Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tayi cikin Murya kamar dariya tace "Dan Allah dagaske?" Kai a kasa Ayrah tace "Eh Mamy amma fa bai dad'e ba ya kuma komawa" "Ban gane ya kuma komawa ba?" " Ya sake Shiga comma" Dafe kai mamy tayi Tace "Ai ga irin tanan Wallahi Ayrah kin cuci d'an uwanki kun biye wa son zuciya da uban ki, Dole Mutane suji tsoron *Dangin Uba* kuma Wallahi idan Haisam bai yafe muku ba baza ku tabay ganin rahamar ubangiji ba" tana kaina ta haura d'akin ta cikin tsananin 'bacin rai da takaicin abinda Mijinta da yar ta suka aikata. Ayrah fashe wa tayi da kuka mai sauti da karfi ta saki jikin ta a kasa ta cigaba da rera kukan ta,da gudu Nabila ta karasa inda take cike da kulawa ta fara rarrashin ta tana tambayar ta laifin da tayiwa Mamy cikin Muryar kuka ta Sanar mata da komai, baki a bud'e Nabila ke kallon ta Tama rasa abin Fad'i hakan yasa ta tsaya kallon Yar uwar tata. Muryar Faisal sukaji yana Fad'in "Tabbas biri yayi kama da Mutum Wai ace abinda Daddy yake aikatawa Kenan? Taya na za'a ce alhakin su zai barmu gaskiya daddy ya cuce mu" Sunusi yace "Ka duba kaga ni fa Yaya abin fa bai tsaya Akan sa shi Kad'ai ba harda big sis yayi involving a ciki and abin haushin ma she blindly did what he ask to do" Nabila Tace "Sunusi didn't you heard the story since from the beginning? Bata fa San komai akai ba, and ni ina blaming Mamy ma for not telling her the truth since from day one" Sunusi yace "Uhhh here you go again look sis Nabila Mamy bata da laifi had it been lokacin da Dad ya Fad'a mata abinda zatayi ta Sanar da Mamy ai da zata hanata Amma ta boye mata gaskiya" Faisal yace "Ya Isa please this is not the solution here, fad'in wa yake da laifi ko baiyi da laifi duk bai taso ba, sabida bazai amfane mu da komai let the bygones be gone please" ya karasa maganar yana hard'e Hannayen sa alamun roko. Shiru Sukayi na d'an wasu lokutan Babu Wanda yace komai sai kukan Ayrah dake tashi a d'akin Faisal ne ya matso kusa da ita ta durkusa, handkerchief ya ciro daga aljihun sa ya Mika mata had'e da fad'in "Please ki daina kuka hakan ya Isa Dan Allah karfa ki ja wa kanki wani matsala" Cikin shesshekar kuka tace "Faisal idan banyi kuka ba mezanyi kaina ya kulle duk duniyar bata yimin Dad'i" Yace "Ki fawwala wa Allah komai Insha Allah komai zai dai daita" Ciza le'be Sunusi yayi yace "Wato a cikin Haram aka Haife mu haryanzu kuma muna cikin ta Allah ya isan mu Wallahi......." kallon da Faisal yayi masane yasa ya shiru. Mardiya na Isa gida da murna ta Shiga d'akin Yayanta ta Sanar dashi cewar zancen auren sa da isha na nan yace "Idan na Kira ta naji akasin hakan fa?" Shiru tayi na d'an wasu sakonni kana tace "Ka d'auki Duk matakin da ya Dace" Yace "Okay" had'e kiran Layin Isha,duka biyu ta d'aga da sallama ajiyar zuciya yayi yace "Na d'auka na rasaki" "Uhmn baka rasani ba,Ina mardiya ta Isa gida kalau?" Kallon mardiya yayi kana yace "Eh kalau gata Nan ma muna tare" "Okay ka gaida min ita" Ya amsa da " tana amsawa" Nan ya fara Jan ta da Hira tun bata kulashi har ta saki jikin ta Sukayi ta Hira. Da Yamma Ma'aruf ne zaune da Mummyn sa da Daddyn sa suna ta shirye shirye Don a