Chapter 11
Chapter 11
naga maganar yanzu na gidane ba sai a office zamuyi shi ba" "Wannan ma hakane" Mikewa DPO yayi ya Mika wa daddy wasu files, karb'a daddy yayi ya shiga dubawa, bayan ya Gama dubawa yace "Ka tabbata ka had'a komai da komai?" Murya na rawa yace "Eh Alhaji" Daddy yace "Son Zo ka karb'a, har ya sa hannu zai karb'a yace "Daddy da dai ka bar su a wurin ka tukanna, Ni ban San me zanyi dasu ba a yanzu gaskiya" Yar karamar dariya daddy yayi yace "Son Kenan dukiyar kace fa, ba nawa ba" "Eh na sani daddy shiysa nace ka rike su tukunna" "A a son ba za a yi Hakaba" Umma Tace "Alhaji haryanzu Haisam yaro ne ka rike d'in kamar yadda ya bukata" " Toh Shikenan" Sai ya ajiye su a Kan side table dage gefen kujerar da suke zaune. Ya maida kallon da ga DPO yace "Nagode sosai dpo Allah ya saka da alhairi" "a a Alhaji bakomai aikina kawai nake yi" ya maida kallon sa ga Malam Hassan yace "Mu tafi ko?" Yace "Umm umm Dan Allah Alhaji alfarma nake nema a wurin ka" "Babu wata alfarma da zan maka ka tashi ka fice min daga gida" Mummy ce ta dafe shi a fad'a alamun plz ka saurare shi Sai Kuma yace "Fad'i ina jinka" "Alhaji Dan Allah so nake a taimaka min da muhalli ko da gidan da muke cikine naci Albarkacin yayana Dan Allah, bani da inda zan zauna da iyalai na" Kallon kallo a ka Fara yi a d'akin Haisam Kuma Murmushi kawai yayi. Daddy yace "Hakan ba Mai yiwuwa bane ko da yake bani da iko da dukiyar nan, dukiyar Nan ta Haisam ce shi zaka roka ya maka wannan alfaramar bani ba" Malam hassan har kasa ya durkusa a gaban Haisam yace "Haisam Dan Allah ka taimaka min , nasan ban chanchanchi yafiyar ka ba amma dan Allah find a place in your heart and forgive me" Haisam kallon Umma yayi da tun dazu take ta aikin kallon sa, Murmushi tayi shima ya maida Mata. ___________________ Please kuyi min sharhi, shi kad'ai zai bani karfin gwiwar typing. Sannan Kumin sharing Milhaat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 15 and 16 Kallon Baffan sa yayi yace "Dan Allah ka tashi baffa meyasa zaka durkuwa a gabana bayan kana matsayin ubane a gare ni, Ni na yafe maka duniya da lahira, maganar gida Kuma na bar maka shi halak malak hatta company d'in da kake aiki a Cikin na mallaka maka" Malam hassan kirkirerren kuka ya Fara yi yana fad'in "Nagode, Nagode Haisam Allah ya maka Albarka" ya maida kallon sa ga Umma yace "Zainabu kiyi hakuri ki yafe min Dan Allah" "Bakomai na yafe maka, Allah ya yafe Mana baki d'aya." Duk suka amsa da amiin, Malam Hassan Banda godiya babu Abinda yake har suka fice daga gidan, Nan su Daddy suka shiga hirar su suna farin cikin nasarar da suka samu. Tana ganin shigowar sa ta mike tana fad'in "Daddy ya dai? Da fatan anyi nasara" Murmushin irin zasu gane kuren su yayi yace "Yar daddy ai daddyn nakin ba daga nan, plan d'inmu zai Fara ne daga yau, na gama nawa saura naki" Murmushi tayi Tace "Insha Allah Daddy kasa ranka anyi an gama kawai" "Allah ya miki Albarka Yar Daddy" Ta amsa da "Ameen." Umma da Haisam hankalin