hankali da ya Shiga ya had'u da shanyewan 'barin Jiki, duk wani kud'i da ake kashewa Faisal ne yake bada su, yayin da Mamy har ta cire Rai da ganin Ayrah, kullum sai tayi kuka. "Mamy nifa na gaji da 'bata kud'i na Akan wannan mutumin" Faisal ke wannan maganar Kama hab'a mamy cike da mamaki tace "Kaci gidan ku" had'e da masa dakuwa. "Yanzu Kai Faisal rashin hankalin naka ya Kai haka? Ubankane fa duk lalacin sa, ni na d'auka kayi Dana sanin abinda ka aikata Ashe ba haka ba, ka godewa Allah ma da ya kowa abun da sauki da yanzu Ana irga kwanakin da ka mutu, daba don Allah yasa yaran basu da gata ba wallahi na tabbata da yanzu baka raye" "Mamy dama tun chan kwanakin mutuwa ta basu yi bane, Kuma wallahi ko kad'an bana Dana sanin abinda na aikata, Ban so hakan ba, naso da shi d'in ne ya mutu ko hankali ya zai kwanta" Tasss Tass Mamy ta shafa Masa maruka har sau biyu, rike kuncin sa yayi Yana matsar kwalla. Mikewa Mamy tayi Tace "Ka fice min daga gani Kar Kuma na Kuma ganin ka anan, Kan kazo ka karasa min shi" Faisal kwallon mahaifin sa yayi da yake kallon su, cike da hawaye a idanun sa, Murmushin Takaici Faisal yayi kana yace "Mamy mari na kikayi? Akan mutumin da bai damu dake ba, mutumin da bazai San mutuncin ki ba? Shin kin San irin bakin cikin da muke ciki da ni da Yan uwana Akan irin abubuwan da yake aikata Amma ke sabida.......... " Shiru yayi ya kasa karasa maganar kallon mahaifin nasa ya Kuma yi ya fice yana matsar kwalla. "Zainabu!!! A hankali cikin sanyin Murya taji ya Kira sunan ta, da sauri har kafarta na hard'ewa ta nufi inda yake tana tambayar sa "Malam wani abun kake buka ne?" Kai ya girgiza mata alamun a'a cikin Muryar sa Wanda baya fita mai kyau yace "Da baki mare shi ba sabida duk abinda yake fad'a gaskiyane, na kasa Mai son zuciya da son Kai, ban damu da kowa ba, ban damu da komai ba in dai zan samu abin da nake so...... " Ajiyar zuciya yayi Mai d'an tsawo kana yace "Na cutar dake da ke da 'ya'yan mu, ban kasance miji na gari ba sannan ni ba Uba na gari bane da ko wani yaro yake fatan samu, ki yafe min Abu, Dan Allah" Cikin muryar kuka Tace "Na yafe maka mallam, dama ban rike ka a Raina ba irin wannan ranar na ke jira Wanda zaka gane koren ka kuma kayi Dana sani , Alhamdulillah Allah nagode maka" ta karasa maganar tana kallon sling na d'akin tana matsar kwalla. Faisal da dawowar sa Kenan ya manta wayar sa , yaji dukkanin maganar da suke Yar karama tsaki yayi a zuciyar sa yace "Yanzun ma tuban muzuru ne don dama halin sane" kofar ya bud'e ba tare da yayi sallama ba ya sa kai ya shige,Mamy da Malam Hassan duk suka kalle shi,kawar da kansa yayi kamar baiga kowa a gun ba, ya nufi inda wayarsa take ya sa hannu ya d'auka sannan ya fice, girgiza Kai many tayi a zuciyar ta Tace "Allah ka shirya min yaran Nan" kwasam Ayrah ta Fad'o mata a rai mikewa tayi ta fice ta samu d'an corridor ta zauna tana kuka mai cin Rai, tana Jin zuciyar tana mata zafi,tana addu'ar Allah ya bayyana mata Yar ta,ko da kuwa gawar tane,sai da tayi mai isarta kana ta koma ciki. Soyyaya ce Mai karfi ta Shiga tsakanin Abdallah da Mardiya