yau suke so sukai kayan lefe,Daddy tace "Yauwa Babana Nikam ya batun gidan naka ne an gama had'a komai ko?" "eh dad an gama had'a komai" Mummy Tace "Dan Allah yallab'ai ka bar min su anan tunda ka chan part d'aya ba kowa su zauna in yaso daga baya su zauna a Chan" "in dai ya amince da hakan ai bani da matsala" Kallon Ma'aruf yayi Yar karamar dariya yayi yace "mummy irin wannan Kallo haka?" "Eh so nake naji ta bakin kane ko bakaji maganar da muke bane?" "naji Mummy yanda kikace Haka za'a yi" Murmushi kawai tayi suka cigaba da abinda suke. Lefe ya had'u iya had'uwa in tsaya muku bayanin sa 'bata lokaci ne sabida haka just imagine it in your imagination,su Umma ne Kan gaba an karb'i baki yanda ya dace sai dai muce Allah ya nuna mana ranar biki. *WASHE GARI* Ma'isha tun da ta farka tayi sallah Bata Koma ta kwanta ba, had'a kayan ta tashigayi har sai da gari ya soma haske ta gama ban d'aki ta fad'a tayi wanka a gurguje sabida karfe 8 na safe jirgin su zai tashi, bayan ta gama shirine ta sauko kasa hannun ta rike yake da handbag d'inta d'ayan Kuma d'an madaidaicin akwatin ta take jaa, Driver da tun d'azu ya kai kayan Mummy mota yayi saurin zuwa ya karb'i akwatin natan yasa a jaka. Mummy da Daddy da hango suna saukowa daga stairs ya rungume ta a jikin sa suna tafiya suna Hira had'e da dariya gyaran murya Isha tayi kana ta sunkuyar da kanta a kasa. Murmushi daddy yayi had'e da fad'in "Har kin fito?" Ba tare da kalle sa ba ta amsa da "Eh Daddy Good morning" Ya amsa da "Morning" kallon Mummy yayi yace "Naso na kaiku Airport da kaina Amma Kuma zamuyi baki Kuma 8 ne yakamata mu had'u" " Bakomai Alhaji gaba da yawa fatan mu shine mu Isa Lafiya kawai" " To Hajiya Allah ya kaiku Lafiya ya Dawo daku Lafiya" Ta amsa da "Ameen" Ta d'aura da fad'in "Muje ko Isha? Driver na jiran mu dafan ba kiyi mantuwa ba?" "Eh mummy banyi mantuwa ba, Amma ina Umman take ban ganta ba ko zamu biya mu d'auke ta ne?" " A'a Umman Ku baza taje ba" 'dan Turo baki tayi Tace "To Amma mummy mai yasa haka bayan tafiyar Nan da ita aka shirya?" " Gashi Nan ki tambaye shi da Abban kune suka Hana" tana nuna Abba had'e da tab'e baki. Turo baki Isha tayi had'e da d'an buga kafa tace "Daddy why?" Ta karasa maganar kamar zatayi kuka. Yar karamar dariya yayi yace "wato Hajiya so kike ki had'a min wuri ko? Daughter idan Umman ku ta tafi wa zai kula da yaran? Abban ku baya nan Kinga bazai yu a bar su da masu aiki bako?" "But daddy 2 days fa kawai zamuyi" "Yeah I know kawai kuje da mummyn naku, kinji kiyi hakuri" Ba don tasa ba tayi shiru bubbuga kafa ta Shiga yi had'e da fita waje, motar ta fad'a, ta zauna had'e da rungume hannun ta sai faman Turo baki take, Mummy a gefen ta tazaun, Driver ya kunna wa motar wuta kai tsaye airport suka nufa, Basu dad'e da isa ba jirgin su ya Lula a sararin samaniya Nigeria to Turkey. Bayan sun Isa ne a ranar hutawa sukayi basu fita ba sai washe gari suka fita, tun da suka fita basu dawo ba sai yamma liss, washe gari ma hakan Sukayi a takaice dai kwanaki uku sukayi sabida basu samu damar gama sayayyar tasu ba, sai a rana ta hud'u suka koma gida. Yau

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});