su kwance ko bakomai sun karb'i hakkin su, Basu da sauran damuwa a rayuwar su, duk wanni abu da suke bukata na jin dad'in Rayuwa suna dashi. Wannan Kenan Haisam da Ma'isha shakuwace Mai karfi ta shiga tsakanin su tare suke zuwa makaranta su dawo tare, kullum Haisam ke Kai su school, ko da kuwa bai da lectures yakan kaita ta idan sun tashi ya koma ya d'auko ta wasu lokutan Kuma ya jira ta har sai ta gama su koma gida. Umma da Mummy komai tare suke hatta unguwa zasuje tare suke zuwa shopping, har kauyen su Mummy tare suke zuwa. Haisam ke zaune a Cafeteria yana cin abinci,Yana jiran Ma'isha ta Gama lectures,cin abincin sa yake hankalinsa kwance yayin da d'ayan hannun sa yake Kan wayar sa, wata budurwa da baza ta haura shekaru 20 ba ta nufi inda yake, da sallama ta karasa inda yake a hankali ya d'ago kansa had'e da amsa sallamar ta, kallon ta ya tsaya yi, Murmushi tayi Wanda hakan ya kara bayyana kyakkyawar fuskar ta Tace "Sannu dai" Dai dai ta nutsuwar sa yayi ya amsa da "yauwa sannu da" "Dan Allah idan baza ka damu ba zan iya Zama anan?" Tana nuna kujerar da ke fuskan ta nasa. Yace "Eh... Eh zauna Mana" Tace "Nagode, ta jaa kujerar kana ta zauna tana Murmushi, waige waige ta Fara yi kana ta hango wata ta d'aga Mata hannu had'e da fad'in "Waiter!!!" Cikin sauri ta karaso inda take Tace "Welcome ma what will I offer you?" Kallon Haisam budurwan Nan tayi da ya maida hankalin sa Kan wayarsa, Murmushi tayi Tace "Ki bani irin abincin da yake" Haisam d'an d'agowa yayi ya kalleta ya girgiza Kai had'e da Murmushi ya cigaba da cin abinci sa, ba a d'au lokaci ba ta dawo plate d'in chicken and chips, tasa hannu ta karb'a. Ganin Haisam bai kulata ba tayi gyaran murya Tace "Ni suna na Aysha kaifa?" Ba tare da ya d'ago ya kalleta ba yace "Haisam" Tace "Wow Nice name, kai a school d'in Nan kake ne?" "Eh" "Wani department?" "Medicine" "Nima a medicine nake Amma ban tab'a ganin ka ba, Amma aji nawa kake?" "200 level" "Oh shiyasa ni a 100 level nake" Yace "Maybe" Duk maganar Nan da suke bai d'ago ya kalleta ba. "Lalle gayen Nan akwai rainin hankali duk yanda nake so muyi Hira ya kasa sakin jikinsa , dama ance kyawawan mazan Nan haka suke da girman kai" duk maganar Nan a zuciyar ta take. Bata lura ba har ya Kira Waiter ya biya su kud'in su ya Mike zai tafi, karar kujeran da ta jaa Ne ya dawo da ita daga tunanin da ta lula da murya mai d'an karfi Tace "Ina Kuma zaka?" Kallon ta yayi cike da rashin fahimta yayi d'an Murmushi yace "Gida" ya juya zai tafi tayi saurin mikewa Tace "Dan Allah ko zaka iya bani number ka?" "Number ta Kuma?" "Eh number ka" " Da fatan dai ba laifi nayi bako?" Murmushi tayi Wanda hakan yasa Beauty point d'inta ya nuna tace "A a kawai so nake muyi wata magana da kai idan bazan takura maka ba" Yace "Okay" ya Mika hannun sa alamun ta Mika Masa wayar ta, cikin sauri ta Mika masa wayar Yana sawa ya Mika Mata ya fice daga gun, bata samu damar yi Masa Godiya ba,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76