musamman ma Mardiya da take ji baza ta iya Rayuwa babu shi ba, don ta shaku dashi. Adnan na bawa Ayrah duk wata kulawar da miji ke bawa matar sa, tasan tana son Adnan Amma da zaran ta bar gidan dole ne ma ya sake ta taya ma Za'ayi ka 'boye Mutum har na tsawon watanni 8? Mardiya da Abdallah na hango a wani d'an madaidaicin shopping complex , Hirar su suke suna d'aukan abinda suke so kana ganin su kasan masoyan Nan suna suna cikin farin ciki, Bayan sun gama suka nufi inda zasu biya kudi, Mika mata wayan sa yayi Sabida ya samu damar ciro wallet d'insa. Tana rike da wayar a hannun ta yayin da take Danna wayarta da d'ayan hannun ganin ana ta Kiran sa Tace "Baby ana ta Kiran ka fa" a Shagwab'ance tayi maganar ba tare da ya kalle ta ba yace "wane ne?" "Adnan" "Bari in na gama zan kira sa" "Okay" A dai dai nan ya gama dasu suka nufi hanyar fita,Yana gaba tana biye dashi,booth ya bud'e ya sa kayan dake hannun sa. Mardiya na tsaye tana kallon sa ji take kamar ta sace shi,Jin Shigowar message yasa ta kalli fuskar wayar nasan,zaro Ido tayi ta bude sakon, kasantuwar wayar ba Key, sai da ta gama karanta sakon tayi saurin fita a ciki,tayi kokari dai dai ta kanta. Sau biyu yana Kiran sunan ta Bata ji ba,a d'an razane ta amsa da ya Kira sunanta a karo na uku,cike da kulawa yace "Lafiyan ki kuwa?" Turo baki tayi Tace "Bana jin dad'ine" "Ban gane ba yanzun Nan fa lafiyar ki kalau" "Uhmn Nikam ka maidani gida" "Kin fasa cin kifin ne?" "Eh na fasa ka maidani gida" ta karasa maganar kamar zatayi kuka. "Ikon Allah,to Shiga muje" Had'e da bud'e mata marfin motar ta Shiga ta zauna,ganin ya zaga tayi saurin ciro karamar wayarta a jaka ta wurga a Bayan mota, ta yi saurin gyara Zama kana ganinta kaga Mara gaskiya. Kallon ta kawai yayi ya girgiza Kai kana yace "Baby na Mai abun mamaki" Murmushi kawai ta masa,suna Isa gida Bata Tsaya Hira dashi kamar yanda ta saba ba, ajiye masa wayarsa tayi,tayi saurin fita,bai Ankara ba har ta isa gate,da d'an karfi yace "Kin manta ledan naki" "Au Na manta" ta dawo da d'an saurin ta karba had'e da fad'in "Thank you bye" ta shige gida da sauri,ya d'anyi Jim yana tunanin canzawan ta, kafad'ar Sa ya d'aga kana ya Shiga,Yana tada motar ya bar wajen,hannun ya sa d'auki wayar sa ya Shiga dialling number Adnan. Da sauri ta Shiga cikin gida bata ma lura da Haisam da ke zaune a parlor ba ,shi Kuma tab'e baki yayi ya girgiza Kai ya cigaba da danna wayarsa,tana Shiga d'akin ta yatsar da ledojin da jakar dake hannun ta kana ta cire gyallen dake Jikin ta,Zama tayi a bakin gado kana ta Kara wayar ta a kunnen ta. Ta dad'e a haka kana Naga ta miki zumbur ta d'auki jakar ta da mayafinta ta yafa ta fita da sauri, Haisam da Ma'isha ta hango Amma tayi kamar bata gansu ba tayi ficewar ta da sauri had'e da d'an gudu. Ma'isha Tace "Ita kuma wannan fa?" Hararar ta yayi kana yace " miko mini takalmin ki na rike miki Naga Alama sun miki nauyine sai kije ki tambayeta" dariya kawai tayi. Mardiya kuwa motarta ta fad'a tun Kan ta Isa gate take Masa horn, da sauri ya bud'e don ya

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});